Search
Subscribe
Yadda kasuwar albasa ta fadi warwas a Katsina

Albasa a cikin kasuwa

Yadda kasuwar albasa ta fadi warwas a Katsina

Rashin dabarar da za a adana albasa, ya sa take karyewa sannan kasuwannin gwari su kuma na lokaci guda ne kawai.

Tun cikin makon farko na watan Agustan bana, albasa ta cika kasuwannin Jihar Katsina inda manoma ke shigowa da ita domin sayarwa kuma hakan ya jawo karyewar albasar a kasuwanin jihar.

Manoman sun ce, domin su kauce wa rashin kudi a hannunsu a tsakiyar damina ya sa suke shuka kayan gona irin su albasa wadda take kawo su kasuwa kafin lokacin girbin hatsi ya zo.

Wani manomin albasa mai suna Shehu Sani Mairuwa ya ce, daga watan Yuni zuwa Oktoba sukan noma kayan gona; irin su tumatir da albasa da sauransu, domin samun kudin da za su biya bukatunsu da su kafin zuwan hatsi.

“Duk irin karyewar da albasa za ta yi  ba za mu daina noma ta a cikin damina ba, saboda tana rufa mana asiri a lokacin da muka zuba kudinmu wajen noman hatsi da sauransu, kuma sai mun jira lokaci mai tsawo domin girbi. Su kuwa wadannan nan da nan za mu kawo su kasuwa domin mu samu abin biyan bukatu,” inji Mairuwa.

Ya ci gaba da cewa, a bana taki ya yi tsada sosai inda farashinsa ya kai Naira 7,500 zuwa 8,500 sabanin bara da aka sayar da shi a kan Naira  5,800 zuwa Naira 6,000.

Ya danganta koma bayan da ake samu a noman kayan gwari kan Gwamnatin Tarayya domin ba ta samar da na’urar zamani wacce za rika adana kayan gwari ba, inda ya ce gwamnati ta maida hankali a kan noman shinkafa, ta manta da noman kayan lambu irin su albasa, wanda shi ma noma ne da zai samar da kudin shiga masu yawa ga kasa.

“Albasa abincin kowa ne babu wata al’umma a duniya da ba ta amfani da albasa. Haka ana amfani da ita wajen  sarrafa magani. Yadda gwamnati ta kyale masu noman albasa hakan bai kamata ba. Ya kamata Gwamnati ta shigo cikin noman albasa ta ba ta kula ta musamman wajen samarwa da nomanta  da kayayyakin ajiye ta domin gudun lalacewa,” inji Mairuwa.

Aminiya ta gano cewa manoman albasa a Jihar Katsina sun dogara ne a kan ’yan kasuwar da suke zuwa daga Kudancin kasar nan sai makwabtan jihohi kamar Swakkato da Kebbi da kuma Jamhuriyyar Nijar.

A makon jiya ana sayar da kilo 100  na buhun albasa  a kan Naira 1,800 zuwa  3,500 ya danganta da irin ingancinta.

Wani manomi mai suna Bello Salisu Danja ya ce manoma a jihar suna bukatar kafa wata kungiya mai karfi kamar yadda takwarorinsu  manoman shinkafa da auduga suka yi. Domin su sama wa kansu mafita a bangaren da ya shafi girbi da kuma kasuwancinta.

“Idan har ana so noman albasa ya kai mataki na gaba, dole sai an kafa kungiya mai karfi ta masu noman albasa kamar takwarorinsu na shinkafa da auduga. Babbar matsalarmu ita ce ta rashin jajircewa da kuma fasahar zamani ta ajiyar kayan gona. Da yawa daga cikinmu sun dogara ne a kan noman gargajiya wanda hakan ba ya haifar da da mai ido ga manoman,” inji Danja.

Ya kara da cewa noman albasa ya fi samar da riba lokacin rani idan aka kwatanta da lokacin damina, saboda a lokacin rani tana daukar lokaci mai tsawo ba tare da ta lalace ba saboda bushewar yanayi.

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin