Search
Subscribe
Yadda jihadin dan Fodiyo ya je Zazzau

Yadda jihadin dan Fodiyo ya je Zazzau


Na Sadik Tukur Gwarzo daga shafin kasar Zazzau a jiya da yau


Sabanin yadda jihadin fulani ya auku a Kano wajajen shekara ta 1803-1804, jihadi a kasar Zazzau bai auku ba sai a wajajen shekarar1808.

  Dalilin haka kuwa shi ne karbar kiran limamin yakin wato Shehu Usmanu dan Fodio da sarkin kasar Zazzau Isyaku Jatau ya yi a zamanin rayuwarsa.

   Sarki Jatau ya aike wa shehu Usmanu sakon mubaya’arsa a lokacin da Shehun ya yi hijira zuwa Gudu. Haka kuma ya aike wa malamai masu yakin jihadi a Kano bukatar aiko malami gare shi wanda zai koyar da su addini, inda aka ce jakadun sarkin sun hadu da malaman jihadin Kano a gundumar karaye, har kuma suka aike da Malam dan Zabuwa da wasu mutane gare shi.

  Daga baya Malam dan Zabuwa ya fada ga malaman jihadi cewar lokacin da ya riski fadar Zazzau, ya tarar da Sarki Jatau bisa karagar mulki, sanye da rawani na mabiya sunni irin wanda Shehu Usmanu ya kawo, sabanin rawanin habe da sarakunan Hausawa ke sanyawa kafin zuwan Shehu.

   Sai dai wannan abu ya tayar da kura a Zazzau. Mutane da yawa ba su ji dadin yadda sarki Jatau ya bijire wa al’adun da ya gada ba ya koma kan abin da Shehu ya zo da shi. Haka kuma yadda ya sa aka rushe wurin bautar Iskokai tare da maishe su Masallatai ya yi wa mutanen Zazzau ciwo, ciki har da manyan fadawa masu fada a ji ga Sarki.

  A kan haka aka ce wasu kusoshi a daular irinsu Magajiya, da Iya da Shebagu da Wagu suka rika hada kan mutane domin yi wa sarkin bore ko kuma a tilasta masa komawa tsohuwar al’ada, amma sarkin ya ki biye musu.

   Ana haka sai sarkin ya gushe, masu zaben sarki suka hadu a kan nada dansa Makau, amma bisa sharadi guda uku.

  Na daya aka ce masa dole ya karya duk wata yarjejeniya da mahaifinsa Jatau ya yi da Tubake, wato musulmi mabiya koyarwar shehu Usmanu dan Fodio.

  Na biyu dole ya hukunta wadanda suka dora sarki Jatau bisa wannan tafarki na bijere wa abin da kakanninsu suke yi a Zazzau ,musamman limamin kona da Limamin Juma.

  Na uku dole ya rushe masallatai da Sarki Jatau ya yi, ya maishe su wurin bautar iskokai kamar yadda suke a baya.

  darewar sarki Makau mulkin Zazzau ke da wuya, abin da ya soma ke nan na kokarin cika wadannan sharuda.

  A kan haka ya sa aka rushe masallatai har da na Jumu’a, aka maishe su wuraren bautar iskokai.

  Sannan ya sa aka kama Liman Malam Muhammadu Lawal aka daure shi a fadan-fadan, daga baya aka kashe shi. Shi kuwa daya limanin, Malam Hamidu mai Jan Rago sai ya gudu ya tsira da ransa.

Koda labarun Wadannan abubuwa suka riski Shehu Usmanu, sai ya hada tawagar mabiyansa karkashin Malam Musa ya turo su Zazzau domin su yi yakin jihadi a nan..  

  A cikin wadanda za su taimaka masa akwai Malam Yamusa, da Malam Abdulkarim, da Malam Abdulsalam wadanda dukkansu sai da su ka yi sarautar zazzau bayan sun samu nasarar karbe iko.

  Sai kuma malamai irinsu Malam Usmanu Sabulu bahaushen Kano wanda ya zamo Katukan Zazzau, da Dokaji bafullatani da aka yi wa sarautar Galadima, da Malam Hamma bahaushen Kano da aka yi wa Dallatun zazzau, da Malam Gabdo bafullatanin ‘Yandoto da ya zamo limamin Zazzau na farko bayan jihadi.

  Sauran kuma mutane ne mabiya shehu Usmanu da suka fito daga wurare daban-daban, misalin Tofa, ‘Yandoto, Borno, Katsinawa, Dan Dorori, Yeskwa, Joli, Gadidi, Bebeji da Zariya.

  Sai dai tun kafin isowarsu har labari ya iske sarki Makau. Don haka ya tara dakaru masu dimbin yawa, ya aike da wasu kimanin dubu 20 garin Hunkuyi domin tarar masu jihadi da daidaita su.

  Hakan kuwa aka yi, domin an gwabza fada da masu jihadi a garuruwan Hunkuyi da Kudan har kuma an kusa cin galaba a kan su, amma cikin ikon Allah sai suka samu taimako daga wasu sarakunan mulki na yankunan.

  Mutum na farko da ya ba su taimako shi ne Dagacin kauyen Durum, wanda ya kubutar da su daga dakarun Makau.

  Na biyu kuma shi ne sarkin Fawan Likoro da ya labarta musu yawan adadin dakarun da ke gabansu a Hunkuyi. Don Haka sai suka yanke shawarar kaurace wa yakin fito na fito, suka sulale ta Kudaru suka shige birnin Zariya ta kofar Bai ba tare da kowa ya sani ba.

   Wasu sun ce Sarki Makau da mabiyansa na cikin gudanar da Sallar Idi masu jihadi suka karbe iko da Zariya, amma saboda hujjar kiyayyar Sarki Makau ga musulunci, wasu suka ce sam ba haka ba ne, yana bayan gari da dakaru yana sauraron ya ji yadda ta kaya tsakanin dakarunsa da masu jihadi sai labari ya riske shi cewa masu jihadi sun karbe ikon garinsa cikin ruwan sanyi.

  Wannan abu sai ya tsorata rundunarsa da shi kansa.

 An ruwaito cewa sai Sarki Makau ya yi kudu tare da wasu tsirarun dakaru da ba su wuce dubu uku ba, ya sauka a garin Kajuru inda dan uwansa mai suna Albarka ke shugabanci.

  Daga nan sai sarki Makau ya bar Kajuru ya tafi Abuja inda ya kafa mulki a can. An ce kuma shi ne dalilin da har yanzu ake kiran sarkin Suleja da Sarkin Zazzau din Suleja.

Shi kuwa Albarka sai ya taho Zariya tare da dan wani malami mai suna Abduljalil da ke karantarwa a Kajuru, suka yi mubaya’a ga Malam Musa, aka kuma karbe su da martabawa.

An ruwaito cewa shi ne aka bai wa Albarka gida a kusa da Fada, kuma daga gare shi sunan Unguwar Albarkawa ya samo asali. 

Shi kuma Ibrahim Tsoho aka ba shi gida kusa da gidan wasu masu Kakaki, kuma daga nan sunan Unguwar Kakaki ya samo asali.

 Malam Musa kuwa shi ne ya zama sarkin Zazzau na farko bayan jihadi. Kuma ya yi mulki ne a gidansa da ke Unguwar kwarbai, bayan fadar Zazzau ba tare da ya shiga gidan sarautar Bakwa ba saboda tsoron kada ya sauka daga tafarkin Sunna zuwa aikata abin da sarakunan Habe suke aikatawa.

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin