✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda dan kwallo ya kashe kocinsa a Kano

A ranar Asabar din da ta gabata ce aka zargi wani matashi mai suna Salisu Mohammed ya kashe ubangidansa Koci Mujitapha Musa (Mato) a Unguwar Yakasai…

A ranar Asabar din da ta gabata ce aka zargi wani matashi mai suna Salisu Mohammed ya kashe ubangidansa Koci Mujitapha Musa (Mato) a Unguwar Yakasai a Karamar Hukumar Birni da Kewayen Kano kan rashin fahimta da ta shiga tsakaninsu game da wasan kwallon kafa.

Binciken Aminiya ya gano cewa rigima a tsakanin matasan biyu ta faro ne wata takwas da suka gabata inda marigayi Koci Mujitapha mai kimanin shekara 30 ya kori Salisu Mohammed mai kimanin shekara 18 daga kulob dinsa na  Home Base sakamakon nuna halin rashin da’a da wanda ake zargin yake yi a koyaushe.

Majiyar Aminiya ta ce haushin korar da marigayin ya yi wa dan wasan ne ya sanya ya kullace shi inda ya sha alwashin ganin bayan kulob din da kuma marigayin gaba daya.

Yahaya Ibrahim mazaunin Unguwar  Yakasai ya yi wa Aminiya karin haske cewa “Ya kasance duk lokacin da kulob din maigayin yake yin wasa, Salisun zai je wurin ya yi ta nuna adawarsa ga kulob din domin har golan kulob din yake ja wa riga. Hakan ya sa marigayin ya yi masa gargadi amma bai daina ba.”

A cewar Yahaya a ranar da waki’ar ta auku kulob din marigayin ya gudanar da wasa da yamma a filin unguwar kuma wanda ake zargin ya halarci wurin yana tsokanar ’yan wasan kulob din kamar yadda ya saba, take suka fara fada da marigayin sai da ’yan   unguwar suka shiga tsakaninsu. “To bayan an yi haka da daddare kuma bayan an fito daga kallon wasan kwallon kafa na El Classico a tsakanin kulob din Real Madrid da FC Barcelona da ke Sifen, sai marigayin ya tafi filin unguwar ya zauna yana cin abinci sai ga Salisu ya zo ya same shi yana tsokanarsa yana yi masa habaici. Hakan ya fusata marigayin ya tashi ya mammare shi. Ashe Salisu yana da wuka a jikinsa sai ya zaro ya daba masa a kirji. Sai mutanen da suke kofar wani gida suka hango abin da ke faruwa suka zo suka rike Salisu lokacin da yake kokarin gudu inda suka mika mini shi na rike shi har sai da na kai shi ga ’yan sanda. Shi kuma marigayin sai jiri ya debe shi ya fadi kasa yana dafe da kirjinsa kafin a samo mota don a kai shi asibiti sai ya fara aman jini. Bayan da aka samo mota ne aka  kai shi Asibitin Murtala inda tun kafin a isa rai ya yi halinsa,” inji shi.

Marikin marigayin mai suna Malam  Ibrahim Muhammad ya shaida wa Aminiya  cewa har ya fara barci aka sanar da shi game da lamarin. “Da misalin karfe 11:00 na dare iyalina ta tashe ni ta gaya mini cewa ga shi can an soka wa Mujitapha wuka har yana aman jini, hakan ya sa na tashi na fita don in ga abin da ke faruwa sai dai lokacin da na je na tarar an kai shi asibiti,” inji shi.

Malam Ibrahim ya bayyana marigayin a matsayin yaro nagari wanda ba ya da abokin fada a cikin abokansa ballantana na kasa da shi.

Wanda ake zargi da kisan, Salisu Mohammed ya shaida wa Aminiya cewa “Mun samu sabani da marigayin a kan wani wasa da na yi inda kulob din marigayin ya sha kasa hakan ya sa ya zage ni. Ni kuma na tube rigar kwallon da nake yi wa kulob dinsa wasa na bar filin saboda haushi.  Daga nan ne na fita daga kulob din marigayin na koma na adawa.

To ranar Asabar da ta wuce kulob dinsa ya yi wasa ni kuma na je na tsokane su to a nan ne marigayin ya yi mini barazana cewa idan ya kama ni sai ya yi min dukan tsiya. To da daddare bayan mutane suna dawowa daga gidan kallon wasan Madrid da Barcelona sai kawai marigayin ya mare ni ya kuma rike ni hakan ya sa na zaro wata wuka na soka masa a kirji.”

DSP Haruna Abdullahi Kiyawa shi ne Kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Kano ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya ce da zarar sun kammala bincike za su gurfanar da wanda ake zargin gaban kuliya.