✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda lalata da mata ta addabi Jami’ar Ahmadu Bello

   Malami mai cutar kanjamau ya yi wa daliba fyade    An kama tare da korar malaman da ke da hannu Duk da irin matakan…

  •    Malami mai cutar kanjamau ya yi wa daliba fyade
  •    An kama tare da korar malaman da ke da hannu

Duk da irin matakan da mahukunta ke dauka kan masu takura wa dalibai wajen lalata da su kafin su ci jarrabawa, har yanzu al’amarin bai sauya ba a Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, inda galibin dalibai ke fama da hantara da neman yin lalata daga wadansu malamansu. Aminiya ta yi nazari game da batun, ga kuma ta gano:

Asabe, (ba sunanta na aihini ba) ta kasance cikin zumudin samun gurbin karatu a mashahuriyar jami’ar nan wato Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, sai dai ba ta taba yin tunanin za ta tsinci kanta cikin halin dimuwa a yayin bidar ilimin da take yi a jami’ar ba.

Abin kaico gare ta, mutumin da nauyin koyar da ita tare da tarbiyyantar da ita ya rataya a wuyansa ya yi amfani da karfin tuwo wajen lalata da ita a cikin ofishinsa.

Wata majiya a jami’ar ta tsegunta wa Aminiya cewa lamarin ya faru ne a Tsangayar Ilimi ta Jami’ar. “Da farko dai sashin tsaron jami’ar ne ya kula da korafin, gabanin ’yan sanda su bi kadin lamarin. Kowa a cikinmu ya tsinci kansa cikin kaduwa, lokacin da aka gano malamin da ya tafka danyen aikin yana dauke da cututtukan kanjamau da na hanta,” inji wata majiya.

Dalibar, kamar yadda bincike ya gano, ’yar aji daya ce a jami’ar.

Majiyar tamu ta kara da cewa: “Duk lokacin da irin haka ta faru, mukan sanya a yi gwaje-gwaje ga wanda ya tafka ta’asar da  wacce abin ya rutsa da ita. Bayan gwajen-gwajen ne sai aka gano malamin yana dauke da cututtukan kanjamau da na hanta. Hakan ya kara zafafa batun; inda ’yan sanda suka dauki nauyin kula da lamarin. Ranmu ya yi matukar baci da irin wannan mugunta, a ce wai mutumin da yake sane cewa yana dauke da miyagun cututtuka irin wadannan amma ya buge da yi wa yarinyar da ba-ta-ji-ba-ta gani-ba fyade.”

A halin yanzu, al’amarin Asabe na hannun Runduar ’Yan sandan Jihar Kaduna tana kula da shi. Kamar yadda Aminiya ta gano, saboda kasancewar mahaifinta kusa ne a gwamnati, hakan ya sa ake kokarin ganin ba a yi wa batun nata rikon sakainar kashi ba.

Binciken Aminiya ya gano cewa da dama cikin malamai da daliban da aka kama dumu-dumu a irin wannan badakala ta lalata, an sallame su daga jami’ar, wadansu ma jami’ar kan gabatar da su gaban shari’a. Sai dai duk da haka wannan muguwar dabi’ar ta ki ta kau.

Wata badakalar baya-bayan nan, ita ce wadda ta shafi wani malami da ke Tsangayar Kimiyyar Zamantakewa. Malamin, kamar yadda bincike ya gano, ya yi ta kayar da wata dalibarsa a wani darasi da yake koyarwa ga ’yan aji uku. Majiyar sashen tsaro ta jami’ar ta ce, “Kiri-kiri, malamin ya fada wa dalibar cewa ba za ta taba tsallake wannan darasi ba; muddin ba ta bayar da kai bori ya hau ba. Da ta rasa na yi sai kawai ta gabatar da korafinta gaban sashen tsaron jami’ar. Mu kuma sai muka dana masa tarko, ta hanyar nuna wa dalibar ta nuna cewa ta amince da bukatarsa. Sai ya je ya kama daki a wani otel, inda muka kama shi a yayin da yake kokarin lalata da ita.

“Amma mun samu izina kwarai,  sa’ilin da aka kori wani Farfesa kan matsa wa dalibai mata da lalata, amma sai daga bisani Kotun Koli ta mayar da shi bakin aiki. To daga nan muke kokarin sai mun samu hujjojin nadar murya da na bidiyo. Jami’ar na kokari matuka wajen ganin duk wanda aka kama an hukunta shi yadda ya dace da laifinsa kan doron tsarin dokokin jami’ar da kuma na kasa. Hakan ne ya sa al’amarin yake raguwa matuka,” inji majiyar.

