✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda ake gadon kamanni da dabi’u da cututtuka daga iyaye

Yaya ake yara su biyo dangin uwa ko na uba ne a tsarin kimiyya? Daga Idris Umar, AbujaAmsa: kwayoyin halittu na gado su ne ke…

Yaya ake yara su biyo dangin uwa ko na uba ne a tsarin kimiyya?

Daga Idris Umar, Abuja
Amsa: kwayoyin halittu na gado su ne ke da alhakin yada kamanni da siffofi da cututtukan gado a tsakanin iyali ko ma cikin jinsi. Su wadannan kwayoyin halittu masu daukar gado, su ake kira chromosomes.
Da farko dai ya kamata mu san cewa kowane ruwan da namiji da kwan mace na dauke da kwayoyin halittun gado guda ashirin da uku, wadanda idan sun hade sun zama dan tayi za su zama dan na dauke da arba’in da shida ke nan. A jikin wadannan halittu arba’in da shida ne ake samun masu dauke da siffofin da yaro yakan gada daga mahaifi ko mahaifiya. Siffofin sun hada da namiji ko mace, tsayi ko gajarta, kiba ko siranta, fari ko baki, haske ko duhu, katon kai ko karamin kai, karfi ko rauni, kin ji ko salahanta, da ajin jini, da yanayin jerin hakora da dai sauransu. Ban da siffofi kuma, har da masu dauke da gadon cututtuka. Akwai cututtuka da dama masu bin zuri’a wadanda muke kira cututtkan gado, wadanda idan akwai mai su a zuri’arka kai ma za ka iya samu. Suna nan sun fi dari, amma bari mu lissafto muhimmai daga cikinsu:
1-Ciwon Suga, 2-Hawan Jini/Ciwon Zuciya, 3-Tabin hankali, 4-Amosanin Jini, 5-Sanyin kashi, 6-Ciwon Daji na Mama, 7-Ciwon Daji na Mahaifa da kuma 8-Yankakken lebe.
Ya kamata kuma mu san cewa kwayoyi masu dauke da wasu siffofi a mafi yawan lokuta (wato a kashi 75 cikin dari) sun fi na wasu siffofin karfi. Misali, kwayoyi masu ba da jinsin mace da masu ba da tsayi ko farar fata sun fi masu ba da namiji da masu ba da gajarta da duhu karfi. To yayin da namiji mai tsayi ya auri mace mai gajarta ko mace mai tsayi ta auri namiji mai gajarta, kwayoyin tsayi sukan danne na gajarta, ta yadda za a samu yaro mai tsayi ko madaidaici amma da wuya a samu gajere. Kusan haka zancen yake idan duka masu tsayi ne, ta yadda a iyaye masu tsayi da wuya a samu da gajere (sai dai idan a kakanni akwai). To da a ce kuma duk ma’auratan gajeru ne fa? To ’ya’yansu kusan duka gajarta za su yi (sai dai fa idan a kakanni akwai dogo). Wannan ce ma ta sa a auren farin mutum (farar fata) da bakar fata, kan haifar da samun farin fata ba baki ba saboda a tsarin gado farar fata ta fi baka karfi.
Akwai siffofi na zahiri akwai kuma na badini. Wato sauran halaye ko siffofi da muke dauke da su wadanda ba su fito fili ba suna cikin wadannan halittu a boye har sai an hayayyafa ake ganewa. Misali, gajerun mutane wadanda dayansu ke dauke da kwayar halitta mai siffar tsayi za su iya samun da ko ’ya mai tsayi. Wannan kuma shi ne gado na wurin kakanni ke nan.
Ya kamata kuma mu san cewa wurin zama da yanayin karfin aljihu da wasu al’adu suna iya yin tasiri a kan kwayoyin halittu na zahiri ta yadda sukan rikide idan aka ba su wani lokaci. Wato idan mazaunar ’ya’ya da iyaye daban-daban ce, (kamar a ce ’ya’ya na birni iyaye na kauye) to za a iya ganin bambancin kamanni da juna. Wani babban misali mai nuni da hakan kuma shi ne, idan aka haifi ’yan tagwaye masu kama daya, aka raba mazauninsu (misali aka kai daya kasar Larabawa ko ta Turawa, aka bar daya a nan gida), bayan kamar shekaru ashirin idan an gan su a tare sai an yi da gaske kafin a iya cewa ’yan gida daya ne ma ballantana a gane ’yan biyu ne. Idan da a ce kuma duka biyun za su rayu a wuri guda, dole bayan shekara ashirin a ga ba su da wani bambanci na kuzo-mu-gani.
Irin wannan ilmi yana da muhimmanci kwarai da gaske musamman a wajen alkalanci, kamar wajen rabon gado ko raba rigimar ’ya’ya. A kasashen da suka ci gaba, a rikici irin na gado bayan rasuwar wani hamshakin mai arziki, mutane da dama suka zo a matsayin magada. A nan ana kiran masana kimiyyar gado su fayyace ko shin wane dan wane ne ko kuma a’a. Hanyar farko da ake bi a gano shi ne na kalar jini ko ajin jini. Da yake jini an kasafta shi kashi hudu, idan an riga an san ajin jinin uban da na uwar, ajin jinin yaron dole ya dauko na daya daga cikin iyayen. Idan ya yi daban to ba dansu ba ne. Haka ma ko da ta yi daidai, akwai mataki na gaba da ake iya dauka domin tabbatarwa.
Wadannan kananan kwayoyin halittu masu dauke da gado har ila yau sukan bambanta daga jinsi zuwa jinsi, sukan kuma yi kamanceceniya a tsakanin jinsi daya. Misali, jinsin Hausawa na da nasa kamanni, na Fulani ma haka. Ta irin wannan ilmi ne kuma yawanci fitattun bakaken kasar Amurka suka gano jinsunsu na asali da kuma inda suka fito a wannan nahiya ta Afirka. An gwada kwayoyin halittun gadon ’yan wasan kwallon tenis din nan na Amurka wato Serena da benus Williams da na iyayensu an gano sun fi kama da na Yarabawa. Wasu kuma sun gwada an ce sun fi kama da na mutanen kasar Afirka ta Kudu, wasu da dama kuma an gwada an ga sun fi kama da na mutanen kasar Senegal da dai sauransu.
karin bayani: A makon jiya, a shafin Kimiyya da kere-kere wani mai karatu, Ali Fancy ya tambayi Baban Sadik dalilin da ya sa yakan ji kara a kunnensa idan ya amsa waya, inda aka ce ya tuntubi wannan shafi don karin bayani. To karin bayanin shi ne, a gaskiya a binciken kimiyyar lafiya babu inda wayar hannu take sa irin wannan kara, sai dai idan wayarka ce ke da matsala. Don haka ka canza waya, wato ka sayi mai kyau.
Hakora na ne suka yi rami ta yadda idan na ci abu mai gishiri ko mai suga kamar an sa wuta don zafi. Don Allah ina mafita?
Daga Aliyu Saheel, Ondo
Amsa: To da yake kai ma da alama sabon zuwa ne, bari a dan yi maka bayani a takaice. kwayoyin cuta na zama a kan hakoranmu, har wasu lokuta su cinye su, wurin ya yi rami. Dole ka je ka a duba hakoran, idan ramin ne a cike shi, domin idan ba haka aka yi ba, za ka ci gaba da shan wahala.

