Da Dumi Dumi

Yadda likita mai nakuda ta karbi haihuwa

Wata Likita da ke aiki Jihar Kentucky ta Amurka ta dakatar nakudarta, don ceto rayuwar wata mai nakudar da ta shiga halin kaka-ni-ka-yi, kamar yadda kafar yada labarai ta NBC ta ruwaito.

Amanda Hess kwararriya kan harkar mata masu juna biyu da ta fito daga Frankfort, ta shiga Cibiyar kula da lafiya ta Frankfort, inda aka dura mata ruwan nakuda don ta haihu, sai ta ji daya daga cikin matan da take kula da su a asibitin, wato Leah Halliday Johnson na ihu jaririnta na neman fadowa. Ganin cewa ta saba duba lafiyar matar sai ta sauko daga gadonta na haihuwa ta nufi inda matar take.

Malaman jinya suka tabbatar wa Hess da cewa jaririn Halliday Johnson na fitowa da sauri kuma cibiyarsa ta daure masa wuya, kamar yadda kafar sadarwar People.com ta ruwaito ranar Lahadin makon jiya. Likitan da aka kirawo don duba marasa lafiya tuni ya fice daga asibitin zuwa wajen karya kumallo, don haka ake neman taimakon  gaggawa.

Sai Hess ta fito cikin  sauri. “Nan take na sanya rigar aiki, na daura takalman  boot a kan takalman a, don kada ruwa ya fallatso mini, sai na shiga dakinta,” a cewar Hess kamar yadda ta bayyana wa jaridar mako ta WKYT.

ADVERTISEMENT

Dan malamn jinyar  asibitin sun shawarci mai nakudar ta dan yi hakuri kadan, amma zafin ciwo ya yi mata tsanani, kamar  yadda ta bayyana wa kafar sadarwar People-com a Lahadin da ta gabata.

Lokacin da Hess ta shiga wajenta, Halliday Johnson ba ta san cewa likitar na shirin shiga dakin nakuda ba.

“Tamkar likita ce da t ayi shirin aiki,” a cewar Halliday Johnson a hirarta da NB C. “Mijina ya fahimci cewa akwai wani abu tare da ita duk da cewa tana sanye da rigar aikin likita, amma ni ban fahimta ba saboda ina kwance ina nakuda. Na kasance a cikin wata duniyar, “ injita,

Halliday ta haifi ’yarta mace, kamar yadda NBC suka bayar da labari.

Bayan da likitan da aka kira ya zo ya karbi aikin sai Hess ta koma dakin nakuda. A cikin wannan daren dai ita ma ta haifi jaririya mace.

 

Share
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya