✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda mabarata 18 suka bace a Legas shekara 5 ba labarinsu

Mun yi iya  kokarin nemansu har mun hakura – Iyalansu Malam Abubakar Ibrahim shi ne Sarkin Guragun Alagbado da ke Jihar Ogun, a zantawarsa da…

  • Mun yi iya  kokarin nemansu har mun hakura – Iyalansu

Malam Abubakar Ibrahim shi ne Sarkin Guragun Alagbado da ke Jihar Ogun, a zantawarsa da Aminiya ya bayyana yadda mutanensu mabarata 18  suka bace a lokacin wani shiri da gwamnatin Legas ta kaddamar na kama mabarata a jihar. Ya ce tun lokacin da aka kama mabaratan 18, kusan shekara biyar har yanzu babu labarinsu:

 

Za mu so ga gabatar da kanka?

Sarkin Guragun: Sunana Abubakar Ibrahim, ni ne Sarkin Guragun garin Albgbado da ke Jihar Ogun a kan iyakar Jihar Ogun da Legas, na shafe sama da shekara 45 a Legas sannan na shafe kusan shekara 25 ina jagorantar guragun wannan yanki a matsayin sarkinsu. Garin Alagbado gari ne matattarar nakasassu musamman guragu, sannan mafi yawan nakasassun da ke zaune a Legas suke tsallakawa bara in yamma ta yi su dawo gida

Me ya sa garin Alagbado ya zama matattara gare ku?

Sarkin Guragun: Eh, a baya can ko kuma in ce har yanzu ma gidajen haya sun fi sauki a nan idan ka kwatanta su da Jihar Legas. To kasancewar gari ne da ke kusa da Legas sai mutanenmu suke yin masauki a nan, saboda a baya can marigayi Cif Ganiyu Fawehenmi shahararren lauyan nan mai kare hakkin dan Adam shi ke biya mana kudin hayar gidajenmu. Sannan a wancan lokaci idan gwamnati ta kama mutanenmu shi muke kai wa kukanmu ya share mana hawaye ya ba mu lauyoyi su tsaya mana har gwamnati ta sake su. Amma yanzu mun shiga wani hali bayan da ya rasu, saboda babu wanda yake mana irin wannan taimako, domin yau sama da shekara biyar ke nan lokacin mulkin tsohon Gwamnan Jihar Legas Babatunde Fashola aka yi wani kame, inda muka rasa mutum 18 kuma har yanzu babu labarinsu.

A nemi Jaridar AMINIYA don samun cikakken rahoton.