✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda ‘yan kasar waje ke juya farashin fulawa a Najeriya

Kamfanonin kasashen waje na yin yadda suka ga dama da farashin fulawa a Najeriya

Masu sana’ar biredi da danwake da taliya na samun matsin lamba daga kamfanonin fulawa mallakin ‘yan kasuwar kasashen waje a Najeriya.

Masu kamfanonin na yin karin farashi ba gaira babu dalili da ake yi, wanda ke haddasa tsadar duk wani abu dangin fulawa a kasar nan.

Binciken Aminiya ya yi nuni da cewar kamfanonin fulawar na kuma yin amfani da karfin jarinsu wajen karya farashin alkama a hannun manoman da wadanda suke saye hannusu.

Tsaka mai wuyar tasa manoman da masu gasa burodi kokawa kan hauhawar farashin, tare da zargin cewa, “masu kamfanoni fulawar na hada kansu ne su tsawwala farashin don a cuci mutane”.

Su wa ke shugabantar kamfanonin fulawar?

Wata takarda da Aminiya ta gano a kamfanonin ta yi nuni da cewa yawancin kamfanonin fulawar da ke Najeriya na ‘yan kasuwar kasashen waje ne, kuma kansu hade yake wajen sanya farashi da kuma karin sa duk lokacin da suke bukata.

Takardar ta tabbatar da cewa Kamfanonin ba sa tuntubar masu gidajen burodi ko taliya kafin su kara farashin fulawa da dangoginta.

Kamfanonin ‘yan kasuwar kasashen wajen sun hada da: Flour Mills of Nigeria (FMN) da ke karkashin jagorancin Greek management; da Crown Flour Mill (Olam Flour Mills) na Indiyawa; da Dufil Group (De United) shi ma na Indiyawa.

Akwai kuma Life Flour Mills, wanda mafi yawan jarinsa na baki ne; sai kuma Kings Flour Mill da Honeywell Flour Mill, wadanda na ‘yan Najeriya ne.

Me ya sa farashin fulawar ya karu

Kwanan nan, mutane da ‘yan kasuwa suna ta kokawa kan yadda kayan masarufi dangin fulawa suka yi tsada.

Masu cin burodi a Kano da Maiduguri sun koka kamar yadda masu cin Semolina da Taliya da danwake kai har da dusar alkama ta dabbobi suka koka a kasar nan.

Karin farashin ya tilasta kungiyar masu gidajen burodi shiga yajin aiki a ranar Alhamis, wanda hakan ya haddasa karancin burodi a wasu manyan garuruwan kasar nan.

Wani magidanci da ba ya son a fadi sunansa ya ce annobar sayar da burodi a Maiduguri.

Manajan gidan burodin My Lady’s Bakery, da ke hanyar Baga, Matthew Clement, ya ce kungiyarsu ta ce su shiga yajin aiki “saboda an ce kar farashin burodi ya wuce N400″, amma farashin fulawa da sauran kayan hadin sai kara hauhawar suke yi.

Kuma farashin burodin sai karuwa yake yi a Kano da Abuja, wanda kungiyoyin masu sayar da shi ke dangantawa da tsadar fulawa da kayan hadinta.

Aminiya ta rawaito cewar karin farashin ya fito karara ne a wata ranar Lahadi a Jihar Kano.

Sakataren Kungiyar masu burodi na Kano, Kabiru Hassan Abdullahi, ya ce dole ne a kara farashin domin kauce wa faduwa.

“Gaskiya ne mun kara kudin burodi ranar Lahadi. karin ya zama dole saboda muna yin kasuwanci ne domin riba amma sai aka kara kusan N4,000 kan kowane buhun filawa”, inji Abdullahi.

Burodi abincin gidaje da dama ne a Najeriya. Kuma ya fi sauran abinci saurin samu da saffarawa. Za a iya samunsa a gidajen masu kudi ko talakawa. Kuma kowa na samun sa ya siya daidai karfinsa.

Haka nan kuma kamfanonin burodi da na fulawa na samar da ayyukan yi ga jama’a; Kama daga ma’aikata da masu rarrabawa da masu sayarwa da masu tallar sa a kan hanya da sai sauransu.

Rahotanni sun yi nuni da cewa Najeriya ita ce ta 12 wajen cin taliya a duniya inda take da akalla mutum biliyan 2 masu cin taliya a duk shekara.

Haka nan kuma an ce Indiyawa ke juya kasuwar biliyoyin Daloli a Najeriya inda kamfanin Indomie Noodles da Dufil ke kwashe fiye da kashi 70 na kasuwar taliyar a cikin kasar.

An kuma yi kiyasin cewa kashi 99 na kayan yin abubuwan dangin fulawa da suka hada da fulawar biredi da filawar taliya da Semolina da nauyinsu ya kai Metric tons 5.67, kuma kudin su ya kai Dala biliyan 4.48, ana shigowa da su ne daga kasashen waje a duk shekara, kuma babu wani yinkuri da ake yi na habbaka samar da kayan a cikin gida.

Hukumar Kiddidiga ta Kasa (NBS) ta ce alkama ce ta shida a cikin abubuwan da aka shigowa da su Najeriya a zangon farko na shekarar 2020.

Su kuma manoma sun ce ba su da karfin noma alkamar da za su wadata kamfanonin filawar.

Alkalumma sun yi nuni da cewa daga watan Janairu zuwa Maris na 2020 an shigo da alkama da kudinta ya kai Naira biliyan N101.58.

Takardun bayanin da aka samu daga hannun ma’aikatan kamfanonin filawar sun yi nuni da cewar kamfanoni hudu a Najeriya suna murza metric tons 30,032 na filawa a masana’antunsu.

Babban kamfanin shi ne Flour Mills of Nigeria (FMN) da ke dauke da kashi 39 cikin da dari; sai Crown Flour Mills (Olam) da ke biye da shi da kashi 38 cikin dari.

Wadannan kamfanoni ne ke da kashi 77 cikin dari na kasuwar fulawa a Najeriya.

An kuma ce kamfanin Olam ya mallaki kamfanoni uku da suka ba shi damar zama babban kamfanin fulawa a Najeriya. Ya sayi Crown Flour Mill (CFM) daga hannun ‘yan Lebanon a 2010, sai BUA Flour Mill daga hannun Abdussamad Isiyaka Rabiu a 2015 da kuma Dangote Flour Mills cikin shekarar 2019.

Honeywell Flour Mill, wanda shi ne kamfanin da ‘yan Najeriya ke takama da shi yana dauke ne da adadin kashi 9 cikin dari na fulawar da ake murzawa a kasa da nauyin ta zai kai metric tons 2,600.

Dufil Group, wanda Indiyawa ke da shi yana da kashi 8 cikin dari na fulawar da ake murzawa sai dai kuma shi ya ke da kashi 70 na kasuwar taliya na Najeriya.

Sai kuma Life Flour Mill, wanda shi ma na baki ne, yana da kashi 4 cikin dari, yayin da Kings Floury Mill yake da kashi 2 cikin dari.

Najeriya ta gaza kare ‘yan kasarta

A Najeriya, kamfanonin kasashen waje sun yi kakagida a kasuwar fulawa tare da tsawwala farashinta da sauran kaya danginta, ba kamar a kasar Ghana ba da take kula da farashin domin hana tsadar kaya.