Da Dumi Dumi

Yadda fadan ’yan dako ya koma rikicin kabilanci a Legas

Sarkin Hausawan Alimosho, Alhaji Haruna Kuraja da dogarinsa lokacin da ya ziyarci wadanda suka jikkata a Babban Asibitin Ikeja a Legas
Sarkin Hausawan Alimosho, Alhaji Haruna Kuraja da dogarinsa lokacin da ya ziyarci wadanda suka jikkata a Babban Asibitin Ikeja a Legas

A ranar Lahadin da ta gabata ce wani rikici mai nasaba da kabilanci ya barke a Kasuwar Kayan Gwari ta Ileko da ke Oke Ado a Karamar Hukumar Alimosho a Jihar Legas, lamarin da ya yi sanadiyyar jikkatar jama’a da dama baya ga dimbin dukiya da ta salwanta.

Wakilin Aminiya da ya ziyarci kasuwar lokacin da lamarin ya faru, ya iske dimbin jami’an tsaro  a kasuwar, yayin da wadansu daga cikinsu ke kai-komo, kuma a bangare guda wadansu ’yan kasuwa suna kwashe ragowar hajarsu da aka yi fatali da ita lokacin rikicin. Kayayyakin da suka hada da kayan miya da gari da manja da makamantansu suna warwatse a hanya.

Aminiya ta zanta da wadansu ’yan kasuwar, wadanda suka ce rikicin ya samo asali ne sakamakon sabani a tsakanin wadansu ’yan dako a kasuwar su biyu.

Malam Zulkifulu Adam ya  ce rikicin ya taso ne a tsakanin wadansu ’yan dakon lemo. “Irin ’yan dakon nan ne masu daukar buhun lemo a bayansu, wadansu kuma a ka. To daya daga cikinsu ya dauko  lemon a kansa dayan kuma a baya, suna tafe sai daya ya ture dayan ya fadi kasa. Sai fada ya kaure a tsakaninsu. Daya Bayarabe ne daya kuma Bahaushe, to sai Bayaraben ya buge abokin sana’arsa kuma dama ya fi shi karfi ya kuma rufe shi da duka har ya suma. Da ’yan uwansa suka ga haka sai suka kama Bayaraben suka yi ta jibga, suka hau da shi saman bola suna yi ta jibgarsa, sai ’yan uwan Bayaraben sai suka yi zuga don rama wa dan uwansu. Nan da nan sai rikici ya barke, ana jifar juna da duwatsu ana zubar wa jama’a kaya, wadansu kuma suna kwasar ganima,” inji shi.

Ya ce “Ganin rikicin zai kazanta ne sai shugabannin kasuwar suka sanar da ’yan sanda a ofishinsu da ke daura da kasuwar. Lokacin da ’yan sandan suka zo sai suka nufi saman bolar inda matattara ce ga matasan da ke sana’a a kasuwar da masu sana’ar gwangwan. Ko da ’yan sandan suka isa wajen tare da ’yan dabar Yarabawa da ke biye da su sai suka cinna wa wajen wuta, suka kone wa jama’a dakunan kwanansu, kuma akasari a cikin wadannan dakunan jama’a ke ajiyar kudinsu na kasuwanci. Ana cikin haka sai ’yan sandan suka fara harbin kan mai uwa da wabi, kafin daga bisani lamarin ya lafa.”

ADVERTISEMENT

Ya ce rikincin ba na kabilanci ba ne domin ’yan kasuwar zaune suke lafiya da abokan kasuwancinsu Yarabawa. “Ka ga nan rumfunanmu ne da aka zo za a kone su Yarbawan ne suka hana, suka ce ba za a kone mana shagonmu ba. Don haka ba rikicin kabilanci ba ne amma ya kusa ya juye ya zama haka,” inji shi.

Lokacin da wakilin Aminiya ya isa kasuwar ta Ileko, ya iske shugabannin kasuwar da jam’ian tsaro suna kokarin kwantar da hankalin jama’a, inda shugabannin kasuwar a karkashin jagorancin Sarkin Hausawan Alimosho, Alhaji Haruna Kuraja da Alhaji Ado Shu’aibu Dansudu suka yi taron zaman lafiya a ofishin ’yan sandan da ke daura da kasuwar tare da ’yan sanda da suka hada da shugaban ayarin tsaron hada-ka ta ko ta-kwana ta Jihar Legas da manyyan ’yan sanda da suka hada da Mataimakan Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Legas. Bayan kammala taron ne sai suka umarci shugabannin su yi magana da al’ummarsu domin kwantar da hankalinsu.

Sarkin Hausawan Alimosho, Alhaji Haruna Kuraja da Alhaji Ado Dansudu sun taro ilahirin matasan kasuwar, suka kwantar musu da hankuli tare da gargadin  su guji fitina, su kasance masu son zaman lafiya, su kuma yi hakuri da asarar da ta auka musu, sakamakon rikicin. Sun ba su tabbacin cewa za su yi kokarinsu don ganin sun tallafa wa wadanda suka yi asara.

