✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda Babban Taron Majalisar dinkin Duniya ke wakana

A ranar Talatar da ta gabata ce aka fara Babban Taron Majalisar dinkin Duniya karo na 73, inda shugabannin kasashen duniya suka hadu domin tattaunawa…

A ranar Talatar da ta gabata ce aka fara Babban Taron Majalisar dinkin Duniya karo na 73, inda shugabannin kasashen duniya suka hadu domin tattaunawa halin da duniya ke ciki a birnin New York.

An bude taro ne tun ranar 18 ga Satumba, sannan aka fara tattaunawa a ranar 25 ga watan, inda za a kwashe kwana tara na aiki ana yi.

Wannan shi ne karo na hudu cikin tarurruka 73 da aka zabi mace ta zama Shugabar taron na Majalisar dinkin Duniya, bayan an zabi ’yar siyasa daga kasar Ecuador María Fernanda Espinosa Garcés ta jagoranci zaman tattaunawar.

Shugabannin kasashen duniya da suka hada da Shugaban Amurka Donald Trump sun fara gabatar da jawabai yayin da ake ci gaba da tarurrukan ministoci da wakilan kasashen duniya a gefe guda.

Zabar María Fernanda Espinosa Garcés a matsayin Shugabar Taron na bana wani yunkuri ne na nanata kira game da mai da hankali a kan yaki da tsangwamar da ake yi wa mata da kuma karfafa musu gwiwa a cikin harkokin siyasa a duk wasu jawabai da za a yi a taron.

A abban taron an shirya tattauna batutuwan da suke da muhimmanci ga harkokin mata, kama daga kawo karshen cin zarafin mata da ’yan mata da kuma daidaiton albashi da shirye-shiyen agaza wa mata bakin haure da sauransu.

Loretta Anocie Mataimakiya ta Musamman ga Shugaban Najeriya a kan Harkokin Kafafen Sadwar Zamani ta bayyana wa Muryar Amurka abin da za a gabatar a taron da aka shirya wa mata, “Za mu gabatar da batun da ya shafi mata da kananan yaran Afirka saboda muna da matsaloli iri daya kuma al’adu iri daya. Bayan haka matan shugabannin Afirka za su tattauna a kan wannan batu ta yadda za a taimaka wa kasashen Afirka.

“Tattaunawar matan shugabannin kasashen za ta kuma mai da hankali a kan mata da matasa, musamman ilimin yara mata,” inji ta.

…Ya kamata da mayar da Iran saniyar ware a duniya- Shugaba Trump

Da yake gabatar da jawabinsa, Shugaban Amurka Donald Trump ya yi kira ga shugabannin kasashen duniya da suka hallara cewa, ya kamata su mai da gwamnatin Iran saniyar ware muddin ta ci gaba da cin zali, inda ya zargi shugabannin Iran da haddasa rudani da mutuwa da kuma barna.

Trump ya ce, shugabannin Iran “Ba su mutunta makwabtansu ko kan iyakokinsu ko sauran kasashe. A maimakon haka shugabannin Iran suna azurta kansu da dukiyar kasar, yayin da kuma suke haddasa tashin hankali a Gabas ta Tsakiya da kuma wasu yankuna da ke nesa.”

Trump ya nanata cewa, yarjejeniyar da aka cimma a shekarar 2015  a zamanin mulkin Obama na kawo karshen ayyukan nukiliya a Iran, wanda ya janye, wata garabasa ce kawai shugabannin Iran suka samu da ta ba da damar kara karfin ayyukan sojin kasar Iran da kimanin kashi 40 cikin 100 da kuma daukar nauyin ayyukan ta’addanci da aikata ta’asa a Syria da Yemen kamar yadda Muryar Amurka ta tsakuro daga cikin jawabinsa.

…Cin hanci ne ke kawo matsala a duniya- Shugaba Buhari

Shi kuma Shugaban kasa Muhammadu Buhari a nasa jawabin, ya bayyana damuwarsa ce a kan yadda ake ci gaba da samun matsalolin tsaro a duniya.

Ya ce abin takaici abubuwan da ke kawo barazana da koma baya ga tsaro da zaman lafiyar duniya da “muka tattauna a bara,” har yanzu kwalliya ba ta biya kudin sabulu ba kamar yadda Muryar Amurka ta ruwaito.

Ya tabo batun rashin tsaro da ake fama da shi a Nahiyar Afirka da yankin Asiya musamman rikicin Syria da Yemen da Falasdinu da ma ayyukan ta’addanci na cikin gida kamar Boko Haram da sauransu.

A kan batun mummunan kisa da aka yi wa kabilar Rohinygya a Myanmar, Shugaba Buhari ya yaba wa Majalisar dinkin Duniya a kan kokarin kawo karshen wahalhalun da Musulmin Rohingya suka fada ciki.

Shugba Buhari ya kuma yi magana a kan yaki da cin hanci da rashawa inda ya ce dole ne a yaki cin hanci da rasahwa, saboda su suke hana kasashe ci gaba tare da jefa su cikin rashin tsaro.