✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda ’yan bindiga suka kone mutum 30 a Katsina

Wani mummunan hari da ’yan bindiga suka kai wasu kauyuka biyu a Karamar Hukumar Batsari a Jihar Katsina ya hallaka mutum sama da 30, lokacin…

Wani mummunan hari da ’yan bindiga suka kai wasu kauyuka biyu a Karamar Hukumar Batsari a Jihar Katsina ya hallaka mutum sama da 30, lokacin da ’yan bindigar suke banka wa gidajen jama’a wuta.

Sama da mutum 27 ne suka kone kurmus a kauyen Tsauwa inda har zuwa lokacin da wakilinmu ya isa kauyen ake aikin tono wasu gawarwakin daga cikin buraguzan gini, yayin da ba a san halin da suke ciki ba.

Aminiya ta samu labarin cewa ’yan bindigar da ake zargin sun kai harin ramuwar gayya ce, sun je kauyen ne a kan babura akalla 150 dauke da mutum uku a kan kowane babur da suke dauke da bindiga, inda wata motar kirar Kanta ke biye da su.

Jama’ar garin sun ce maharan sun shiga garin Tsauwa lokacin da mutane ke Sallar Magariba da misalin karfe 6:30 na yamma zuwa wajen karfe 8:00 duk da gwamnatin jihar ta kafa dokar hana hawa babura daga karfe 7:00 na yamma zuwa karfe 6:00 na safe.

“Sun shigo garin ne daga bangaren gabas tare da fara cinna wa garin wuta gami da harbin kan mai uwa da wab, kamar yadda kuke gani. Wutar ta cinye akalla kashi 90 cikin 100 na garin, duk da alamun da suka nuna tamkar an zabi gidajen da aka sanya wa wutar ne,” iji wani mazaunin garin.

Mafi yawan wadanda suka rasa rayukansu ta hanyar konewar mata ne da tsofaffi da kananan yara tare da dabbobi da kayan abinci.

Abubuwan da wakilin Aminiya ya gani, akwai gawar wata yarinya wadda ba ta wuce shekara hudu ba wadda hayakin wutar ya kashe. Sai kuma kasusuwan da suka rage na wata yarinya mai kimanin shekara biyu mai suna Yado da mahaifinta Alhaji Akilu ya tattara. Sai kuma ’yar uwarta da gawayinta ke cikin dakin da ya toye tare da mahaifiyar yaran wato matarsa.

Har ila yau, akwai gawar wata mata wadda ta kone tana rungume da ’ya’yanta hudu wadanda duka suka zama toka. Kuma Aminiya ta samu labarin cewa, mijin matar mai suna Ila da dan uwansa Tsalha maharan sun kashe su.

A wani gidan da Aminiya ta leka, ta ga gawar wani dattijo ne wanda aka ce ya haura shekara 60 kuma ba ya da lafiya. Gawar ta kone kurmus tare da wani karamin yaro da alamu suka nuna yana kwance kusa da dattijon.

A wani bangaren gawar wani mai suna Isa Na-Bara’u ce mai shekaru sama da 50 da aka yi wa wanka bayan harbin bindiga akalla biyu a cikinsa ba ya ga karya masa kafada da harsashe ya yi.

Kazalika, Aminiya ta tarar da wadansu dattawa da suka kubuta daga harin suna ta hidimar dinka likkafani domin rufe wadanda aka samu gawarwakinsu.

Can kuma a makabartar garin kaburbura ne ake ta hakawa yayin da ake kawo wasu gawarwaki ana rufewa.

Mai unguwar garin ya ce, har zuwa lokacin zuwan ayarin Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Katsina Alhaji Sanusi Buba da ’an jarida bai samu damar yin Sallar Magaribar da harin ya hana su yi ba, yana nan makabartar ana rufe jama’a.

Har barowar ayarin garin na Tsauwa, ba a fara tattara gawarwakin da suka kone ba domin ana rufe wadanda ake ganin in an bar su za su yi kumburi ne su fashe.

Duk da cewa, an samu rahotannin da suka saba wa juna, mafi yawan mutanen da Aminiya ta zanta da su sun ce, mutum 27 ne aka tabbatar sun mutu ta hanyar konewa wadanda mafi yawansu mata ne da kananan yara da kuma tsofaffi. Batun dabbobi mutanen kauyen sun ce ba a san yawan wadanda wutar ta ci ba, baya ga wadanda ’yan bindigar suka kora.

