Da Dumi Dumi

‘Yadda ’ya’yana 3 maza uku suka makance suna samari’

Hajiya Huraira Muhammad wadda take bayan Babban Masallacin Lafiya fadar Jihar Nasarawa ta bayyana yadda ’ya’yanta uku maza suka makance daya-bayan-dayayayin da mata uku suke nan garau da idanuwansu.

Da take zantawa da Aminiya a Lafiya, Hajiya Huraira ta ce, “Allah Ya ba ni haihuwa shida, uku maza kuma uku mata. Amma abin mamaki shi ne, mazan uku duk sun makance. Babban dana ya yi zazzabi, aka yi masa karin ruwa, bayan kwana uku, sai na ce ya fito waje don ya sha iska, sai ya ce ba ya gani sosai. Sai muka sa aka yi rokon Allah Ya samu sauki, daga bisani dangi suka yi taron gaggawa, aka kai shi asibiti a Kano, suka tambaye mu ko mun kai shi aikin walda ne ko ciwon gadon gidanmu ne, muka ce a’a, babu ko daya. Bayan gwaje-gwaje, sai suka ce mu koma gida mu hakura.”

Ta ci gaba da cewa:  “Bayan nan sai na biyu ya kamu da irin ciwon, kuma sai shi ma na ukun ya kamu. Amma na gode wa Allah domin duk da cewa mahaifinsu ya rasu, ba sa yin bara, har sun fi wadansu masu idon kokarin neman na kansu.”

Ku nemi Jaridar AMINIYA don samun cikakken rahoton.

ADVERTISEMENT
Share