✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda za a sasanta da ’yan uwa Musulmi da sojojin Masar

Gungun ’yan tawayen Masar sun shirya yadda za a sasanta tsakanin Sojoji da kungiyar ’yan uwa Musulmi ta hambararren shugaba Muhammad Mursi. kungiyar ta Jama’a…

Magoya bayan Shugaba Muhammad Mursi a wajen taronsuGungun ’yan tawayen Masar sun shirya yadda za a sasanta tsakanin Sojoji da kungiyar ’yan uwa Musulmi ta hambararren shugaba Muhammad Mursi. kungiyar ta Jama’a Islamiyya da Jihadin Musulunci, sun yi kira ga magoya bayan Mursi da su daina zanga-zanga a tituna da zarar gwamnatin da sojoji suka kafa ta daina hantararsu.
kungiyoyin biyu da suka taba yakar gwamnati a shekarun 1990, amma daga bisani suka daina tashe-tashen hankula, sun bukaci sojoji da ’yan uwa Musulmi su shiga tattaunawar sasanci.
Shugaban kungiyar Jihadin Musulunci, Muhammad Abu Samra, ya bayyana wa Kamfanin Dillancin Labarai na AP sun gabatar da shawarar sasantawar ne ba tare da wasu sharudda masu wuya ba. Duk da cewar kungiya ba tana magana da yawun ’yan uwa Musulmi ba ne, wannan na nuni da sassauci a gungun magoya bayan Mursi. Mafi yawan shugabannin kungiyar ’yan uwa Musulmi suna can a tsare, kuma yawan farmakin da ake ta kai musu ya raunata gangamin da suka shirya.
Shi ma mai shiga tsakanin ’yan uwa Musulmi da hukumomin kasar, Amr Darrag, ya bayyana cewa, kungiyarsa a shirye take ta shiga tattaunawa, amma tana bukatar “kwarin gwiwa.” Sai dai ya bayyana cewa “daya bangaren bai nuna alamun ya yi shirin sasantawa ba,” inji shi.
Gwamnatin Masar na ci gaba da kassara duk wata harka ta ’yan uwa Musulmi, musamman al’amuran da suka shafi harkokin kasuwancinsu, kuma kafofin yada labaran Masar kullum sai sukarsu suke yi, tun bayan da aka rufe gidan talabijin din sun a “Islamist Tb. A halin yanzu har danganta su ake da ta’addanci.
A Litinin din da ta gabata, hukumomi sun tsare wata malama a birnin Nile Delta da ake kira Kafr el-Zayat, bayan da aka sameta tana koya wa kananan yara wakokin yabon Mursi da na adawa da sojoji, kamar yadda jami’an tsaro suka bayyana.
Firayiministan riko na Masar, Hazem AlBeblawi ya yi nuni da cewa akwai dole kungiyar ’yan uwa Musulmi ta sassauto daidai da sauye-sauyen da suka auku a Masar, duk da cewa magoya bayan Mursi na ta kiraye-kirayen ci gaba da zanga-zanga.
Da wuya kungiyar ’yan uwa Musulmi  asasanta da gwamnatin da sojoji ta kafa, matukar ta dauke su a matsayin ’yan ta’adda, musamman ganin yadda take musguna wa ’ya’yanta. Don haka wannan matsala ta Masar za ta yi wuyar warwarewa, kamar yadda masu sharhi kan al’amuran yau da kullum ke kallon rikicin siyasar da ya dabaibaye kasar.