✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda ake hada lemon Na’a-Na’a da Kokumba

Kayan hadi: •         Na’a-Na’a •         Kokumba •         Sukari/Sirof •         Filebo   Yadda ake yi: Da farko uwargida za ki samu Na’a-Na’a irin koriyar nan sosai…

Kayan hadi:

•         Na’a-Na’a

•         Kokumba

•         Sukari/Sirof

•         Filebo

 

Yadda ake yi:

Da farko uwargida za ki samu Na’a-Na’a irin koriyar nan sosai sai ki wanke ta sosai ki tabbatar duk kasar da ke jiki ta fita tas sannan sai ki markada ta a bilenda daga nan sai ki tace ki ajiye ruwan a gefe guda, sai ki samu Kokumba mai kyau ki yanyanka ta sannan ki markada ki tace. Sai ki dafa sukari wanda zai zama abin da ake kira sirof. Sai ki samo babban kofinki ki juye tattaccen ruwan Na’a-Na’a da na Kokumba a ciki ki dauko sirof din nan ki zuba a kai. Sai ki samu filebo mai kamshi ki zuba a ciki.

Shi ke nan sai ki sa a firiji, idan ya yi sanyi sai sha.