Da Dumi Dumi

Yadda wata amarya ta ‘hadiyi zuciya’ ta mutu

Amare da yawa kan yi kuka idan za a kai su gidan miji—galibi ba don ba sa son zuwa gidan mijin ba, sai dai don zafin rabuwa da iyaye da sauran ’yan uwa.

Amma a wasu lokutan, wasu amaren kan yi kukan saboda dalilan biyu—za su rabu da ’yan uwa, kuma ba sa son mijin da za a kai su gidanshi.

Mai yiwuwa Hansatu, wata ’yar shekara 17 da haihuwa, ta yi irin wannan kuka ranar da aka kai ta dakinta—don kuwa binciken ‘yan sanda ya tabbatar da cewa auren dole aka yi mata.

Watakila ma shi ya sa da aka wayi gari aka same ta a mace a tsakar dakinta kwana 20 bayan budar kai aka yi amanna cewa ta hadiyi zuciya ne ta mutu.

Amma masu iya magana kan ce “Ruwa ba ya tsami banza”, me ya kai ga wannan amarya ta hadiyi zuciya?

ADVERTISEMENT

Ina dalili?

Wannan lamari dai ya faru ne a kauyen Kankaleru da ke karamar hukumar Ringim a jihar Jigawa, inda ’yan sanda suka kama angon Hansatu, wani matashi mai shekara 30 a duniya, a matsayin wanda suke zargi na farko.

Amma kafin nan sai da jami’an tsaron suka dauki amaryar suka kai ta asibiti aka tabbatar da cewa ba ta numfashi sannan suka fara bincike.

Binciken kuma, kamar yadda Jami’in Hulda da Jama’a na Rundunar ’Yan Sanda ta jihar Jigawa, SP Abdu Jinjiri ya tabbatar, ya nuna cewa angon ya sha tunkarar marigayiyar da batun sunnar aure, amma tana nuna mishi cewa ita fa ba shi ta so ta aura ba, don haka ba za ta yarda da shi ba.

Kwana ya kare

A jajibirin ranar da lamarin ya faru dai, angon ya yi amfani da karfi don biya wa kansa bukata, lamarin da ya sa marigayiyar, wacce ta kasance ba ta kaunar wata mu’amala ta aure ta shiga tsakaninta da shi, ta hadiyi zuciya, inji ‘yan sanda.

SP Jinjiri ya kuma ce angon na hannun ’yan sanda suna ci gaba da bincike, kuma da zarar sun kammala za su gurfanar da shi a gaban kotu.

Ba wannan ne dai karo na farko da ake samun wata baiwar Allah mai karancin shekaru ta rasa ranta ba a jihar ta Jigawa.

Ko a makon jiya ma an samu wata ‘yar shekara 15 da ta kashe kanta a karamar hukumar Gwaram.

Tura
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya