✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda mutumin da ya ceto jariri daga gobara ya mutu

Wani mutum mai suna Micheal Anthony, mai shekara 27, wanda a ranar 13 ga watan Agusta da misalin karfe 8.30 na dare ya fada cikin…

Mahaifiyar jaririn da aka kubutar, Misis Shiminenge Terfa tare da danta, Saanmoyol TerfaWani mutum mai suna Micheal Anthony, mai shekara 27, wanda a ranar 13 ga watan Agusta da misalin karfe 8.30 na dare ya fada cikin balbalin gobara ya ceto wani jariri dan wata 16, ya mutu a ranar Lahadin da ta gabata saboda kunar da ya samu a yayin ceton.  
A yayin da ya kunduma cikin wutar, Micheal ya yi nasarar ceton yaron, amma ya samu munanan kuna a sassa daban-daban na jikinsa, aka kai shi dakin musamman na asibitin koyarwa na Jami’ar Binuwai (BSUTH), inda aka yi ta ba shi magani har dai rai ya yi halinsa da misalin karfe 11.45 na dare a ranar Lahadin.
Abin kaddara, a ranar Lahadin ne dai da dare, kimanin lokacin da ya kusa cikawa, gidan talabijin na kasa (NTA) ya gabatar da wani nunin majinyacin a lokacin da yake wadansu dabaru na motsa jiki, alamar yana samun sauki dangane da kunar da ya samu.
An sami birbishin labarin cewa Shugaba Goodluck Jonathan ya bayar da Naira miliyan biyu don a tallafa wa jinyar da Michael yake yi a asibitin kuma an yi nufin a kai shi kasar waje don ya samu kular da ta fi ta cikin gida, amma aka fasa saboda likitocin da ke kula da shi sun bayar da tabbacin yana samun sauki, kamar dai ya yayansa Charles Anthony ya bayyana.
Shi Charles Anthony din ne kuma ya sanar da manema labarai, yana kuka, cewa marigayin ya rasu ne a yayin da ya yi korafin wani tsananin ciwon kirji.
Ya tabbatar da cewa lallai Michael ya fara samun sauki, kafin ya suma a wannan daren kuma duk kokarin da likitoci suka yi wajen ganin sun farfado da shi ya ci tura.  “Ya mutu ranar Lahadi da dare.  Na kasa fita da wannan juyayi mai tayar da hankali.  kanena ya sa rai matuka wajen komawa makaranta, kuma yana cike da burin zama wani mai fada a ji cikin al’umma,” inji shi.
Lokacin da yake kwance a gadon asibiti, Michael ya fada wa mutanensa cewa idan an sallame shi daga asibiti, zai mayar da hankali wajen samun shiga jami’a don ya tabbatar da mafarkinsa na zama injiniyan kayan lantarki.
Shugaban sashen hulda da jama’a na asibitin ta BSUTH, Cephas Hough, ya tabbatar da cewa ‘mala’ika’ Michael, kamar yadda mutane suka lakana masa, ya mutu a asibitin, bayan da kowa yana masa fatar warkewa ya ci gaba da harkokin rayuwarsa a duniya.
A yayin hada wannan rahoto dai, an ajiye gawarsa a dakin adana gawarwaki na asibitin, alhali mahaifansa suna cikin jimamin rashinsa kodayake masu ta’aziyya sai kwarara suke cikin gidansu, suna taya su alhinin rashin nasa.
Kafin mutuwarsa, Michael, a cikin wata ganawa da wakiliyarmu a kan gadonsa na asibiti, ya bayyana farin cikinsa dangane da gudanar da abin da ya aikata na taimakon mabukaci, wanda kuma ya dace da abin da Allah Yake so, kamar yadda faston ya rika yin wa’azi a kan haka.
Before his death, Michael in an interbiew with our correspondent on his sick bed had edpressed joy that his actions were premised on the word of God preached by his pastor.
Ya ce, “Na dawo daga wurin aiki ke nan a ranar da lamarin ya auku wajen karfe tara, yayin mahaifana da ’yan uwana suka rika jin kukan jariri.  Da farko mun yi tsammanin makwabciyarmu ce ke horon yaronta, amma da kukan ya wuce misali, sai muka dunguma da gudu muka fita daga cikin gida, inda muka yi arba da gobara a gidan makwabciyar tamu.  
 “A daidai lokacin kuwa falon gidan ya balbale da gobarar.  Ba wani abin da kowa zai iya yi, in dai ana son a ceto yaron da ke ciki, sai dai a yi kukan-kura  da kunar-bakin-wake, a yi ta-maza, a kunduma cikin balbalin gobarar.
“Na kasa biye wa tsoro, balle har in bari yaron ya kone ya mutu.  Saboda haka, sai na yi nufin taimakon jaririn na kunduma cikin falon na nemi dakin da yake ya nannado shi na jefa shi ta taga”. Inji shi.
Micheal, wanda yake koyon gyaran kayan lantarki, duk da ya kone matuka wajen ceton jaririn, ya kara da cewa, “Ina farin cikin cewa yunkurin da na yi ya yi nasara.  Ba ni da wani takaici kan abin da na aikata.  Duk yadda ya kaya, ko in mutu, ko in yi rai, fatar da nake yi dai in samu rabo a ranar lahira,” inji shi.
Kamar da kasa, inji mai ciwon ido, mahaifiyar jaririn, Misis Shiminenge Terfa, wadda ta kidime tun lokacin da lamarin ya auku, ta ce dole ta koma gidan iyayenta don kada ta aikata wa kanta wani karin kaico-kaico.
