✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda muke fuskantar zaben Gwamnan Katsina  bana – Muntari Lawal   

Alhaji Muntari Lawal shi ne Daraktan Yakin Neman Zaben Gwamna Aminu Masari a karo na biyu. Aminiya ta tattauna da shi kan abubuwan da suka…

Alhaji Muntari Lawal shi ne Daraktan Yakin Neman Zaben Gwamna Aminu Masari a karo na biyu. Aminiya ta tattauna da shi kan abubuwan da suka shirya domin jan hankalin al’ummar jihar su sake zaben Gwamnan:

 

Kun bude yakin zabenku a garin Funtuwa da wane take kuka bude shi?

Taken da muka sanya shi ne,”Restoration Agenda 2”, wato Dawo da Martabar Jihar Karo na Biyu.  Saboda aikin da muka fara ba mu kammala ba, a kan haka muke so mu yi amfani da wannan lokaci domin mu karasa in Allah Ya ba mu dama a wannan zabe na bana. Kasan sha’anin gwamnati ba a zuwa daya ake kammalawa ba. Akwai shirye-shirye da yawa wadanda wasu an kammala wasu kuma ba a kammala ba, wasu ma ba a fara ba. To wannan dalili ne ya sa muka ce karo na biyu.

Wasu bangarori ne za ku fi mayar da hankali wajen jawo hankalin mutane a kamfe din?

Ko yanzu ma mun fifita ilimi fiye da komai don shi ne matakin farko da na biyu da na uku, sannan saura su biyo baya. Har yanzu burinmu bai cika ba game da harkar ilimi domin har yanzu da sauran aiki. In har Allah Ya sa jama’ar Katsina sun sake zabenmu, to za mu ci gaba a kan batun ilimi daga inda muka tsaya, sannan sai batun kiwon lafiya da sauransu.

Wane tsari kuka dauka na yakin neman zaben na bana?

To ka san wancan karon ba mu ke da gwamnati ba, muna adawa ne. To yanzu mu ke da gwamnati, ka ga za a samu sabani wajen yakin neman zabe. A wancan karon babu karamar hukumar da ba mu je ba, wata ma har sama da kwana daya. To yanzu ka ga sai ka yi aikin gwamnati sannan ka yi siyasa. To sai muka raba abin kashi uku. A yanzu haka muna cikin kashin farko, mun fara da shiyyar Funtuwa da sauran shiyyoyin Daura da Katsina. Ka ga mun gama da jihar baki daya ke nan.

Jama’a na ganin kamar ba ku da abin da za ku gaya masu na ci gaba da kuka kawo?

To me za mu fada wa jama’a? Ai jama’ar ke da bakin magana yanzu ba mu ba. Mu aiki ne aka zabe mu mu yi ga shi kuma mun yi domin kowa ya zo ya gani. Mutane ne za su ce, aiki ya yi ko bai yi ba. Mu alkawurra muka dauka kuma gwargwadon iko mun sauke, wasu ko muna hanyar saukewa ko muna cikin saukewa. Shin abin da muka yi ya yi daidai da abin da muka ce za mu yi musu ko an samu akasi? Masu jefa kuri’a ne za su yi mana wadannan tambayoyi. A kan haka ne ma ya sa muka fara bikin baje kolin ayyukan Gwamna Masari ga jama’ar da muka san ba su iya zuwa wajen taron kamfen balle a yi musu bayani a can. Mutane wadanda ko dai fadawansu ko na tare da su ne ke kawo masu labari. Shi ya sa muka gayyato su don su ji kuma su ga irin ayyukan da muka yi. Kuma mun tsara kowace ma’aikata su fito su yi bayani da kansu kafin mu je ga masu kuri’a. To wannan shi ne abin da jama’a za su yi magana, kuma ita wannan maganar za a yi ta ce a ranar zabe, wato ta nuna gamsuwa da abin da muka yi ko kuma akasi.

Yay batun kalubalen adawa kasancewar Katsina ce jihar Shugaban Kasa?

Ina wata adawa take a nan jihar? In ma har akwai wata adawa to ta suna ce a baki a tawa fahimtar, domin ba ta kai irin wadda muka yi a shekarar 2014 ba. In ka lura da abubuwa irin musgunawar da aka yi mana a 2014 mu yanzu babu abin da muke yi. Duk wani dan adawa mun kyale shi ya yi adawarsa. Mun bar su su yi amfani da kafafen watsa labarai na gwamnati da ke cikin jihar da na masu zaman kansu, su yi amfani da fastocinsu da duk wani abu nasu ba tare da musgunawa ba kamar yadda su suka yi mana. Amma a wancan lokacin hatta da shigowa Katsina mu kawo fom na dan takararmu sai da aka hana mu. Mun bude ofis a wajen tsohon bankin CBN Sule, ’yan bangar siyasa suka kai wa ofis din hari sannan aka sanya ’yan sanda suka rufe ofishin. A nan garin da aka haife mu amma in muka lika fosta ko allon talla, kafin safe an kware su. Wurin da za mu yi taro an hana, da mun yi magana a hada mu da jami’an tsaro. Hatta yawon kamfe da muke yi a nan kauyen Radda ni Muntari Lawal aka kama kuma a ranar Juma’a yadda babu wanda zai yi belina, kawai don ina jagorantar kamfe. Amma mu yanzu hana masu ma son su yi wani ba daidai ba muke yi. Abin da muka sa gaba a yanzu shi ne mu ga mun cika alkawurran da muka yi wa jama’a.

Ana ganin kun karya doka na bude yakin neman zaben saboda kuna da shari’a da wasu?

Wace shari’a? A kwai dokar da ta hana mu ne? Ai dokar ce ta ba mu damar mu yi domin sunanmu ke Hukumar Zabe kuma ita INEC ba ta ce ta hana mu ba. Saboda haka don me za mu ki yin abin da kowa ke yi? Kuma inda ba mu ke takara ba me zai kawo Shugaban Jam’iyya na Kasa ya zo ya ba mu tutar takara? Ke nan da saboda wata shari’a ce ai da ba zai zo ba. Sannan magana ta biyu ai ba suna kalubalantar zaben fid da dan takara ba ne, suna kalubalantar babban taro ne wato Conference. Kuma har zuwa yanzu da muke wannan magana babu wanda ya dauko wata takarda daga kotu ya shigo da ita Katsina ya ba APC ko ya ba Gwamna cewa ana kararsa a kotu.

Me taron Funtuwar ya nuna muku kan zabe mai zuwa?

Abin da na fahimta shi ne kyakyawar dangantakar da ke tsakanin Gwamnatin Masari da al’ummar Katsina da APC tare da sauran ’yan takarar dangantaka ce mai karfi. Kuma insha Allah in aka zo zabe za ka gani. Abin da muke so a wannan zaben mu samu kuri’a fiye da miliyan biyu sabanin 2015 inda muka samu miliyan daya da wani abu. Muna so mu ga cewa ko an samu matsala a wata jiha kan zaben Shugaban Kasa to ya zamo ratar kuri’unmu sun maye gurbin da aka samu, in ma har an samu. Mu dai a wajenmu ba mu da matsala da kowa saboda mun san Katsina jiha ce ta APC. Duk wani mai hauragiyar cewa shi dan PDP ne to ba shi da abin yi ne kuma zai gane haka in an zo zabe.

Ko kana da wani sako zuwa ga jama’a?

Sakona shi ne ina kira ga jama’a cewa duk inda za mu je yakin neman zabe a yi abin cikin natsuwa, a kauce wa duk wani abin da zai kawo tashin hankali. Za mu taho da sakonninmu mu karanta wa jama’ar Jihar Katsina inda muka sa gaba game da manufofinmu da kuma abin da muke so mu yi wa jama’a. Ba za mu fita don yin fada da kowa ba domin ba za mu bari a tafi da ko sanda ce ba balle wani makami. Sako na biyu shi ne mutane su dage su ga cewa abubuwan da muka yi na alheri sun yada su kuma sun shirya za su kare su. Har yanzu abin da wadansu suke gani shi ne a siyasar kasar nan in mutun ya zo da ’yan kudin shi zai iya sayen kuri’a, to mu kuma abin da kowane lokaci muke nunawa shi ne a kauce wa irin wannan tunani domin ba siyasa ba ce mai kyau kuma hakan ke sawa a zabi mutanen banza wadanda da zarar sun ci zabe sun tafi ba za a sake ganinsu ba sai in wani zaben ya zo. Mutane su zabi wadanda suke zaune a cikinsu wadanda suka san komai nasu kuma suke tare da su da wuya ko dadi. Wannan shi ne sakona ga al’ummar Jihar Katsina da kasa baki daya.