Da Dumi Dumi

Yadda shugaban kasar Nijar ya yi hawan sallar idi

Kasar Nijar na daya daga cikin kasashen Afirka da suka gabatar da sallar Idi karama a ranar Asabar, 23 ga watan Mayu bayan mahukuntan kasar sun sanar da ganin jinjirin watan Shawwal a ranar Juma’a.

Shugaban kasar Issoufou Muhammadou ya yi hawan Idi tare da mukarabbansa da tarin jama’ar kasar a babban masallacin kasar da ke Birnin Niamey, Babban Birnin kasar Nijar.

Sharing
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya