Da Dumi Dumi

Yadda za a samu fata mai haske cikin kankanen lokaci

Fatar jiki na daya daga cikin abubuwan da suke kare jiki baki daya. Domin kafin komai ya taba cikin jiki sai ya taba fata. Don haka wajibi ne mu kula da fatar jiki. A yau na kawo muku hanyoyi da dama da za a bi domin sanin yadda za a kara hasken fata da kula ta a cikin kankanen lokaci. Amfani da abubuwa kamar gurji da lemun tsami da ruwan ‘glycerin’ na cikin abubuwan da suke kare fata daga kunar rana da ke janyo kodewar fata, sannan ya sanya ta haske da sauransu.

  • A rika shafa ruwan lemun tsami da auduga kullum dare kafin a kwanta barci bayan an wanke fuskar da sabulu. Yin hakan na dada wa fata haske.
  • A matse ruwan dankalin Turawa sannan a rika shafawa a fuska a kullum kamar sau biyu; safe da yamma sannan sai a wanke da ruwan dumi wannan hadin na haskaka fata.
  • Idan biki kuma za a yi ana son yin kwalliya ga fatar da ta yi duhu, sai a samu ayaba a bare ta sannan a kwaba ayabar sai a shafa kwabin a fuska na tsawon minti 10 zuwa 15 sannan a wanke za a yi matukar mamaki yadda fatar za ta kara haske cikin kankanen lokaci.
  • Idan ana da fata mai yawan maiko, za a iya amfani da ruwan gurji da ruwan lemun tsami a gaurayasu sannan a rika shafawa a fuska ko jiki domin samun fata mai haske.
  • A samu bawon lemu a busar da shi sai a daka a tankade sannan a samu madara a kwaba sai a shafa a fuska na tsawon minti 20, shi ma sai an yi mamakin yadda fuskar ta kara haske.
  • Za a iya shafa ruwan ‘glycerin’ ko ‘rose water’ a fuska domin samun fuska mai sheki da kuma santsi.
  • A samu ruwan kwai sannan a yawaita shafa farin ruwan a fuska a kullum domin sanya fuska haske da sheki da kuma laushi. Idan za a iya, sai a shafa a jikin baki daya.

Share