✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda bikin maulidin bana ya kayatar

Ranar Lahadin da ta gabata ita ce ranar 12 ga Rabi’ul Auwal wadda rana ce da al’ummar Musulmin duniya ke bikin tunawa da ranar haihuwar…

Ranar Lahadin da ta gabata ita ce ranar 12 ga Rabi’ul Auwal wadda rana ce da al’ummar Musulmin duniya ke bikin tunawa da ranar haihuwar Manzon Allah Annabi Muhammadu (SAW).

A ranar Musulmi sukan dafa abinci iri-iri suna raba wa ga makwabta da ’yan uwa da sauran mabukata tare da ziyartar ’yan uwa da gidajen marayu da asibitoci da gidajen yari

A Jihar Bauchi, tun sanyin safiya daruruwan dalibai ’yan makaranta da masu waken yabo da zakiraisuka fara tururuwa don fara jerin gwanon bikin.

Daliban wadanda suka sha ado  wadansu a kan dawaki da motoci da babura da masu tafiya a kafa, garin Bauchi ya cika makil, lamarin da ya jawo ’yan kasuwa suka rika rufe shagunansu, masu ababen hawa suka kaurace wa hanyoyin cikin gari saboda cinkoson mutane masu jerin gwano da masu kallo.

Mai martaba Sarkin Bauchi Alhaji Rilwanu Suleimanu Adamu ya karbi gaisuwa daga masu mauludin a fadarsa yayin da Gwamnan Jihar Bauchi Sanata Bala Mohammed ya halarci mauludin da Sheikh Dahiru Bauchi ya jagoranta a ranar Asabar, 11 da dare a filin wasa na Abubakar Tafawa Balewa da ke Bauchi, wanda ya cika makil da jama’a.

A jawabinsa a wajen maulidin, Gwamna Bala Mohammed ya ce bai taba ganin taro da dandazon jama’a irin wanda ya gani a wannan wuri ba. Ya ce hakika taron ya kara masa imani da tsoron Allah, sai ya shawarci al’ummar jihar su rika koyi da halayen Manzon Allah Annabi Muhamamadu (SAW).

Gwamna Bala ya hori al’umma su zauna lafiya da juna ba tare da la’akari da bambancin addini ko kabilanci ba, sannan su rika dabbaka halayen gaskiya cikin al’amuransu.

A jawabin, Sheikh Dahiru Bauchi ya gode wa Allah da Ya sake zagayo da wannan babbar rana, inda ya karanta tarihin Manzon Allah (SAW) tun daga haihuwarsa har zuwa wafatinsa da kuma irin jagoranci da khalifofinsa hudu suka yi a bayansa.

Sheikh Dahiru Bauchi ya nuna muhimmancin yin maulidin Annabi wanda ya ce shi ne yake nuna hadin kai da karfin Musulunci da kuma nuna farin cikin samuwar Manzon Allah, sannan ya ce duk Idin da ake yi a duniya babu Idin da ya kai na samuwar Manzon Allah (SAW).

Ya jawo hankalin gwamnatoci a dukkan matakai su rika bai wa dukkan ’yan kasa ’yancin gudanar da addininsu ba tare da wata tsangwama ko tarnaki ba kamar yadda Allah Ya ba su ’yancin yi kuma dokar kasa ta ba su.

A birnin Ibadan, Musulmi sun bi sahun ’yan uwansu na kasashen duniya wajen gudanar maulidin na bana a ranar Lahadin da ta gabata.

Muhimman abubuwan da aka gudanar domin girmama wannan rana sun hada da fitowar Musulmi maza da mata manya da yara cikin sababbin tufafi inda suka yi jerin gwano a karkashin jagorancin halifofin darikun sufaye da shugabannin makarantun Islamiyya suka yi doguwar tafiya suna zikiri da wakokin yabon Manzon Allah (SAW).

