✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda Hukumar VIO ke mana rashin adalci – Direbobin KEKE-Napep

Kungiyar masu KEKE-Napep ta kasa reshen Babban Birnin Tarayya Abuja sun koka kan yadda Hukumar Kula da Lafiyar Ababen Hawa wato (VIO) ke musu tara…

Kungiyar masu KEKE-Napep ta kasa reshen Babban Birnin Tarayya Abuja sun koka kan yadda Hukumar Kula da Lafiyar Ababen Hawa wato (VIO) ke musu tara ta rashin adalci wanda hukumar take cin tarar su har Naira 20,550 kan kowane babur da aka kama wanda suka ce tarar akwai rashin tausayi a ciki.

Da yake zantawa da Aminiya, Mai Magana da Yawun Kungiyar Alhaji Muhammad Kachalla cewa ya yi, “Jami’an VIO suna takura wa ’yan kungiyarmu da yawan kame da kuma tara mai tsanani da ke kai Naira 20,550 a kan kowane KEKE-Napep da aka kama, wannan tarar ta yi yawa kwarai da gaske ko motoci akeyi wa wannan tarar ba za su jure ba ballantana mu.’’

Kachalla ya yi karin haske a kan irin kudade da ake karba a hannunsu ta bayan fage:  “Ranar 8 ga watan Mayun bana, wani mai suna Shehu Ma’aikaci a hukumar ya kama mana KEKE-Napep guda 11, sai da yaranmu suka hada masa kudi Naira 10,000 a kan kowane guda daya, inda ya karbi kudi kimanin Naira 110,000 sannan ya sakar musu da misalin karfe 10 na dare.’’

Sai kuma kame na biyu da ya ce an yi musu a daidai Arab da ke yankin Utako da misalin karfe 6 na safe, inda suka kama KEKE-Napep guda 11.

Kachalla ya bayyana cewa, “mun samu mako daya tsakanin kame na farko da na biyu, inda Shehu ya sake jagorantarsu. Sai ya ce zai kai mu kotu mu biya tarar Naira 20,550. Kuma mun tambaye shi laifin da muka yi ya ce an hana mu aiki a yankin Utako.

“Mu kuma da izinin hukuma muke yi domin idan mun karya doka ai da ’yan sanda sun rika kama mu. Idan laifi muka yi ma ai wannan tara ta yi yawa kuma ya kamata a fada mana irin laifin mu da ya sa ake yanke mana irin wannan tara,’’ inji shi

Wakilin Aminiya ya tuntubi mai Magana da Yawun Hukumar VIO da ke Abuja, Mista Kalu Emetu a kan faruwar wannan lamarin kuma ya tabbatar da cewa hakika mutanensu sun kama KEKE-Napep 11 bisa karya dokokin hanya da suka yi, “Jami’anmu sun kama wadannan KEKE-Napep 11 sakamakon karya dokokin hanya da suka yi, kuma an rubuta musu tara su je su biya kamar yadda ake yi wa duk wanda ya karya dokar hanya’’ inji shi.

Game dakudin tara kuma da aka ce sun yi yawa sai ya ce “kotu ce ta yanke musu wannan tarar wacce ake kira da ‘kotun tafi da gidanka’ tarar Naira 20,550 a kan kowane KEKE-Napep daya.”

Game da wadanda ke da alhakin kame da tara, sai ya ce, “Ministan Babban Birnin Tarayya Abuja shi ne ya nada wadannan mutane na musamman da ake kira Task Force domin dakile masu karya dokokin hanya.’’