✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda taron masu ruwa-da-tsaki a kan samar da abinci ya gudana a Maiduguri

A makon jiya ne tsohon Shugaban kasa, Cif Olusegun Obasanjo ya jagoranci wani taron masu ruwa-da- tsaki game da harkar samar da abinci da nufin…

A makon jiya ne tsohon Shugaban kasa, Cif Olusegun Obasanjo ya jagoranci wani taron masu ruwa-da- tsaki game da harkar samar da abinci da nufin yaki da yunwa a kasar nan, inda aka fitar da takardar bayan taron da take kiran a kara kaimi wajen inganta harkar noma da samar da abinci daga nan zuwa shekara ta 2025.

Takardar bayan taron ta bukaci gwamnatocin jihohi su kara zage damtse wajen inganta harkar noma a jihohinsu musamman wajen tallafa wa kananan manoma ta fuskar ba su takin zamani a kan lokaci da kuma inganta noman rani a dukanin jihohin Najeriya, ta yadda abinci zai bunkasa a tsakanin al’umma. Sannan wajibi ne manoma su mayar da hankali wajen noma kayayyakin abinci da nufin yaki da yunwa da ta addabi al’ummar yankin Arewa maso Gaba wanda yakin Boko Haram ya daidaita.

Har ila yau takardar ta yi nuni kan muhimmancin adana abinci  ta yadda za a iya cin moriyarsa a gaba tare da tallata kayayyakin da manoman suka noma ga al’ummar duniya don su rika cin ribarsu. Takardar ta kara da cewa wajibi ne manoma su hada karfi da karfe wajen samar da ingantattun iri kuma kada su raina abin da suke nomawa. Sai takardar ta yi kira ga gwamnatocin jihohi da na tarayya su agaza wa manoma ta kowace fuska domin bunkasa kasa da abinci.

Haka kuma taron ya yaba da kokarin gwamnatocin Najeriya ta hannun Babban Bankin Najeriya wajen bullo da shirin bai wa manoma bashi ta yadda za su bunkasa sana’ar tasu. Sannan ya nanata bukatar da ke akwai ta ganin cewar manoman rogo sun bunkasa harkar noman rogon ta yadda zai yawaita a kasa domin sarrafa shi ta kowace fuska, ganin cewa noman rogon zai taimaka matuka wajen samar da abinci da kuma samar wa matasa aikin yi.