Yanzu na koma gidan iyayena a titin bandekiya, saboda gudun kada in jefa kaina cikin wani hali.  Ba na iya jure jin cewa Michael ya bayar da ransa don ceton yarona”. Inji ta.
Misis Terfa ta ce ta je wani shagon magani wajen karfe 8 ta bar ’ya’yanta hudu a cikin gida a lokacin da gobarar ta tashi.
 Ta bayyana cewa sauran yaran uku, nan da nan makwabta suka ceto su, shi kuma jaririn mai suna Saanmoyol Terfa, sai aka manta da shi cikin daki, wanda a lokacin duk ya kama da wutar. Tsananin karar kukansa ta ja hankalin makwabtan, wadanda kuma ba yadda suka iya, saboda daidai lokacin gobarar ta kara kamari, ta yadda ba wani da ya yi wani yunkurin ceto shi.
Ta ce sai Michael, wanda ta ce mutumin Jihar Inugu ne, wanda kuma ya kasa jure wa karajin yaron, ya fada cikin balbalin wutar ya cukuikuyo jaririn ya jeho shi waje.
Ta ce abin da tuzurun Ibo ya yi, a ganinta, Yesu Almasihu ne kadai zai iya yin irinsa, amma ba kowane mutum zai iya sayar da ransa don ceton ran wani mutum daban ba.
“Ina ganin ko mijina ba zai iya yin abin da Michael ya yi ba, abin a ce yana wurin wannan lamarin ya auku, balle ni kuma uwar yaron.  Kawai abin da zan yi, sai in sadakar, in sa ran cewa mai yiwuwa Allah Ya ba ni wani dan a madadinsa.  A gaskiya, ina cikin takaici da juyayi da kidima a kan wannan al’amari,” inji ta.
A yayin da yake tsokaci, maihaifin marigayin, Mista Anthony Anthony, mai shekara 61, kawai daga hannu ya yi sama yana mai godiya ga Allah, Wanda Yake rayarwa da matarwa ta yadda Yake so.  “Babu wani abin bakin cikin rashi, tunda dana ya yi kyakkyawan abin kirki kuma ya mutu a kan yin abin alheri.  Shi abokin kananan yara ne tun yana karami, kuma wannan shi ne ya tunkuda shi ya sayar da ransa don ceton jaririn”. Inji shi.
Ya ce yanayin lafiyar dansa ya fara sukurkucewa tun ranar Asabar da dare a yayin da ya kama ’yan tsugunguni, sai dai wanshekare ranar Lahadi da safe ya samu walwala har zuwa yamma a lokacin da ciwon kirjinsa ya yi tsanani.
Ya ce likitoci hudu da ke aiki a wannan daren da wata nas sun yi gumurzun farfado da Michael lokacin da aka sanya masa karin jini, amma dai rai ya yi halinsa.  “Na yaba wa kokarin da likitocin da kuma ita nas din suka nuna a daren.  Sun yi iyakar abin da za su iya don farfado da shi, amma dai Allah Ya fi son abinSa, shi ya sa Ya dauke shi”. Inji shi.
Haka nan wani makwabcinsu Ikechukwu Obeta, wanda ke cikin masu ta’aziyya a gidan nasu da ke gefen kwalejin baatia a tsallaken titin Abu King Shuluwa a Makurdi, ya ce lallai mutuwar Michael ta bar gurbin alhini a zukatan duk wanda ya fahimci yadda al’amarin ya faru.
“Ya mutu kan aikin alheri.  Mutuwa irin ta manyan mutune da suka wuce.  Za mu ci gaba da tuna irin wannan namijin kokari nasa.  Michael mutumin kirki ne, mai tawali’u, musamman saboda irin aikinsa da yake koyo na gyaran kayan lantarki, mukan sanya shi ya yi mana aiki”. Inji shi.
Wadansu da ke zuwa coci tare da shi, Judith Akujobi da Ifeoma Chike sun bayyana marigayin da mutumin kirki mai son zaman lafiya, wanda kuma yake gudanar da ayyukansa cikin gaskiya da rikon amana, ta yadda kowa ke sha’awarsa.
Mahaifiyarsa Misis Edith Anthony, wadda ita ce shugabar mata a cocin ‘The Lord Choosen’, ta ce ba za a manta da mutuwar danta da sauri ba, kuma madalla da Allah ta kowane hali.  “Tunda nufin Allah ne, ba na bakin ciki da wannan rashi”. Inji ta.
Shi kuwa kawun mamacin, Mista Eugene Eureka, har zuwa lokacin da wakiliyarmu ta zanta da shi, bai sankankance Michael, wanda shi ne na biyar cikin su bakwai da gidansu, maza biyar mata biyu, ya mutu ba.  “Har yanzu ban sakankance dan dan uwana ya mutu ba”, inji shi.
Babban wansu Moses Anthony shi ma ya bayyana mamacin da mai son yara, “Babu mamaki ganin yadda ya saida ransa don ceton jaririn.  Abin da Michael ya yi ya nuna kyakkyawan halin kirista. Ba wata alaka ta jini ko ma kabila tsakaninsa da wanda ya ceto, balle a ce. Saboda haka wannan ita ce dabi’ar da ta kamata kirista ya rika yi, wato ya rika son mutane ba tare da nuna bambancin addini ko kabila ba”. inji shi.
A asibitin, har ana ta shawarar gabatar da suna Michael don a ba shi lambar girmamawa a ranar 1 ga wata Oktoba, kuma wani mai magana a madadin iyalan ya ce wani kamfani a Legas ya yi nufin bayar da gudummawar Dala dubu 20 (kimanin Naira miliyan 3) don biyan kudin jinyarsa.