✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda na fara noman goro a Arewa – Shehu Musa

Masu iya magana sun ce da gwaji jirgin sama ya tashi. Hakan ya tabbata inda wani manomi a Katsina ya fara noman goro. Fitaccen manomin…

Masu iya magana sun ce da gwaji jirgin sama ya tashi. Hakan ya tabbata inda wani manomi a Katsina ya fara noman goro. Fitaccen manomin zamanin, Alhaji Shehu Musa, ya shuka itacen goro a gonarsa da ke Maulumfashi a Jihar Katsina kuma har ya fara dibar ’ya’yansa. Ta yaya ya samu wannan nasara? Ya bayyana komai dalla-dalla, kamar haka:

 

Mun ji ka sanar cewa ka noma goro a Malumfashi a Jihar Katsina kuma har ka fara dibar ’ya’yansa. Ko za ka yi bayani kan wannan al’amari, ganin cewa Arewa ba kamar Kudu ba ce, inda aka san ana noman goro?

Hakika na shuka goro a gidana da ke Malumfashi a Jihar Katsina da kowa ya sani Arewacin Najeriya ce. Kuma na shuka shi a gona, kuma goron ya nuna har na cire ’ya’yansa daga itatuwansu, na nuna hotunansu a shafina na Facebook.

Itatuwan goro biyu da suke a gidana, mahaifinmu marigayi Alhaji Musa Dankano (Sarkin Fulani), shi ya shuka mini su, kamar yadda ya shuka a gidajen ’yan uwana, Alhaji Bello Musa Dankano da Ambasada Abdula’aziz Musa Dankano. Shi kuma itacen goro da ke gonata, ni na nemi irinsa na shuka.

A matsayinka na kwararren manomin zamani, ta yaya ka bi ka samu nasarar noman goro a wannan yanki?

To, na farko dai samun irin bai da wahala, domin idan ka samu daushen goro ka sanya shi a cikin algarara, ya zama koyaushe yana cikin danshi, to za ka ga ya fara yin tsiro. Daga nan sai ka maida shi cikin ledar shuka, inda tsironsa zai ci gaba da girma. Idan ya yi kwari sai ka mai da shi kasa.

Shi itacen goro zai rayu wajen da yake da danshi kuma da rani sai a rika ba shi ruwa isasshe da takin gargajiya. Kuma yana bukatar ka shuka wani itace kusa da shi, wanda zai fi shi girma a gaba, domin shi itacen goro yana bukatar inuwa. Ko a Kurmi suna shuka shi a karkashin manyan itatuwan koko ne da sauran manyan itatuwansu masu ba da inuwa da rike danshin kasa, domin ta haka ne yake samun inuwa.

Wace riba manomi zai iya samu da noman goro fiye da kayan da aka saba nomawa a Arewa?

Wato su itatuwan da ake shukawa a nan Arewa sun fi saukin shukawa da raino. Saboda itatuwa da dabbobi sun fi saukin raino idan aka shuka su inda Allah Ya halicce su tun asali. Amma shi goro idan ka shuka shi a nan wajenmu Arewa, yana bukatar kulawa ta musamman. Amma tunda kasancewar yana da tsada kuma koyaushe ana cikin bukatarsa, nomansa zai zama da riba sosai. Kuma ka san itace, nomansa daban yake saboda yana daukar shekaru daga uku zuwa bakwai kafin a fara samun amfaninsa.

Baya ga goro, wane kayan gona ne za a iya nomawa a Arewa, wanda a can baya muka dauka sai a Kudu kawai za a iya noma shi?

Baya ga goro, akwai abubuwa masu yawa wadanda a da ana tsammani sai a Kudancin Najeriya za su iya yi. A ciki akwai kwakwa (fara) da kwakwar manja da itatuwan da ake yin katako da su, kamar maje, madaci da sauransu da dama.

Idan mutum na sha’awar fara noma goro a Arewa, wadanne matakai ko hanyoyi zai bi ya samu nasara?

Idan kana so ka fara noman goro a Arewa, ta yadda za ka yi nasara, kana bukatar filin gona wanda ya kai eka 20, kana bukatar jari mai kauri da ma’aikata wadanda suka san yadda ake rainon itatuwa. Haka kana bukatar ruwa, wanda za a ci gaba da yin ban-ruwa da rani kuma sai an hada da hakuri saboda zai iya daukar kusan shekara hudu zuwa biyar kafin ya fara ’ya’ya.

Ko akwai wani tallafi ko agaji da wata kungiya ko hukuma ta tanada ga masu bukatar fara irin wannan noma?

Akwai su a rubuce amma kamar sauran tallafin noma da ake ta yayatawa, suna da wahalar samu, idan ma ka samun ke nan.

Ta fannin kasuwa fa, wadanne hanyoyi manomi zai bi ya sayar da wadannan kayayyaki cikin sauki, idan ya noma?

Duk abin da za ka kai kasuwa ka tabbatar da kyawunsa kuma ka tabbatar da cewa jama’a na bukatarsa, kamar goro, koyaushe ana bukatarsa. Kuma ka sanya masa farashi mai sauki, har in dai ba za ka fadi ba, ma’ana ya zamana kana yin rangwame.

Ko akwai bukatar gwamnati ko manyan ’yan kasuwa su shigo cikin wannan harka?

Akwai bukatar gwannati da manyan ’yan kasuwa su shigo wannan harka. Gwannati za ta iya tallafawa saboda tsawon lokacin da noman itatuwa yake dauka kafin manomi ya fara samun wani abu daga gonar. Manyan ’yan kasuwa ko suna da babban jari, za su iya yin juriyar hakurin har amfanin ya fara.

Ko akwai kiran da za ka yi ga kananan manoma dangane da irin wadannan bakin kayan gona da ka fara samarwa a Arewa?

Kananan manoma ma za su iya yin wannan noma na goro saboda yanzu ana bukatar mutane su rika shuka itatuwa na gargajiya da baki saboda amfanin da ke kunshe da su.

Ina kira ga gwannatocinmu su rika kulawa sosai a kan mutane da ma’aikatun da aka dora wa hakkin tafiyar da al’amarin noma gaba daya saboda kururuwar da ake yi ta fi aikin da ke a kasa.