✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda ake zaben sabon Sarkin Zazzau

Bayani daki-daki kan yadda ake zabar sarki a Masarautar Zazzau

Hankula sun karkata zuwa ganin wanda zai zama sabon Sarkin Zazzau, tun bayan rasuwar Sarki Shehu Idris, wanda ya rasu bayan shafe shekara 45 a kan karagar mulki.

Aminiya ta tattaro muku yadda ake zaben sabon sarki, duba da gibin da aka samu a kujerar mulkin Masarautar Zazzau sakamakon rasuwar Sarki Shehu Idris.

Bisa al’ada a masarauta akwai tsarin da ake bi domin zaben wanda zai zama sabon sarki, a duk lokacin da sarki mai ci ra rasu ko aka tube shi ko wani dalili ya sa aka samu gurbi a kujerar.

A masarautar Zazzau da ke Jihar Kaduna, masu zabar sarki (’Yan Majalisar Zaben Sarki) su ne:

  1. Makaman Zazzau, Alhaji Muhammad Abbas
  2. Fagacin Zazzau, Alhaji Umar Muhammad
  3. Wazirin Zazzau, Alhaji Ibrahim Aminu
  4. Limamin Kona, Shaikh Muhammad Sani Aliyu
  5. Limamin Gari, Shaikh Dalhatu Kasim

Majalisar ce ke da alhakin zabar sabon sarki a duk sadda aka samu gurbi a kujerar, amma kuma ’yan majalisar ba sa yin sarauta.

Gwamnatin jihar kan tura wakilinta idan za a zabi sarki, ya zauna da majalisar domin tantance masu bukatar zama sarki daga gidajen sarautar Zazzau.

Gidajen sarauta hudu ne a Masarautar Zazzau – Gidan Katsinawa da Gidan Barebari da Gidan Sullubawa da Gidan Mallawa.

‘Yan gidajen kan zabi daya daga cikinsu ya wakilce su wurin yin takarar neman sarauta. Amma duk mai sha’awa na iya bayyanawa ba lallai sai gidan da ya fito ya ayyana shi ba.

 

  • Hanyoyin nada Sarkin Zazzau

BBC ta ruwaito Masanin Tarihin Masarautar Zazzau kuma Daraktan Gidan Tarihi na Arewa da ke karkashin Jami’ar Ahmadu Bello, Shu’aibu Shehu Aliyu, yana cewa ka’idojin tantance ’yan takara su ne ya kasance mai neman sarautar:

  • Bai taba yin laifin da hukuma ta kama shi ko ta hukunta shi ba
  • Ya taba rike matsayi na sarauta ko hakimta a Zazzau
  • Yana da cikakken ilimin zamani da na addini
  • Ba tsoho tukuf ba ne
  • Ya fito daga daya daga gidajen sarautan Zazzau.

 

  • Tantancewa a majalisar zabar sarki

Daga na sai majalisar ta shiga zaman tattaunawa kan dukkannin ’yan takarar daya bayan daya.

Tancewar kar kan yi duba ne ga irin ayyukan da kowane dan takara ya gabatar da iliminsa da kuma mu’amala da mutane.

Daga karshe ’yan majalisar za su zabi mutum uku a cikin masu neman zama sarki, su aike wa gwamna.

 

Alkalancin Gwamna

Idan sunayen suka isa wurin gwamna sai ya fitar da da mutum daya da ya ga ya dace ya zama sarki.

Daga nan sai gwamnatin jihar ta sanar da sunan wanda gwamna ya zaba a matsayin sabon sarkin Zazzau.

“Daga bisani kuma sai a ba da sanarwa ga wanda shi ne sarki sannan sai a mika masa takardar cewa gwamnati ta zabe shi ya zama sabon sarki na masarautar Zazzau”, kamar yadda masanin ya shaida wa BBC.

Idan gwamna na da mulahaza ko bai gamsu da mutum ukun da aka mika amsa sunayensu ba, yana na ikon jan hankalin majalisar ta sake komawa ta tattauna ko ma ta sake fitar da wasu mutum uku da a cikinsu gwamna zai zabi sabon sarki.

 

  • Bikin nadin sabon sarki

Bayan nan sai a shirya gagarumin bikin inda a wurin bikin za a yi wa sabon sarkin nadi a ba shi takarda shaida da kuma babbar sandar zama sarkin Masarautar Zazzau.