Search
Subscribe
Yadda wata mata ta farke cikinta da reza ta ciro jariri

Yadda wata mata ta farke cikinta da reza ta ciro jariri

Wata mata mai suna Misis Joyce Kalinda a kasar Tanzaniya ta yi wa kanta tiyatar haihuwa inda ta yi amfani da reza ta farke cikinta ta ciro jariri.

‘Yan sandan Tanzaniya sun tabbatar da al’amarin inda suka bayyana Misis Joyce Kalinda ‘yar shekara 30 da aikata hakan.

Lamarin wanda ya ba mutane mamaki ya faru ne a Kirondo da ke kusa da tafkin Tanganyika a lardin Rukwa Kudu maso Yammacin Tanzaniya.

Matar ta gudo ne daga dakin karbar haihuwa a asibiti zuwa gida. Bayan ta dawo gida ne ta dauki reza ta farke cikinta ta ciro jaririn.

Babban jami’in ‘yan sandan yankin ya ce, matar ta aiki ’yarta ne, kafin ’yar ta dawo ta iske mahaifiyarta da jariri, daga nan ne kuma ’yar ta nemi taimakon makwabta.

An sake mayar da ita asibitin Kirondo. ‘Yan sanda sun ce babu wani laifi da ta aikata bayan gudanar da binciken lafiya a kanta da kuma jaririn. Jaririn da ta ciro da reza shi ne na takwas da ta haifa. (Daga Majiyar BBC ).

 

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin