✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda auren wata amarya ya kusa mutuwa saboda amfani da ‘a-cuci-maza’ (3)

A makon farko na aurensu, Faruka bai kusanci Ramlat ba, saboda ta nuna masa tana jinin al’ada. To ashe Faruk bai sani ba, duk kyawun…

A makon farko na aurensu, Faruka bai kusanci Ramlat ba, saboda ta nuna masa tana jinin al’ada.

To ashe Faruk bai sani ba, duk kyawun jiki da surar da Ramlat take takama da shi, ba nata ba ne. Tana amfani ne da wasu irin surori ko gashi na ’yan kanti da Hausawa ke kira ‘a-cuci-maza’.

A tsawon lokacin da Faruk ya shafe tare da Ramlat ba ta taba yi masa bayani ko ya fahimci halin da ake ciki ba. Irin gashin da yake ganin Ramlat take dauke da shi har gadon bayanta, ashe na kanti ne, ba asalin gashinta ba ne.

Ramlat takan fakaici idon Faruk  sai ya fita kafin ta cire wannan kyale-kyale da take dauke da shi idan za ta shiga wanka.  Kuma da zarar ta fito sai ta rika alla-alla tana shiryawa don kada ya koma gida ya same ta.  Kafin ya koma sai ta caba ado ta hanyar amfani da ‘a-cuci-maza’.  Da zarar Faruk ya koma gida sai ya ji Ramlat ta kara kwanta masa a rai saboda irin adon da take yi masa. Yakan zolaye ta cewa “Ya dace da irin matar da ya dade yana da burin ya aura”.  Ita kuma sai ta yi murmushi kawai, don ta san ba haka jikinta yake ba.

Asirinta ya tonu ne a ranar da Faruk ya koma gida ba tare da sanar da ita ba. Ya yi amfani da mabudinsa wajen bude kofar dakin ba tare da saninta ba.

Ya yi haka ne don ya mamayi amaryarsa sai dai kawai ta gan shi a gida ba tare da ya sanar da ita ba.   Shiga dakin ke da wuya sai ya tarar da gashin kanti a gefe da wata rigar nono mai kama da siffar mutum.  Sannan ya tarar da mazaunin mace da shi ma na roba ne wanda ke fitarwa da mace siffa.

Wadannan abubuwa da Faruk ya gani sun tayar masa da hankali don ya tabbatar da su Ramlat ta yi amfani wajen yaudararsa har suka yi aure.

Bayan ta fito daga wanka ba tare da sanin mijinta Faruk ya koma gida ba, sai suka yi ido biyu, inda nan take ta sunkuyar da kai saboda kunya.  Ta gane Faruk dai ya san halin da take ciki yanzu.

Nan take ta fara kwalla da juyayin abin da ya faru.  Ta fara lallashinsa, amma saboda bacin rai da rudewa sai ya dauki mabudin motarsa ya bar gidan.

Bai zame ko’ina ba sai wajen wani abokinsa kuma amininsa mai suna Abdullahi, inda ya shaida masa halin da yake ciki. Da farko Faruk ya yanke shawarar idan ya koma zai sallame ta ne, amma abokinsa Abdullahi ya yi masa nasiha kuma ya nuna masa illar yin hakan.

Nan take suka yanke shawarar komawa gidan tare don su tunkari Ramlat dalilin da ya sanya ta aikata haka. Bayan sun turke Ramlat ne, sai ta fada musu tarihinta da kuma dalilin da ya sanya ta aikata haka. Ta ce ta yi rayuwa ne da wadansu kawanyenta da iyayensu masu kudi ne a lokacin da take makaranta, inda suka canja mata ra’ayi.

Nan take tausayinta ya kama Faruk tare da abokinsa. Daga nan suka yi mata nasiha ta daina yin karya, musamman a matsayinta na mace.  Faruk ya ce  ba don abokinsa Abdullahi ya lallashe shi ba da tuni ya ba ta takardar saki, kuma idan ya yi haka tamkar ya tona wa kansa asiri ne.  A ce ya yi aure ba a dade ba ya rabu da matar.

Nan dai Faruk ya yafe mata, kuma ya dauki alkawarin ba zai tozarta ta ba. Sai dai ya gindaya mata sharadin zai sake auro irin matar da yake so.  Ita kuma Ramlat in da rabo nan gaba Allah zai iya ba ta irin siffar da yake so a wajenta, tunda za ta rika cin abincin mai gina jiki. Nan Ramlat ta amince tunda babu yadda za ta yi.  Kuma ta gode masa a bisa karamcin da ya nuna mata.  Kuma ta yi alkawarin zai same ta mai ladabi da biyayya har tsawon rayuwar aurensu.

Daga haka mata masu irin wannan hali na canja fasalin jikinsu da “a cuci maza” don su yaudari maza, sai wannan dai ya zama darasi gare su.

Mun kammala.

Za a iya samun Ahmed Garba Mohammed a 08028797883