✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda nake hada sana’ar wanzanci da tukin mota – Aliyu Bektara

Aminiya ta tattaunawa da Sarkin Askan Maisandari wanda kuma sanannen direba ne a tashar mota ta Borno Edpress, Aliyu Isah Imam Bektara, ya yi bayanin…

Aminiya ta tattaunawa da Sarkin Askan Maisandari wanda kuma sanannen direba ne a tashar mota ta Borno Edpress, Aliyu Isah Imam Bektara, ya yi bayanin yadda yake hada sana’o’in biyu a lokaci guda:

Ko yaya sha’anin gudanar da safarar motoci yake a tashar Borno Edpress a halin yanzu?

Alhamdulillahi dama kafin a kai ga matakin sarautar Sarkin Aska,  ina wannan sana’a ta tukin mota kuma akwai mutane da dama da suke cin abinci a karkashina.  Sannan muna daukar fasinjoji daga wannan tasha zuwa wasu garuruwa irin su Bauchi da Jos da Kano da Kaduna da Abuja da sauransu da motocinmu irin su Sharon da Bectra da sauransu. Akwai direbobinmu na Sharon da Bectra kamar mutum 100, sannan ni kaina wadanda suke karkashina suke cin abinci za su kai mutum 50, ban da wadanda suke saye da sayarwa irin na karafuna da makamantansu.

Ka yi bayanin cewa kai ne Sarkin Askan Maisandari yaya kake hada  sana’ar wanzanci da sana’ar tukin mota?

Eh, to a gaskiya na gaji sana’ar wanzanci daga mahaifina ne da mahaifiyata. Tunda na taso ina da shekara bakwai na fara koyon sana’ar wanzanci. Yau ga shi shekaruna sun haura 40, kuma har na zama Sarkin Askan Maisandari. Sana’ar wanzanci sana’a ce ta taimaka wa al’umma ta kowace fuska domin idan ka dauka ta yin aski ko ta yin kaciya ko ta fuskar bayar da maganin gargajiya ne duk taimaka wa al’umma ne. Gadonta na yi kuma ina alfahari da ita. tunda idan aka dubi tarihi lokacin da Turawan mulkin mallaka suka shigo iyayenmu da kakanninmu da wannan sana’a ta wanzancin suka same su kuma tana taimaka wa al’umma ta fuskar aski da bayar da maganin gargajiya. Domin idan wani abu ya faru da mutum a wancan lokaci wanzami ake gaggawar nema kafin shi kuma ya mika ga likitan zamani. Kuma daga ciki sai aka samu wadanda iliminsu da kokarinsu sun kai ga har sun zama likitoci. Kuma a halin yanzu a cikinmu akwai masu kokarin yin karatun zamani suna hadawa da tsarin gargajiyar.Wadansu kuma suna nan sun rike sana’artasu ta gargajiya ba su bari ba wanda idan ka zo bangarorin da suka shafi cututtuka na jiki to babu ko shakka za ka samu waraka kuma koda likata ya duba zai ce a yi kokari a samu wanzami. To ashe ka ga a tsakanin likitoci da wanzamai akwai alaka. To amma a zamanance mutumin da ya je ya karanta ya kuma ga abu zahiri to ko shakka babu zai fi ka sanin halittar dan Adam, to amma duk da haka dai muna tafiya da su hannu-da- hannu. Don haka ina kira ga ’yan uwana wanzamai cewa duk wanda Allah Ya ba shi dama ya yi kokari ya nemi ilimin zamani don shi ma ya tafi da zamanin ta yadda zai fahimci mene ne aikin likitanci ya kuma kara samun damar  yadda zai ci gaba da taimaka wa al’umma, tunda cikin ayyukan wanzanci muna kokarin taimaka wa al’umma domin samun lafiyarsu da jin dadinsu. Ni da nake magana akalla na bai wa mutum  sama da 50 maganin ciwon daji (Kansa) kuma Allah Ya ba su lafiya sun warke.’

Shin askin baba da ya fito ya tsole muku ido a matsayinku na wanzamai?

A’a ko kadan bai tsole mana ido ba domin idan ka lura ai Allah Shi Yake da zamani, to kuma idan Ya ce ga zamani ya zo ai dole kai mutumin da ba komai ba ne ka bi zamanin. Kuma wani bai cin rabon wani, sannan mu a wurinmu ci gaba ne har ma wani lokacin sukan zo wajemu su nemi taimakon shawara ko magani mukan kuma taimaka musu. Saboda haka babu wani abin da ya tsole mana idanu  a kan wannan. Wani zai yi tunani ya ce maimakon kamar da ana zuwa wajenmu a yi aski ko kaciya yanzu abu ya canja, to mu a wurinmu bai canja ba, don duk abin da aka ga ya bullo mu ma muna tafiya tare da shi. Kuma akwai mutanen da har yanzu ba sa son wani ya yi musu aski sai na aska, sannan aksarin mutane suna zuwa wajenmu karbar magungunan gargajiya, saboda haka babu wani abin da ya tsole mana idanu.

 Mene ne kiranka ga gwamnati kan yadda za ta tallafa wa ire-ire-irenku?

Muna rokon gwamnati ta yi wa Allah ta duba lamuran direbobi da kuma wanzamai. Muna bukatar taimako ta kowace fuska domin muna da abin da za mu taimaka wa mutane amma ba za mu iya ba saboda karancin abin hannu ko kuma kayayyakin aiki. Gwamnati ta agaza mana ta saka mana hannu mu iya mikewa.