LAFIYAR MATA DA YARA

Abubuwan da ke jawo mutuwa ko galabaita ga masu juna biyu
A makon jiya mun fara magana a kan laulayin ’ya mace, inda muka ce ya fi yawa a lokacin daukar ciki. To wadanne dalilai ne suka sanya hakan?
Hawan jini: Wannan ya fi kama mace a haihuwar fari, musamman idan akwai mai hawan jini a danginta. Shi yake sa jijjiga da suma har da mutuwa a wasu lokutan. Mace mai ciki da ta fara ganin kafafuwa na kumbura, fitsari na kumfa, to kananan alamu ne. Manyan alamu su ne matsanancin ciwon kai ko na kirji (kamar ana hura wuta a ciki, irin na gyambon ciki). Idan ba a dau mataki ba a nan akan iya yanke jiki a fadi a fara jijjiga.
Tsinkewar jini: Jinin jiki ne ke karewa ta hanyar mahaifa. Iri biyu ne, akwai wanda kan tsinke kafin haihuwa akwai kuma na bayan haihuwa. Wanda ke zuwa kafin haihuwa a hankali a hankali yake farawa ga mai ciki kafin ya zo ba kakkautawa. Za a iya daukar mataki kafin abin ya yi nisa idan aka je asibiti mafi kusa. Sai kuma wanda ke faruwa bayan an haihu. To wannan ya fi hadari sosai domin ya fi zuwa da yawa kuma da karfinsa zai ta zuba har sai an dau matakin tsayar da shi. Idan ba a dau mataki ba, jinin jiki kan kare nan da nan.
Doguwar nakuda: Duk matar da ta yini ta kwana tana nakuda, a sama mata lafiya, a kai ta asibiti, domin nakuda bai kamata ta wuce awa 14 ba ko da haihuwar fari ce. Ita doguwar nakuda ta fi jawo salwantar ran jariri fiye da na uwa. Takan jawo wa uwa galabaita sosai don takan iya sa ciwon yoyon fitsari.
Jinkirin neman magani: A likitance akwai jinkiri guda uku da ya fi sa mutuwa a mata masu juna biyu fiye da abubuwan da muka lissafa a sama, musamman a karkara ko a wadanda babu asibiti kusa da su.
Jinkiri na farko shi ne wanda kan faru kafin a fito daga gida. Akan dauki lokaci idan abu ya faru ga mai juna biyu kafin ma a fito daga gida. Misali, za ta iya yiwuwa matar ita kadai ce a gidan ba wani babba kuma maigida ba ya nan. Sai kuma jinkiri na tafiya asibiti, wato idan an yanke shawarar a tafi asibiti, to tafiyar ma kan zamo wani tashin hankali, musamman idan daga lungu ko kauye za a fito. Ko dai ba abin hawa ko kuma hanyar ba kyau. Sai kuma jinkiri na uku, wanda akan samu a asibiti kafin a fara kula maras lafiya. Wato dole sai an yi jira kafin a ga ma’aikatan lafiya a mafi yawan lokuta ko kuma a kuma a ce sai an yanki kati, an yi gwaje-gwaje da sauransu, musamman a wadanda ba su taba zuwa awo ba. Idan da ana zuwa awo, za a samu sauki, tunda komai na nan a rubuce a ajiye a kati.
Sauran dalilai da kan sa jin jiki ga mai ciki sun hada da zazzabi da kan samu masu juna biyu sakamakon cizon sauro ko kuma sakamakon kwayoyin cuta da suka fara shiga mahaifa.
A mako mai zuwa in Allah Ya kai mu za mu amsa wasu tambayoyi da suka shafi iyalai, wato mata da yara wadanda wasunku suka aiko.