✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda jita-jita ta jawo asarar rayuka da dukiya a Kaduna

Jita-jita tana daya daga cikin manyan dalilin da suka jawo rikicin da ya faru a ranar Lahadi a cikin kwaryar garin Kaduna da wasu sassan…

Jita-jita tana daya daga cikin manyan dalilin da suka jawo rikicin da ya faru a ranar Lahadi a cikin kwaryar garin Kaduna da wasu sassan wajen birnin wanda hakan ya yi sanadiyar rasuwar mutane tare da jawo hasarar dukiya mai yawa.

ýAkalla mutum 22 ne suka rasu a rikicin na ranar Lahadi, sannan 44 kuma suka samu raunuka inji Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasir E-Rufa’i.ý

Binciken Aminiya ya gano cewa sakamakon rikicin da aka yi a ranar Alhamis din makon jiya a garin Kasuwar Magani da ke Karamar Hukumar Kajuruý a tsakanin kabilar Adara da Hausawa an rika zaman dar-dar da fargaba a wasu sassan jihar.

Rikicin na Kasuwar Magani wanda aka yi shi a lokacin da masuwar mako-mako na garin ke ci ya yi sanadiyar rasuwar mutum 55 a cewar Rundunar ’Yan sandan Jihar.

Babu wanda zai iya bayyana ainihin gaskiyar abin da ya jawo rikicin na Kasuwar Magani, sai dai majiyoyin Aminiya sun ce akwai ruwayoyi aban-daban masu sabani da juna kan dalilin tashin rikicin, inda wadansu suka ce rikicin ya faro sakamakon sabanin da aka samu a tsakanin wadansu matasa ’yan kabilar Adara da wani mai tura baro Bahaushe a cikin kasuwar.

Wadansu kuma sun ce rikici ne ya faru lokacin da aka koro wani barawo dan kabilar Adara zuwa cikin kasuwar, inda ’yan uwansa suka hana a ýtaba shi.

Wadansu kuma sun ce rikicin ya faro a tsakanin wadansu matasa a wani gidan shan giya da ke kusa da kasuwar har ta kai sun fara fada a tsakaninsu daga nan kuma abin ya bazu zuwa cikin kasuwa.

Bayan an kafa dokar hana fita a garin Kasuwar Magani sai kuma a ranar Lahadi ’yan kasuwa da suka je cin kasuwar mako a garin Kujama da ke Karamar Hukumar Chikun suka tsinci kansu a cikin ýrudani.

Wani ganau da ya nemi a sakaya sunansa ya shaida wa Aminiya cewa suna cikin cin kasuwa sai kawai suka ga jama’a suna gudu suna kwashe dukiyansu. Duk wanda aka tambaya sai ya ce wai an fara fada a Kasuwar Magani.ý

Akwai kuma wata majiya da ta ce kudajen zuma ne suka shigo cikin kasuwar Kujama sai mutane suka soma guje-gujen neman tsira inda hakan ya sa wadanda ba su sani me ke faruwa ba suka fara kwashe kayansu domin tsira da rayukansu, bisa tsoron ko rikici ne ya taso.

Wannan rudani ne kuma ya bazu zuwa cikin kwaryar garin Kaduna ta bangaren unguwanin Sabon Tasha da Marabar Rido, inda cikin ’yan mintuna garin ya rude da guje-guje kowa sai fadin abin da bai sani ba yake yi.

Malam Rilwanu Maigwanjo daya daga cikin ’yan kasuwar da ke Kujama a ranar da abin ya faru ya shaida wa Aminiya yadda suka sha. “Gaskiyar abin da ya faru shi ne a wannan rana da misalin karfe hudu muna cikin kasuwar Kujama sai kawai muga hango ’yan sintiri na JTF da ke a kasuwar suna bin wani matashi da gudu. Dama kuma su yan sintirin tun safe suke cikin kasuwar suna yawo domin kwantar wa jama’a hankali saboda abin da ya faru a Kasuwar Magani a ranar Alhamis,” inji shi.

Ya kara da cewa: “Matashin da suka bi a guje dama suna nemansa ne, saboda daya ne daga cikin matasa ko abokan wani da ake nema a Kasuwar Magani da ake kira Zidane. Ganin ’yan JTF suna bin sa da gudu sai mutane suka fara gudu suna cewa an fara fada an fara fada. Kafin ka ce kwabo sai muka samu labarin Marabar Rido ta dauka har da Sabon Tasha.”

“Su kuma ’yan JTF din sun dawo daga baya suna ta ce wa mutane ba fada ake yi ba, amma ina wadansu mutane sun riga sun gudu. A gabanmu suka mika matashin ga sojojin da suka zo wajen har yake fadin cewa su bakwai aka turo kasuwar domin su tayar da fitina,” inji shi.

Rilwanu ya ce koda yake babu wanda aka kashe a Kujama a wancan rana amma motoci sun kai dari da suka kwana a Unguwar Hausawa da ke garin har zuwa wayewar garin Litinin.

“Babu wanda aka kashe a Kujama a ranar kuma a nan muka kwana tare da sauran jama’a. Sai dai akwai wani abokin kasuwancina mai suna Abdullahi da muke tare da shi ranar muna jiran mota, kafin in koma daga karbo wayata a wurin masu caji sai ya samu babur ya yiwo gaba, aka kashe shi a Marabar Rido,” inji shi.

Rilwanu ya musanta zancen da ake yadawa cewa kudan zuma ne suka tarwatsa kasuwar. “A’a babu wani kudan zuma wannan zance ne kawai na mutane. ’Yan JTF da kansu sun tabbatar mana cewa ba fada ake yi ba don haka babu wani kudan zuma kuma,” inji shi.

