Da Dumi Dumi

Yadda ake girka ‘Sweet and Sour Shrimps’

Barkanmu da warhaka Uwargida, tare da fatan ana lafiya. Yana da kyau  idan an girka abincin gida Najeriya, kuma a taba na wadansu kasashe ba don komai ba sai don wayar da kan maigida da manyan gobe wajen sanin nau’ukan girke-girke saboda idan Allah Ya sa aka ziyarci wadannan kasashe ba za a yi bakunta ba da irin girke-girkensu. Sanin girki wata fa’ida ce na ilmantar da al’umma. Wajibi ne uwargida ta koya wa ‘yan dugwui-dugwui  iya girki, domin idan sun kware sosai, za su iya bude wata makaranta ta koyar da wadannan girke-girken kuma hakan zai iya zamo musu sana’a a irin wannan yanayin da muka shiga na rashin samun aiki a kasa. A yau na kawo muku girkin Turawa “Sweet and Sour Shrimps’.

Abubuwan da za a bukata

  • ‘Shrimps’ (Ana iya samunsa a manyan shagunan da ake sayar da kaji ko kifi da suka yi kankara).
  • ‘Dark soy sauce (shi ma ana iya samunsa a manyan shagunan da ke sayar da kayan abinci).
  • Sugarin ko suga
  • Nikakkiyar citta
  • Cokali daya na nikakkiyar tafarnuwa danya
  • Rabin kofin ruwan abarba
  • Man zaitun
  • Karas
  • Attarugu
  • ‘Peas’ (za a iya samu a kasuwa inda ake sayar da su karas)

Hadi

Bayan ‘shrimps sun narke sai a tsoma su a cikin ruwan ‘dark soy sauce’ sannan a saka su a cikin gidan sanyi na tsawon awanni uku. Bayan haka, sai a tsame su daga cikin ruwan sannan a zuba suga da nikakkiyar citta da tafarnuwa da kuma ruwan abarba.

A dora tukunya a kan wuta sannan a rage wuta sai a dora tukunya wadda ba ta cika kama girki ba (non-stick) sannan a zuba man zaitun a cikin tukunyar daga nan sai a zuba wannan ‘shrimps din da aka tsame din a cikin man zaitun mai zafi sai a ci gaba da juyawa sannan a zuba yankakken karas a ciki, a ci gaba da juyawa har sai ta nuna sannan a sauke. Wannan irin girki ya dace da wadanda ke son rage kiba, domin yana dauke da sinadarin gina jiki.

ADVERTISEMENT
Tura
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya