✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda manyan Najeriya suka halarci bikin ‘yar Sarkin Musulmi a Sakkwato

A yau birnin Sakkwato ya dauki manyan baki daga ciki da wajen kasar nan domin halartar shaidar auren ‘yar Mai Alfarma Sarkin musulmi, Muhammad Sa’ad…

A yau birnin Sakkwato ya dauki manyan baki daga ciki da wajen kasar nan domin halartar shaidar auren ‘yar Mai Alfarma Sarkin musulmi, Muhammad Sa’ad Abubakar III da Alhaji Mahmud Isa Yuguda dan tsohon Gwamnan Bauchi. An dai Daura auren kan sadaki Naira dubu 50 kacal.

Cikin wadanda suka samu halartar shaidar auren, akwai manyan Sarakuna, malammai, ‘yan siyasa, ‘yan kasuwa, ma’aikatan Gwamnati da sauran mutanen gari.

Sarkin Bauchi ne Wakilin Ango, sarkin Gwandu Muhammad Bashar Waliyin Amarya

An daura auren ne da misalin karfe 12 a masallacin Juma’a na Sultan Bello da ke Sakkwato.