Wani mazaunin Sabon Tasha kuma daya daga cikin ’yan gidan sarautar Kajuru da bai so a ambace sunansa ya tabbatar wa Aminiya cewa hakika wani matashi aka biyo domin a kama shi.

Kuma matashin da aka biyo ya tsere ne daga gidan yari bayan an kai su noma a kusa da kasuwar Kujama.

“Da aka biyo shi a guje sai ya shiga cikin kasuwar, to, ganin ana biye da shi a guje sai mutane suka fara gudu kasancewar dama can akwai tsoro a zukatan jama’a saboda rikicin Kasuwar Magani da aka yi kwanaki,” inji shi.

A cewarsa, babu wani zancen kudan zuma domin mutum ne ya fita ya gudu mutane kuma suka bi shi da nufin kamo shi.

“Ka san kuma akwai zancen Kasuwar Magani kuma sai ga shi mutane sun ga ana bin wani da gudu ba tare da an tsaya bincike ba. Wannan bayani da nake fada maka daga bakin daya daga cikin masu sarautar Kujama na same shi. Ka san akwai zaman dar-dar a gari daga nan kuma da labari ya isa gari sai ko’ina ya rude, har ta kai ga abin da ya faru. Mutane babu wanda ya san abin da ya faru sun dai ga ana gudu kawai kowa sai ya kama gudu. Ga shi yanzu an zo an hana jama’a fita neman abincinsu. Duk wannan abin jita-jita ce kawai ta jawo shi,” inji shi.

Game da ko sace Agom Adara, Mista Maiwada Madaki na da alaka da rikicin, sai ya ce a’a domin shi an sace shi ne a ranar Juma’a a kan hanyarsa ta komawa Kachiya. “A iya sanina sace ba ya da alaka da rikicin Kasuwar Magani ko na Kujama, ina ganin mutanen sun yi amfani ne da cewa tunda akwai dokar hana fita a Kajuru babu jami’an tsaro a kan titi saboda haka bari su fito su yi sata inda kuma shi tsautsayi ya haushi suka kama shi. Domin Kafin su tare motar Agom Adara sun tare motoci biyu inda suka kashe mutane a ciki. ýKuma shi yana kan hanyarsa ce ta komawa Kachiya abin ya faru da shi,” inji shi.

Sa Gbagyi Mista Danjuma Barde kira ya yi ga jama’ar masarautarsa su guji yada jita-jita ko wani labari da ba su da tabbacinsa.

A cewarsa, babu wata al’umma da za ta ci gaba ba tare da zaman lafiya ba.

“Allah ne Ya halacce mu kabila daban-daban don haka dole mu zauna tare domin a samu ci gaba. Yada jita-jita babu kyau,” inji shi.

Basaraken ya bayyana haka ne lokacin da ya yi jawabi kai-tsaye a Gidan Radiyon Jihar Kaduna (KSMC) domin kwantar wa jama’a hankali.

Shugabar Karamar Hukumar Chikun inda rikicin ya faru Ladi Yahuza ta ce hankali ya kwanta a garin Kujama bayan samun wannan rudani. Ta bukaci jama’a su guji yada jita-jita musamman labaran da ka iya ta da hankalin jama’a.

Baya ga matakin kafa dokar hana fita ta awa 24 wadda aka sassauta shekaranjiya Laraba zuwa karfe 6 na safe zuwa 5 na yamma Gwamnan Jihar Malam Nasir El-Rufa’i wanda ya ziyarci wadanda aka raunata a asibitoci ya umarci jama’a su daina yada jita-jita.

Sannan ya shawarci jama’a su natsu su kwantar da hankalinsu tare da zama da juna lafiya ba tare da nuna bambancin addini ko kabila ba.

Gwamnan ya kuma sha alwashin hukunta duk wadanda aka samu da hannu wajen tayar da rikicin.

Bishop din Cocin Katolika na Kaduna, Rabaran Mathew Ndagoso, ya yi tir da tashin hankalin inda ya bukaci al’ummar Jihar Kaduna su guji yada jita-jita tare da ruruta wutar rikici.

Kamfanin Dillacin Labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito Bishop Ndagoso yana fadi a wata sanarwa cewa jita-jita tana kashe mutane fiye da yadda bindiga ke kashewa inda ya ce, “A matsayinmu na kasa daya wajibi ne mu nemo hanyoyin fahimtar juna da gina kyawawan alaka na gaskiya. Na damu da kuncin da aka jefa Kirista da Musulmi ta wajen kashe musu dangi.”

Ya koka kan yadda ake ci gaba da samun tashin hankali a dogon lokaci, inda ya bukaci a kawo karshen haka, kuma ya yaba wa gwamnatin jihar da hjukumomin tsaro kan gaggawar dakile rikicin.

Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Musulunci ta Najeriya (NSCIA) ta yi tir da kashe-kashen rayuka da lalata dukiyoyi da aka yi a Kaduna, inda ta jajanta  tare da ta’aziyya ga iyalan wadanda aka raunata ko suka rasa dangi ko aka lalata wa dukiya.

Majalisar ta kuma yaba wa Sufeto Janar na ’Yan sandan Najeriya kan hanzarta tura kwamitin bincike na musamman don dawo da zaman lafiya a yankunan da ake rikicin, kuma ta yaba wa gwamnatin jihar kan gaggauta sanya dokar hana fita don magance rikicin.