✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda kashe dan banga ya haifar da rudani a Kafanchan

Hankalin mutane a garin Kafanchan ya tashi yayin da suka samu labarin kashe wani dan bangai mai suna Sani Sale Maikanti da ke aikin gadi…

Hankalin mutane a garin Kafanchan ya tashi yayin da suka samu labarin kashe wani dan bangai mai suna Sani Sale Maikanti da ke aikin gadi a Babban Asibitin da ke garin Kafanchan, hedkwatar Karamar Hukumar Jama’a ta Jihar Kaduna a makon jiya.

Lamarin ya faru ne da misalin karfe 8 zuwa tara kuma babu wani takamaiman dalilin faruwarsa da kuma ko su wane ne suka aikata haka har zuwa lokacin hada wannan rahoton.

Yayin da wasu ke ganin ’yan bindiga sun biyo bayan wasu mutane biyu ne da sojoji suka dauko daga wani kauye da ya hada da wani bafulatani da aka sassara da kuma wanda ya yi saran bayan jama’a sun damke shi tare da yi masa duka, wasu kuma na zargin jami’an ’yan sanda wasu kuma ke ganin barayi ne.

Da ya ke yi wa Aminiya karin haske, Mataimakin Shugaban ’yan bijilenti na Karamar Hukumar Jama’a, Yahaya Usman Rahama ya yi watsi da jita-jitar da ake yadawa cewa wani jami’in dan sanda da suke aiki tare ne ya harbe shi.

Ya ce lamarin kamar yadda binciken da su ka faro ya gwada, marigayin ya zo ke nan ya gama kewaya asibitin bayan karbar aikin dare da ya yi yana dawowa zuwa babban kofar asibitin sai wasu mutane biyu da wasu suka shaida sun gansu suka biyo bayanshi inda aka ce da ya fahimci haka sai ya kara sauri inda nan take suka bude masa wuta suka harbe shi a ka har kwakwalwarsa ta fito.

“Babu wanda ya san hakikanin abin da ya faru ko kuma su wane ne, illa iyaka abin da bincikenmu da na sauran jami’an tsaro na farin kaya da na ’yan sanda zai nuna.”

Ya ce akwai wadanda suka shaida musu sun ga fitan wasu mutane biyu a guje ta kofar baya a kan babur bayan faruwar lamarin.

Shi kuwa wani da ya bukaci a sakaye sunansa wanda yana daya daga cikin wadanda suka fara isa kan gawar ya shaida wa Aminiya cewa suna zaune a majalisarsu da ke layin Ibadan kawai sai suka ji karar bindiga ta wajajen asibitin inda suka garzaya don ganin ko me ke faruwa inda suka tarar babu kowa sai wani jami’in ‘yan sanda a jikin bango dauke da bindiga.

Lokacin da wakilin Aminiya ya isa wurin ya ga gawar mamacin kwance cikin jini ga kuma kwanson harsashin da aka yi harbi guda shida a gefe kafin isowar sojoji cikin mota inda nan da nan wani daga cikinsu ya fara harbi da bindiga don tarwatsa gungun fusatattun matasan da suka cika kofar asibitin don sanin hakikanin abin da ya faru.

Da yake amsa tambayar Aminiya a ofishinsa, Babban Daraktan Asibitin, Dokta Samuel Kure ya ce bayan an kira shi a waya kan wani bafulatani da aka kawo shi daga Afana-Unguwan Rimi da ke Karamar Hukumar Zango Kataf da sojoji suka dauko bayan an sassare shi tare da nasarar cafke wanda ya yi yunkurin kashe shi yana zuwa asibitin sai ya tarar da mutane sun yi cincirindo a bakin inda aka shaida masa cewa an kashe daya daga cikin masu yi musu aikin tsaro ne a asibitin.

“Wannan shi ne kawai abin da na sani. Sai dai ina yin kira ga jama’a da su kawar da hankalinsu da amfani da jita-jita.” Inji shi

Jim kadan bayan kammala jana’izar mamacin, daya daga cikin manyan malamai masu wa’azin addinin musulunci a garin Kafanchan Sheikh Aminu Kassim ya jawo hankalin matasa tare da basu hakuri kan wannan aika-aika da ya shafi dayansu.

Mamacin, dan kimanin shekara 43 da ke zaune a cikin garin Kafanchan yana sana’ar tuka Keke Napep ne da rana yayin da a matsayinsa na dan bijilenti kuma yake zuwa aikin gadi a bakin kofar shiga asibitin tare da jami’an ’yan sanda.

Aminiya ta tuntubi Kakakin Rudunar ‘Yan Sandan Jihar Kaduna DSP Yakubu Sabo ta hanyar tura masa sakon waya, amma bai amsa ba har zuwa lokacin hada labarin.