✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda za a kula da fata lokacin sanyi

Barkanmu da sake saduwa da ku a wannan sabon yanayi da muka shiga na sanyi. Hazo da hunturu da iska da ake yi suna sanya…

Barkanmu da sake saduwa da ku a wannan sabon yanayi da muka shiga na sanyi. Hazo da hunturu da iska da ake yi suna sanya fatarmu ta lalace. Sai a ga mutum ya fara kauje da kurarraji a fata. Yana da matukar muhimmanci a kula da fata musamman a wannan lokaci. Don haka ne a yau na kawo muku abubuwa da dama da za a bi don kare fata.

• A kasance ana shan ruwa sosai kamar kofi takwas a rana. Yin hakan na dada hasken fata.

• Ana shafa man jiki kamar su ‘moisturizers’, domin kare fata daga zama mai gautsi.

• Kada ana kwanciya da kwalliya a fuska: Kwanciya da kwalliyar fuska na sanya kurarrajin fuska. A rika  wanke fuska da sabulun wanke fuska kullum kafin a kwanta barci.

• Yana da kyau a rage zama a cikin rana. Domin hakan na sanya maikon fuska da sanya kuraje da kuma canja wa fata launi.

• Shin ko kun san cewa barci na dada kyau? Kwanciya da wuri domin samun barci na awa takwas na dada lafiyar fata.

Abubuwan da za a yi don samun fata mai santsi a hunturu

• A kwaba ayaba da danyar madara sannan a shafa a fuska. A jira na tsawon minti 20 kafin a wanke da ruwan dumi. Hakan na sanya fata santsi.

•         A shafa kwababbiyar gwanda a fuska da wuya. Sai a jira na tsawon minti 15 kafin a wanke.

•        A tafasa kabeji sai ana wanke fuska da ruwan. Yin hakan na gyara fata sosai.