Sai dai bincike ya gano yadda har yanzu akwai dimbin kararrakin da ke da nasaba da batun lalata, wadanda jami’ar ke gudanar da bincike a kansu. Akwai wata kara a Tsangayar Koyar da Noma, inda ake zargin wani malamin da yi wa dalibarsa fyade. Wasu kararraki biyu kuma daga Tsangayar Kimiyyar Halayyar Zamantakewa, daya daga ciki ya shafi wani Farfesa. Sai kuma daya batun, inda a nan ma wata karar da ta shafi lalatar, inda ake zargin wani da kokarin yi wa dalibinsa (namiji) lalata.

Sai kuma wata karar a Tsangayar Ilimi, inda ake zargin wani Farfesa da neman lalata da wata matar aure, wacce dalibarsa ce a shekarun baya. Bayanai sun ce, Farfesan ya yi ta bibiyar matar da lalata, inda ta sanar da mijinta; sai kawai aka dana wa Farfesan tarko kuma ya fada, inda aka kama shi a wani otel a birnin Kano. An zarge shi da gayyatar matar zuwa daki a otel din da nufin ya yi lalata da ita.

Kodayake bayan ya karbi takardar sallamarsa daga bakin aiki da hukumomin jami’ar suka yi, Farfesan ya garzaya gaban kotu domin kalubalantar korar tasa. “Kotun Kolin ta bayar da umarnin lallai a mayar da shi bakin aikinsa. Sun gabatar wa kotun cewa, ai shi mai duba aikin dalibar ce, kuma ta je dakinsa a otel din da niyyar gabatar da babi na uku na kundin kammala karatunta, don neman sahalewarsa. Alal hakika kotun ta tabbatar da lallai shi mai duba aikin nata ne, daga shaidun da ta tattara a jami’ar. Ka san cewa, ita kotu a kullum tana aiki ne da shaidu ko hujjojin da ke gabanta. Don haka sai kawai ta wanke shi daga tuhumar. Hakan ne ya sanya, kamar yadda na fada a baya, sashen tsaron jami’ar ya sake bullo da wasu sababbin dabaru. Za mu yi amfani da shaidun da ko a kotu ce, wadannan miyagun ba za su sha ba,” inji majiyar.

Sai dai Babban Jami’in Sashen Tsaro na Jami’ar, Kanal Tukur Jibril (mai ritaya) ya ki cewa uffan game da batun, inda ya  ce, ‘Babu bukatar a yayata wadannan batutuwa; tunda dai jami’ar na daukar matakai game da korafe-korafen.’

Kodayake a nasa bangaren, Babban Jami’in Hulda da Jama’a na jami’ar, Dokta Sama’ila Shehu, ya ce a babban bigire irin na Jami’ar Ahamadu Bello, akwai yiyuwar a yi ta samun faruwar batutuwa irin na lalata da sauransu. Amma a cewarsa, muhimmin abin lura a nan shi ne, tunda dai mahukuntan da abin ya shafa suna kokarin daukar matakai na kandagarkin faruwar hakan; tare da hukunta wadanda aka kama da nufin taka birki ga muguwar dabi’ar, “Abin da zan fada a nan shi ne, ina kira ga iyaye su wayar da kan ’ya’yansu na kada su yi kasa a gwiwa wajen gabatar da rahoton duk wani yunkurin neman lalata da su. A wannan zamanin na fasahar zamani, akwai hanyoyi da dama da ’yan mata za su iya daukar hujjojin da za su nuna a matsayin shaidu. Da ire-iren wadannan shaidun, akwai sassan da nauyin duba wadannan korafe-korafen ya rataya a wuyansu. Bangaren tsaron jami’ar da kuma na sashen da ake kira SERBICOM, a shirye suke don karbar koke-koken daga dalibai da kuma sauran al’ummar jami’ar,” inji shi.

Dokta Shehu ya ci gaba da cewa, “A matsayinmu na iyaye, muna samun sanyin rai, lura da yadda mahukuntan jami’ar a kullum suke tsayin daka wajen daukar tsauraran hukunce-hukunce a kan wadanda aka samu da aika-aikar. Kuma tun da jami’ar na bakin kokarinta wajen tabbatar da ’ya’yanmu sun samu kyakkyawar kula da tsaron da suka dace, su ma iyaye kamata ya yi su taka muhimmiyar rawa wajen wayar da kan ’ya’yansu game da al’amarin.”