Subscribe
  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin
Yadda ake dahuwar farfesun kaza da dankalin Turawa

Yadda ake dahuwar farfesun kaza da dankalin Turawa

Assalamu alaikum uwargida. Yaya sanyi? Saboda shigowar sanyi yana da kyau a yawaita shan farfesu domin dumama jiki. Yawan shan farfesu na rage kasala da magance wasu kwayoyin cutar mura a jikin mutum. Hakan ya sanya a yau na kawo muku yadda ake  girka farfesun dankalin Turawa da kaza wanda aka fi sani da Ingilishi da ‘potatoe peper soup’. Domin sanya kunnen maigida motsi, ya kamata a dage wajen koyon girke-girken zamani. Girki shi ne sirrin zaman aure sannan iya girka abinci daban-daban na sanya manyan gobe cikin farin ciki da kuma son komawa gida da wuri a duk inda suka tafi.

 

Abubuwan da za a bukata

•        Kaza

•        Dankalin Turawa

•        Kori

•        ‘Thyme’

•        Karas

•        Attarugu

•        Tumatir

•        Gishiri da magi

Hadi

Bayan uwargida ta fere dankalinta, sai ta yanka shi kanana. Daga nan sai ta wanke kazarta. Ta fara tafasa kazar da attarugu da kori da garin tafarnuwa da citta da magi da tumatir da ‘thyme’. Idan ta dan dahu, sai ta zuba yankakken dankalin Turawan a ciki da koren wake da kuma yankakken karas.  Wannan girkin an fi  so a yi shi da safe domin karyawa.

Ina son jawo hankalin masu karatu cewa duk macen da take zuba man gyada a farfesu kowane iri ne, to da sauranta a girki. Domin farfesun kaza ko na kifi da na nama da sauransu suna dauke da kitse.