Bugu da kari, mutanen kauyen sun ce a yayin da maharan suke kunna wuta a wasu sassan garin, wadansu kuma na can na fasa shaguna da gidaje suna kwasar kayan abinci da sauransu. Kuma duk inda suka dauki abin da suke so, saura sai su sanya masa wuta.

Mazauna kauyen na Tsauwa sun ce kayan da maharan suka dauka sun rika sanya su a cikin wancan Kanta ce da suka zo da ita.

Malam Abdul’aziz na daga cikin wadanda suka tsira daga harin, ya ce, “Lokacin da na ji hayaniya ta yi yawa, na nufi tsallake katanga tare da matata wadda na taimaka muka fitar da ’ya’yanmu uku. Bayan mun fita, yaro daya ya sake dawowa cikin gidan ya kwanta a cikin wannan daki. To a bisan dakin akwai harawar da aka tanada ga dabbobi, ta kama da wuta wadda zafin wutar ya sake fiddo shi daga ciki, domin ina kokarin sakin shanuna da wutar ke gab da kaiwa gare su. Gaskiya babu wanda ya rasa ranai daga cikin iyalina, sai dai dakunan da wuta ta cinye. Su ma wadansu tsofaffin mata biyu, sun ce babu abin da ya same su a cikin dakin da suke kwance, sai dai daya dakin ne hayaki ya kashe wata yarinya.

Sun ce akwai mutane da dama da suka tsira walau ta gudu zuwa cikin daji ko kuma harin bai kai gidajensu ba.

Shi dai wannan hari wanda wadansu ke cewa ramuwar gayya ce kan kashe wadansu ’yan bindigar da ake zargin mutanen kauyen sun yi, wani da ya nemi a sakaya sunansa ya ce, “A ranar Talatar da ta gabata wani mutumin garin Tsauwa ya kai iyalinsa asibitin kauyen Dankar, bayan ya ajiye su wadansu sun roke shi ya kai wadansu mata biyu zuwa garin Kurmiyal kafin a kammala duba iyalinsa, kasancewar an san yana sana’ar acaba da babur. Ba tare da ya san ko akwai wani abu a bisa hanyar ba, ya amince ya dauko matan. A hanyar ce ya ci karo da wadansu mahara a daidai kauyen Fakon Dankishiya. Barayin sun nemi ya ba su babur din da yake kai, amma ya ki. Nan suka fara ba-ta-kashi inda Allah Ya ba shi sa’a ya yi nasara a kansu har ya kwace nasu babur din.”

Ya ce, a karshe ya tafi da babur din zuwa garinssu Tsauwa. “Daga bisani barayin suka biyo sawu suka tare wani dan garin suka karbe nasa babur din. Mutanen Tsauwa sun bi su har cikin dajin da suka nufa, suka karbo babur din kuma aka ce sun kashe mutun guda daga cikin mutum ukun da suka bi. Sun kuma kwato bindiga daga hannun barayin. To dama can baya barayin sun sha kai hari mutanen Tsauwa na korarsu. To wadannan abubuwa ne ake zaton suka sa maharan suka yiwo gayya don ramuwar gayya, bayan an karbi bindigar da babur din ta hanyar sa bakin wadansu manya,” inj shi.

Wasu bayanai sun ce, jama’ar kauyen sun ki bayar da bindigar duk da kokarin da jami’an tsaro suka yi har sai a wannan rana ta Juma’a da aka kai harin.

Wadansu daga cikin mutanen kauyen suna zargin cewa akwai hadin baki, domin a cewarsu, ba a yi awa cikakkiya da karbar bindigar daga mutanen kauyen ba, sai maharan suka shiga kauyen suka auka musu.

Wata majiya ta ce kafin maharan su shiga kauyen Tsauwa mai nisan kilomita 10 daga garin Kurmiyal da ke da tazarar kilomita 33 a tsakaninsa da Katsina babban birnin jihar, sai da suka fara yi wa kauyen Darkar mai nisan kilomita 7 daga Kurmiyal dirar mikiya inda suka kashe mutum tara tare da yin awon gaba da dabbobi da kayan abinci.