Sarkin Hausawan ya shaida wa Aminiya cewa an tafka asara  da dama a rikicin, domin dakunan jama’a da aka kone da yawansu a ciki suke ajiyar dukiyarsu.

“Da yawansu sun rasa jarinsu, wani Naira miliyan daya wani biyu, suna nan da dama. Yawancinsu za ka ga matasa ne da ya kamata a ce suna gida Arewa suna karatu amma sakamakon matsin rayuwa sai suke zuwa nan Kudu domin yin sana’a ko kasuwanci. Kuma in ka lura, za ka ga suna kokarin neman na kansu amma sai ga shi hakan ta faru. Wannan kaddara ce, za mu rungume ta a haka,” inji shi.

Alhaji Ado Shu’aibu Dansudu, daya daga ciki iyayen kasuwar ta Ileko ya shaida wa Aminiya cewa sun gode wa Allah da Ya takaita rikicin kafin ya kai ga yaduwa zuwa wajen kasuwar. Ya dora laifin matsalar ga yadda ’yan sanda suka yi kame a bangare guda kadai.

“Rikici ne da ya shafi bangare biyu na matasan ’yan kasuwa ’yan Arewa da yaran Yarabawa ’yan daba masu zaman banza, amma sai ’yan sanda suka kama ’yan kasuwarmu kadai, wadanda su ne aka yi wa barna, aka kone musu rumfuna, aka ji musu rauni, suka yi asarar dukiyarsu. A cikinsu ne kadai ’yan sandan suka yi kame, in ban da rashin adalci ta yaya za a yi rikicin bangare biyu a kama ’yan bangare guda kadai?

Don haka ya kamata a yi adalci, su ma wancan bangaren a kama su ko a sako mana namu da aka kama. In ban da rashin adalci, wanda ya zo ya yi barna a kyale shi ba a kama shi ba, ba a hukunta shi ba, ai an ce gobe ya je ya sake yin barna ke nan,” inji shi.

Yadda aka varnata kayan gwari a Kasuwar Ileko da ke Legas yayin rikicin
Yadda aka varnata kayan gwari a Kasuwar Ileko da ke Legas yayin rikicin

A sanarwar da Kakakin  Rundunar ’Yan sandan Jihar Legas ya aiko wa Aminiya, ya ce jami’an rundunar sun yi namijin kokari, wajen kwantar da rikicin kafin ya kai ga yaduwa. Ya ce rikici ne da musabbabinsa bai taka kara ya karya ba amma sai ya nemi ya koma na kabilanci.

“Zuwa yanzu an kwatar da tarzomar, mun kuma kama mutum biyar da ake zargi da hannu a rikicin, wadanda suka hada da Kabiru Muhammed da Kabiru Adamu sai Bashiru Muhammed da Salihu Madu da Yusuf Amuda, ba a samu asarar rai a tarzomar ba, amma mutum hudu sun jikkata, wadanda ake kula da lafiyarsu. Za a gabatar da wadanda ake zargi a gaban kotu da zarar an kammala bincike,” inji shi.

Wakilin Aminiya ya ziyarci Asibitin Tarayya da ke Ikeja GRA, inda aka kwantar da daya daga cikin wadanda suka jikkata, wanda harsashin kan mai uwa da wabi ya same shi, inda ya iske shi kwance, an daure masa ciki, yayin da yake ta zubar da jini, a daidai lokacin da likitoci ke kai-komo a kansa. Dan uwansa da ke jinyarsa mai suna Umar Lawal ya shaida wa Aminiya cewa sunan majinyacin Mahadi Lawal kuma dan dako ne a kasuwar ta Ileko. Ya ce tsautsayi ne ya rutsa da shi ya bi ta wajen da ake rikicin har harsashin ’yan sanda ya same shi, ya huda shi ta baya ya fita ta cikinsa.

“Da farko mun kai shi Babban Asibitin Oke-Odo sai suka ki karbarsa, daga baya muka mayar da shi ofishin ’yan sandan. Sai da muka yi da gaske suka ba mu takarda wadda da ita ce aka karbe shi a wannan asibiti. Bayan zuwanmu, likitoci na kokarin ceton rayuwarsa amma kasancewar ba mu da karfi muna bukatar taimako, domin mun kashe ilahirin kudin da abokansa suka hada. Akwai lokacin da aka bukaci za a yi masa karin jini leda uku, Sarkin Hausawan Alimosho Alhaji Haruna Kuraja ne ya taimaka mana da Naira dubu 20 sai uban kasuwar Alhaji Ado Dansudu, shi ma haka.

“A lokacin da suka zo duba shi a daren Lahadi, ranar da aka kawo shi asibitin, jami’an ’yan sandan yankin su ma sun zo duba shi amma ba su ba da ko kwabo ba zuwa yanzu. A cikin kwana biyu, mun kashe sama da Naira dubu 200. Don haka muna fata gwamnati da rundunar ’yan sanda su tallafa a ceto rayuwarsa,” inji shi.

Wakilin Aminiya ya sake ziyartar kasuwar ta Ileko bayan kwana guda da rikicin, inda ya iske jama’a na ci gaba da harkokin kasuwancinsu, kamar yadda suka saba.

Share