Search
Subscribe
Yadda gobara ke addabar Kasuwar Katako ta Jos

Wani bangare na kasuwar ‘yan katako da ya kone

Yadda gobara ke addabar Kasuwar Katako ta Jos

Kasuwar Laranto ko Kasuwar Katako da aka fi kiranta da ke garin Jos fadar Jihar Filato, kasuwa ce da aka kafa kusan shekara 44 da suka gabata. Kasuwar wadda ta fi kowace kasuwa girma a garin Jos, ta kunshi bangarori  32 da suka hada da ’yan gwanjo da ’yan katako da ’yan hatsi da ’yan tukwane da ’yan lemo da ’yan goro  da sauransu.

Babban abin da ke damun kasuwar tun kafuwarta, shi ne  yawan  tashin gobara da ake samu. Domin an samu tashin gobara a lokuta da dama a kasuwar.

A tashe-tashen gobarar da aka rika samu, an yi asarar miliyoyin Naira na kayayyakin ’yan kasuwa  da suka kone.

Wani dattijo mai shekara 72 da mai suna Alhaji Aliyu Umar da yake kasuwar, ya bayyana cewa an fara raba wa ’yan kasuwar filin da suka gina shaguna ne  tun a 1970.

Ya ce ’yan kasuwar goro ne suka fara zama a  kasuwar, don gudanar da harkokin kasuwanci. Ya ce an fara samun tashin gobara a kasuwar ce tun tana da shekara 8 da kafuwa. Kuma sau 15 ke nan ana samun tashin gobara a bangaren ’yan katako kadai na kasuwar.

Alhaji Aliyu Umar ya ce zuwa  yanzu an samu tashin  gobara  sau 30 ke nan, tun daga  kafuwar kasuwar.

Ko a makon jiya an sake samun tashin gobara a kasuwar a bangaren ’yan katako,  inda rumfuna 44 suka kone tare da kayayyaki na sama da Naira miliyan 31.

Da yake zantawa da wakilinmu kan tashin gobarar, Shugaban Kasuwar ’Yan Katako na Hausa Lane, Alhaji Yusuf Aliyu  ya ce   yana  zaune a gida, sai ya ji an kira shi a waya da  misalin karfe 12 na daren ranar Alhamis, ana ce masa  gobara ta tashi a kasuwarsu ta ’Yan Katako.

Ya ce kafin ya iso kasuwar jami’an kashe gobara sun isa kasuwar suna ta kokarin kashe gobarar.

Ya ce bayan da gari ya waye, sun yi lissafi sun gano rumfuna  44 ne suka kone a gobarar. Kuma sun yi asarar dukiya ta sama da Naira miliyan 31 a gobarar na kayayyakinsu da suka kone.

Ya ce a  wannan bangare na ’Yan Katako  an  yi gobara kamar sau 4 a cikin shekara 8.  Don haka ya roki gwamnati ta gina shaguna a kasuwar, ta yadda gobara ba za ta rika yawan tashi ba.

Har ila yau ya yi kira ga  kamfanin rarraba  wutar lantarki na Jos, ya sanya musu wani abu da za su rika katse wutar lantarki a kasuwar,  idan sun tashi da yamma. Ta yadda ko an kawo wuta da daddare babu abin da zai faru.

Shi ma a zantawarsa da wakilinmu Shugaban Kasuwar na Bangaren ’Yan Katako baki daya Mista  Eze Echezona, ya bayyana cewa sun yi godiya ga Allah da Ya sa ba a rasa rai ba a wannan gobara. Ya ce amma sun rasa dukiya ta miliyoyin Naira a gobarar.

Eze Echezona ya ce a duk Jos babu kasuwar da ta kai kasuwar girma. Domin akwai dubban mutane da suke cin abinci a  kasuwar. Don haka duk wani abu da ya samu kasuwar, ya shafi dubban al’umma ne.

Ya ce babban abin da yake yawan kawo tashin gobara a kasuwar, shi ne akwai injinan da ake aiki da su a  kasuwar kuma suna aiki da wutar lantarki, don haka idan an kawo wuta da daddare, lokacin da mutane ba sa kusa sai wuta ta yi tartsatsi ta zube a kasa, daga nan sai  gobara ta tashi.

A zantawarsa da wakilinmu daya daga cikin dattawan kasuwar Alhaji Sulaiman Mu’azu ya bayyana cewa tunda aka fara samun gobara a kasuwar, gwamnatin Jihar Filato ba ta taba tallafa musu ba.

Ya ce amma sun taba  samun tallafi daga waje inda tsohon Gwamnan Jihar Sakkwato Alhaji Dalhatu Bafarawa ya tallafa musu da Naira miliyan 20.

Ya ce a  wannan gobara da aka yi Sadik Plaza ya tallafa masu  da Naira miliyan daya.  Kuma a wannan karo suna ganin alamar gwamnatin Jihar Filato za ta tallafa musu domin har Sakataren Gwamnatin Jihar ya kai musu  ziyarar jaje kan abin da ya faru.

Wani mai shago a  kasuwar mai suna Chunmada Maji ya bayyana cewa, dukkan kayayyakin aikin yin kujeru da ke shagonsa sun kone a gobarar.

’Yan kasuwar da dama sun tabbatar da cewa wutar lantarki ce da aka kawo a cikin dare  ta yi sanadin wannan gobara.

Wani dattijo mai shekara 62 mai suna Yakubu Hassan Bade wanda yake da shago a kasuwar tun 1976, ya ce wannan gobara ita ce ta 5 da ta tashi a kasuwar ta ’yan katako. Ya ce shi kafinta ne a kasuwar yana yin kofofi da gadaje da kujeru. Ya ce ya rasa dukkan kayayyakin shagonsa a gobarar.

Kakakin  Rundunar ’Yan sandan Jihar Filato,  DSP Tyopeb Tern ya tabbatar da cewa gobarar ta kone shaguna da dama. Amma babu  wanda ya rasa ransa ko ya ji rauni a gobarar.

Wakilan Gwamnatin Jihar Filato a karkashin jagorancin Sakataren Gwamnatin Jihar,  Farfesa  Danladi Atu,  sun kai ziyarar jaje ga ’yan kasuwar kan wannan al’amari da ya faru.

Sakataren Gwamnatin ya bayyana wa ’yan kasuwar cewa Gwamnan Jihar Simon Lalong ya nuna juyayinsa, kan wannan abu da ya faru musamman ganin irin asarar da aka yi, da kuma yadda dubban mutane suke samun abin da za su ci a kasuwar.

Ya bai wa shugabannin ’yan kasuwar tabbacin cewa zai mika wa Gwamnan bukatar tallafin da suka nema.

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin