✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda wasu mata 3 ke kasa ’yan uku a gefen hanya da sunan bara

Gadar tsallake titi da ke garin Deidei a Birnin Tarayya Abuja, ta zama mafakar mabarata da suka hada da tsoffafi da zawarawa da ke rike…

Gadar tsallake titi da ke garin Deidei a Birnin Tarayya Abuja, ta zama mafakar mabarata da suka hada da tsoffafi da zawarawa da ke rike da kananan yara, sai kuma guragu. Haka wadansu ’yan kasuwa na amfani da gadar da ke kan hanyar Kubwa zuwa Zuba wajen kasa hajarsu don masu ratsawa ta kanta da adadinsu ke karuwa da safe ko yamma.

Sai dai a cikin mabaratan, hankalin masu ba da sadaka ya fi karkata ne a kan wadansu mata da ke zuwa bara da yara ’yan uku da yawanci suke kwantar da su a gabansu suna neman taimako. Matan da ke bara da ’yan ukun kamar yadda Aminiya ta samu labari adadinsu ya kai uku, sai dai a cewar majiyarmu matan ba su yarda su kasance a wajen a rana guda, “Sai dai guda ta zo na kwana 2 zuwa 3, sannan wata daga cikinsu kuma ta karbi ragamar zuwa na tsawon wannan lokaci,” inji majiyarmu.

Wakilinmu wanda a farkon zuwansa wurin ya zanta da daya daga cikin masu ’yan ukun, wata daban ya tarar daga cikinsu a lokacin da ya koma a karo na biyu, haka a zuwa na uku a baya-bayan nan, ya tarar da wata daban ce tare da nata ’yan ukun.

Matar mai suna Chikodi Okoro ta gabatar da wata yarinya da ke tare da su a matsayin ’yar yayarta da ke tallafa mata wajen rike musu lema don rage zafin rana, kuma ta rike mata daya daga cikin yaran a lokacin fitowa ko komawa gida. Matar wadda ta ce ta fito ne daga yankin Agwu a Jihar Enugu, ta ce ta shiga bara da ’yan ukun ne bayan mutuwar mijinti tun yaran na da wata 3 a ciki.

Ta ce mjinta wanda kafin rasuwarsa yana aikin gini ne a Abuja, an maida gawarsa gida Enugu inda aka yi bikin binne ta daga baya ne ta dawowa Abuja ta rungumi dawainiyar iyali ita kadai. “Da dan abin da muka samu a bara ne nake kula da ’yan ukun da wadansu ’ya’yanmu hudu, ciki har da karatunsu a wata makaranta da ke garin Nyanya Abuja inda muke zaune, sai kuma ni kaina da wannan yarinya da muke tare. Allah Ya albarkace mu da tagwaye a haihuwata ta farko, sai karin ’ya’ya biyu a haihuwa ta 3 da ta 4 sannan wadannan ’yan ukun. Sai dai na gode Allah tare da daukar lamarin a matsayin kyautar Allah saboda wadansu da dama na neman su samu haihuwa ba su samu ijaba ba,” injita.

Ta ce bayan dawowarta daga gida da farko majami’arsu ta taimaka mata da kudi inda ta fara sayar da kayan lambu a Kasuwar Utako da ke Abuja kafin yawan bukata ta kula da iyali ta cinye jarin. Ta ce sunayen ’yan ukun su ne Fabour da Monachi wadanda mata ne, sai kuma Daniel, namiji.

  Madam Chidoka Okoro tare da nata ’yan ukun a kan gadar Deidei
Madam Chidoka Okoro tare da nata ’yan ukun a kan gadar Deidei

Umar Muhammed Nahuche wanda dan asalin Karamar Hukumar Bungudu ne a Jihar Zamfara, na daya daga cikin guragu 4 da suka dora wa kansu share kan gadar a kowane yini inda wadansu daga cikin masu ratsawa ta wajen ke ba su sadaka.  Da ya ke amsa tambayar Aminiya kan zargi da ake yi wa wadansu daga cikin mata masu bara da ’yan uku, ya ce a tsawon zaman da ya yi da su a wajen ya kula cewa da wuya matan su shayar da nono ga yara ukun da ke gabansu.