Harin kauyen Dankar kamar yadda wadansu suka shaida wa Aminiya, an kai shi ne da nufin a hana mutanen kauyen kai dauki ga mutanen Tsauwa wanda bisa ga alamu shi ne babban kudirin ’yan bindigar.

Lokacin da Aminiya ta isa kauyen Dankar tare da ayarin Kwamishinan ’Yan sandan babu kowa a cikinsa sai wadansu dattawa da ba su wuce mutun uku ba, domin duk mutanen kauyen sun yi hijira, duk da cewa ba a kone komai ba kamar yadda aka yi a Tsauwa.

Kwamishinan ’an sandan Jihar Katsina, Alhaji Sanusi Buba ya ce, ana zargin maharan sun fito ne daga dajin Zamfara. Kwamishinan ya ce, jami’an tsaro da gwamnatin jihar bisa jagorancin Gwamna Aminu Bello Masari suna iya kokrinsu na ganin cewa an samu zaman lafiya a tsakanin al’umma.

“Batun daukar fansa da ake cewa babu dalilin yin haka, tunda akwai hukuma sai a kai koke-koke don daukar mataki. Saboda haka, ina kira ga jama’a su daina daukar doka a hannunsu,” inji shi.

’Yan bindigar wadanda suka fara shiga garin Dankar sun kashe mutum tara, amma wata majiyar daga mutanen garin ta ce mutum 11 suka kashe.

A ziyarar jaje da Gwamna Masari ya kai wa al’ummar da abin ya shafa a ranar Litinin, ya shaida wa jama’ar garin Tsauwa cewa, za a kai masu tallafin gaggawa na kayan abinci da sauran kayan amfanin yau da kullum. Kazalika za a tallafa musu da kekunan shanu da jakuna domin ci gaba da nemo ruwa kamar yadda suka yi kuka suna fuskantar matsala, saboda duk wani abin amfani ko dai maharan sun tafi da shi ko sun kone shi.

Har ila yau, Gwamnan ya ce za a tura da injiniyoyi domin duba yadda za a gina musu riyojin burtsatse, kuma a gyara musu hanyarsu ta hanyar shigar da su cikin wani shiri na Bankin Duniya. Kuma ya ce gwamnatin za ta gina musu makaranta inda ya ce karancin ilimi ke haddasa ire-iren wadannan matsaloli, kuma ya ce za a kara yawan jami’an tsaro a yankin.

Gwamnan yana mayar da jawabi ne bayan koken da Mai Unguwa Ibrahim Zangina na garin Tsauwa da takwaransa Mai Unguwa Sake Kandawa suka yi kan matsalolin da suke damun jama’arsu.

Shi kuwa Liman Haruna na garin Dankar kokawwa ya yi kan yadda mutanen garin ke ta gudun hijira inda ya ce, in ba a yi hankali ba zai iya kashe garin baki daya.

A nan Gwamna Masari ya ja hankalin jama’ar kauyen cewa, yin hijirar ba ita ce maganin matsalar ba. Su ci gaba da addu’a tare da daukar kaddara.

Yanayin kauyukan

Kauyukan biyu da ke Arewa da garin Kurmiyal a hanyar zuwa Batsari daga Katsina wadda ta burji ce mai ramuka da dama. Kauyen Dankar ya fi Tsauwa girma, kuma shi ne ke da alamun alkarya domin har da dakin kallon talabijin kuma bai shiga cikin tsaunuka ba kamar na Tsauwa. Ana iya samun kiran waya a Dankar. Kuma lokacin da ayarin ’yan sanda da ’yan jarida suka tunkari kauyen, sun ga mutane suna ta nufa Kurmiyal, masu babura na dauko iyalansu wadansu har da awaki ko tumaki da kullin ’yan kaya suna ficewa daga kauyen.

Yankin mai yawan tsaunuka da ramuka da kwazazzabai, mafi yawansa daji ne da za a iya bi a shiga har dajin Zamfara da maharan suka yi amfani da shi kamar yadda jama’ar suka ce.

A wani labarin, ’yan sanda sun kama wani mutun da ya kai awaki cikin garin Katsina don ya sayar daga yankin da aka kai harin washegarin kai harin, inda ake tuhumarsa. Kazalika ’yan sanda da hadin gwiwar sojojin da suka kai dauki yankin sun yi nasarar kama babura tara da ake bincike a kansu.