✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Yadda na haihu a hannun ’yan bindiga a cikin daji’

A farkon makon nan ne aka sako sauran mutum 15 da ke tsare a hannun ’yan bindigar da Gwamnan Jihar Katsina Alhaji Aminu Bello Masari…

A farkon makon nan ne aka sako sauran mutum 15 da ke tsare a hannun ’yan bindigar da Gwamnan Jihar Katsina Alhaji Aminu Bello Masari ya sasanta da su bayan sun kwashe kwana 44 a dazukan Dansadau da ke Jihar Zamfara da Rugau da ke Jihar Katsina da kuma Kuyanbana da ke Jihar Kaduna.

Daga cikinsu akwai mata 13 da yara biyu cikinsu har da wanda aka haifa kwana daya kafin sako su.

Shugaban riko na Karamar Hukumar Jibiya Alhaji Haruna Musa Mota ne ya karbo mutane kasancewar duk sun fito ne daga garin Mallamawa a Karamar Hukumar Jibiya.

Wadanda aka sakon sun bayyana yadda suka rayu cikin firgici da yunwa, inda ake sam musu abinci sau biyu a rana, babu wanka ballantana wanki. Sun ce baya ga tsoratarwa da barazanar kisa da ake yi musu a kullum, maharan sukan yin harbe-harbe a sama wasu lokutan ma kusa da su domin su kara firgita su.

Murja ita ce matar da aka dauka tana da tsohon ciki daga garin Mallamawa, wadda kuma ta haifi ’ya mace kwana daya kafin a sako su, “Mu 150 ne muke zaune a wuri daya acikin dajin, a hankali ana daukar wadansu har muka koma saura mu 13 sai yaro daya kafin in haihu. Dukkanmu mun fidda ran za mu fita daga wannan waje saboda irin abubuwan da muke gani, bayan barazanar za a kashe mu muddin danginmu ba su kawo kudin fansa ba. Abubuwa dai ga su nan. Allah cikin ikonSa Ya kawo min haihuwar cikin sauki. Na haihu tare da taimakon wadannan mata da muke tare da su. Na kuma haifi mace. Babu abin da zan ce sai godiya ga Allah, amma wahala dai an sha.”

Ita ma A’isha, daya daga cikin matan da aka ceto ta ce, har abada ba za ta manta da ceto su da Gwamna Masari ya yi ba.

A bayanin Gwamna Masari, kamar yadda Babban Daraktan Watsa Labaransa Alhaji Abdu Labaran ya ce, bayan karbar wadannan mutane, Gwamna Masari ya ce mutum 15 su ne mutane na karshe wadanda aka kawo rahotonsu a gwamnatance suna tsare, suna kuma cikin wadanda aka yi yarjejeniyar sakowa daga hannun ’yan bindigar. Ya kara da cewa, a yanzu duk wadanda aka kama daga jihar an sako su a wannan mataki na farko na yarjejeniyar. A mataki na gaba na tabbatar da dorewar zaman lafiyar kamar yadda aka tsara, za a mika wa gwamnati makamai da alburusan da ke hannun ’yan bindigar wanda hakan ne zai sa ita kuma gwamnati ta biyo da ayyukan da suka nema, wato gina musu makarantu da asibitoci da madatsar ruwa da gyara tare da fitar da burtulloli da sauransu.

Gwamnan ya ce dukkan wadannan matakai za a tattauna su a tsakanin su shugabannin jihohin Katsina da Zamfara da na Jihar Maradi da ke Nijar, inda ake sa ran haduwarsu a karshen makon nan a Jihar Katsina.