“Za ka samu yaro daya ne ko biyu suke bai wa nono, yayin da daya daga cikin yaran ko kuma biyu sai su shayar da su da wani abinci na yara a robar jarirai. Haka kuma sau da dama tsofaffin mata da muke tare da su a nan, suna tantance hakikanin da ga matan daga cikin ’yan ukun bayan yin nazari da siffofin kamanni, yayin da suke bayyana cewa wadansu daga cikin yaran ba hakikanin ’ya ’yansu ba ne.

Aminiya ta samu labarin cewa baya ga karba-karba da mata ukun ke yi don bara a wajen, suna kuma kaurace wa wajen dungurugum a wani zubin inda wajen zai kasance ba ko guda daga ckinsu na dan lokaci.

Wadansu nakasassu da ke da abin yi a wurin

Abdullahi Muhammad daga Karamar Hukumar Nasarawa a Jihar Kano, ya ce ya shekara uku yana aikin shara a kan gadar. Ya ce yakan sayi ruwan leda yana watsawa lokacin da yake sharar don rage kura ga jama’a da ke ratsawa. Ya ce wadansu daga cikin jama’ar na taimaka masa da sadaka.

Da Aminiya ta tambaye shi ko akwai wani abu na tallafi da ke fitowa daga bangaren hukuma dalilin aikin nasu. Matashin ya ce “Babu wani abu a tsakaninmu da hukuma sai dai cutar da mu da jami’an duba garinta ke yi idan suka kawo samame a wani zubin. Suna zargin cewa muna fakewa ne kawai da yin sharar muna yin bara. Kamar wata 3 da suka wuce sun kama ni suka kai ni wani waje a Bwari sai da aka yi belina kan Naira dubu 16.”

Kan ko me ya sa bai hakura da zama a cibiyar ba kasancewar ana koya wa nakasassu sana’a, Malam Abdullahi cewa ya yi: “Suna koyar da sana’a ce ga wadanda iyayensu suka kai su wajen tare da biya musu kudin makaranta. Amma yawancin ire-irenmu da suka kama da sunan bara killace mu suke yi a wuri guda a matsayin masu laifi. Gashi babu damar yin Sallah babu abinci a kan kari a inda aka tsare ka za ka yi fitsari da bahaya, wajen dai yana nan tamkar kurkuku ba abin da ake yi sai zalunci.”

Wani guragu da ke kasuwanci a wurin mai suna Ashiru Adamu dan asalin Karamar Hukumar Kafur a Jihar Katsina da ke sayar da magogin roba da mansa da kayan wayar hannu, ya ce ya yi kamar shekara daya a wurin yana kasuwanci. “A baya nakan shiga cikin gari ne kamar masallatan Juma’a ina bara. Sai dai yawan musguna mana da duba gari suna kai mu gidan nakasassu na Bwari ya sa na hakura na kama kasuwanci. “Idan suka ga kai yaro ne sai su ce me ya sa ba za ka yi karatu ba, idan kuwa babba ne sai su ce me ya sa ba za ka yi sana’a ba? Wannan ya sa da na samu fitowa na kama kasuwanci,” inji shi.

Ya ce ya yanke shawarar yin kasuwancin ne bayan an kai shi wajen har sau 2 inda mahaifinsa ke zuwa daga gida Katsina yana yin belinsa. “Sai dai yanzu alhamdu lillahi na samu dogaro da kaina, har ni ke aike wa iyayena kudi baya ga biyan bukatun kaina da nake yi,” inji matashin.

Wata dattijuwa mai suna Adama wacce ta taho Abuja daga Karamar Hukumar Babura a Jihar Jigawa, ta ce ba ta wuce kwana uku da fara zama a kan gadar ba tare da wata da ke kusa da ita mai suna Maimuna Bukari, wadda ita kuma ce ta zo wajen ne bayan rasuwar mijinta da ya barta da ’ya’ya bakwai.

“Kuma kasancewar ban samu wanda zai aure ni ba, har zuwa wannan lokaci sai na yanke shawarar zuwa nan don neman abin da za mu rike kanmu,” inji ta.