✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda ake faten tsaki da gyada

Assalamu alaikum uwargida yaya yara? Tare da fatar ana cikin koshin lafiya. Idan aka ambaci kalmar ‘fate’ nau’o’in fate da dama zai zo a tunaninmu. Akwai…

Assalamu alaikum uwargida yaya yara? Tare da fatar ana cikin koshin lafiya.

Idan aka ambaci kalmar ‘fate’ nau’o’in fate da dama zai zo a tunaninmu. Akwai fate da dama da ake yi kamar: faten doya da faten wake da faten tsaki da sauransu.

A yau za mu shiga gargajiya ce don haka za mu koya muku yadda ake faten tsaki da gyada. A sha fate lafiya.

Abubuwan da ake buqata

  • Tsaki
  • Kifi banda
  • Attarugu
  • Albasa
  • Tumatir
  • Alayyaho
  • Nikakkiyar gyada
  • Magi
  • Kori
  • Garin tafarnuwa
  • Garin citta
  • Manja ko man gyada

 

Yadda ake yin hadin

Da farko za a wanke tsakin masara ya zamo babu tsakuwa ko kadan sannan a dora tukunya a wuta a zuba manja ko man gyada sannan a yayyanka albasa a zuba da nikakken kayan miya a soya tare da bandar kifin.

A zuba magi da kori da garin tafarnuwa da na citta sannan a kwaba gyada kadan a zuba ta yi ta tafasa sannan a zuba tsaki har sai ya nuna.

A zuba tsakin kadan domin yana kumbura. Idan tsakin ya nuna sai a zuba yankakken alayyahon da aka riga aka wanke da ruwan gishiri kuma aka yayyanka.

Sannan sai a rage wutar risho. Bayan minti uku sai a sake gaurayawa a sauke.

A sha fate lafiya.