Tun daga ranar da Majalisar Koli ta Addinin Musulunci ta bayar da sanarwar ganin jaririn watan Rabi’u Awwal, manyan malamai da masana da kungiyoyin addinin Musulunci suka rika shirya tarurrukan lacca a ranaku daban-daban domin tunatar da Musulmi muhimmancin samar da ilmi ga ’ya’yansu da kyautata zamantakewa da rikon amana da hakuri tare da girmama dokoki da rokon Allah Ya samar da mafita ga Najeriya.

A sakonsa ga al’ummar Musulmin Jihar Oyo, Gwamna Seyi Makinde ya yi kira ga mabiya addinai su yi hakuri da juna domin samun ci gaban jihar da kasa baki daya. Sarakuna da manyan malamai sun yi irin wannan kira musamman wajen neman a yi koyi da halayen  Annabi Muhammadu (SAW).

A Jihar Legas, Sarkin Hausawan Agege Alhaji Muhammadu Musa Dogonkadai ya yi kira ga al’ummar Musulmi su zamo masu son zaman lafiya da son juna su kasance masu kyawawan dabi’u da mu’amala a tsakaninsu da kuma tsakaninsu da wadanda ba Musulmi ba, “Mun gode wa Allah da Ya sake nuna mana wannan lokaci da mu al’ummar garin Agege ke taruwa domin tunawa da ranar da aka haifi Annabinmu fiyayyen halitta. Muna fata Allah Ya yi mana albarka a garinmu na Agege da kasarmu baki daya, Allah Ya ba mu zaman lafiya da wadata,” inji shi.

Shugaban Karamar Hukumar Agege Mista Kola Egunjobi wanda yana daga cikin wadanda suka yi zagayen maulidin na bana a Agege ya shaida wa Aminiya cewa sun fito zagayen ne kwansu da kwarkwata domin nuna farin cikinsu da zagayowar watan da aka haifi fiyayyen halitta, inda ya ce al’ummar Agege kansu a hade yake, “Yarbawanmu da Hausawanmu da sauran kabilun wannan gari namu har da wadanda ba Musulmi ba mun fito domin nuna murna, wannan manuniya ce ta hadin kai a tsakanin al’ummar Agege,” inji shi.

Zagayen maulidin wanda shi ne karo na 10 da Kungiyar Ahbabi Rasulullahi ke shiryawa ya samu halartar dubban mutane.

Shugaban Kungiyar Alhaji Isma’il Ibrahim Nayaya ya ce sama da makarantun Islamiyya 50 da kungiyoyi 100 ne suka yi rajistar ’ya’yansu domin yin zagayen mauludin na ban, inda ya ce a baya jama’ar garin Agege kadai ke halartar zagayen, amma a yanzu suna samun baki daga Arewa da kuma kasashen ketare da suka hada da Ghana da Benin da Togo. “Muna yin zagayen ne tare da amincewa da kuma sahalewar Gwamnatin Jihar Legas, wadda ta suke ba mu jami’an tsaro da ke yin aikin tsaro a lokacin zagayen,” inji shi.

Sarkin Yarbawan kasar Ghana ta Tsakiya Alhaji Abdusalami Saka na daya daga cikin wadanda suka halarci zagayen maulidin na Agege daga kasashen ketare, ya shaida wa Aminiya cewa ya gode wa Allah da ya samu damar halartar zagayen maulidin na bana. “Domin a bara ma an gayyace ni sai dai ban samu ikon zuwa ba, amma a bana na zo na ga abin mamaki, na kuma ji dadi, mu ma za mu kwaikwaya mu rika yin irin haka a Ghana, domin wannan abu ne da ke kulla zumunta a tsakanin jama’a,” inji shi.

A zagayen maulidin na Agege na bana, mutanen yankin Unguwar Markas a cikin taswirar inda za a kewaye, domin unguwar na cikin yankunan da suka shahara da al’ummar Hausawa da farko sun nuna takaicinsu na cire unguwarsu, sai dai wadanda suka shirya zagayen sun ba da dalilansu na cire unguwar kan dalilan tsaro. Sannan Sarkin Hausawan Agege, Alhaji Muhammadu Musa Dogonkadai ya bayyana cewa idan Allah Ya yarda badi za a yi zagayen har a Unguwar Markas.