✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda zan mulki Zamfara – Zababben Gwamna

Kogunan Gusau, Alhaji Mukhtar Shehu Idris ne zababben Gwamnan Jihar Zamfara. A tattaunawarsa da Aminiya, ya fayyace dangantakar da ke tsakaninsa da Gwamnan Jihar Zamfara…

Kogunan Gusau, Alhaji Mukhtar Shehu Idris ne zababben Gwamnan Jihar Zamfara. A tattaunawarsa da Aminiya, ya fayyace dangantakar da ke tsakaninsa da Gwamnan Jihar Zamfara mai barin gado, Abdul’aziz Yari da abubuwan da suka wakana a zaben fid da gwani da rade-radin da ake yi cewa yana da alaka da Baturiyar Zabe ta Jihar Zamfara, Dokta Asma’u Maikudi da sauransu. 

 

Da gaske an sa maka ranar aure da ’yar Baturiyar Zabe ta Jihar Zamfara kamar yadda ake rade-radi?

Ina da aure ai. Ina da mata biyu da ’ya’ya takwas. Don haka ban gane abin da ka fada ba.

Amma ai Musulunci ya ba ka dama ka auri sama da mata biyu, sannan ana rada-radin kana shirin kara aure?

Eh! Musulunci ya ba ni damar auren mata hudu. Amma maganar ita ce ban san Baturiyar Zaben Zamfara ba sai bayan da aka fara yada rade-radin cewa wai zan auri ’yarta. Ban san ta ba, ballantana in auri ’yarta. Kuma ina tunanin in ba a fosta ba, ba na tsammanin ita ma ta taba ganina.

’Yan adawa suna zargin cewa an shirya tsaf don bikin aurenka da ’yarta bayan ka lashe zabe a matsayin haryar da za ka saka mata bisa yadda ta murde zabe. Ina gaskiyar wannan zargin?

Ta yaya Baturiyar Zabe za ta murde zabe saboda ni alhalin kowa yana ganin abin da ke wakana a fili. Ba zai yiwu ba ta ba ka takardun zabe. Idan an ba ka me za ka yi da su? A rumfunar zabe ake sanar da sakamakon kowane zabe, kuma daga nan sai a kai cibiyoyin tattara zaben na mazabu. A nan ma a sake sanar da sakamakon a bayyane, a haka har a kai sama. Ka ga ke nan a fii ake lamarin. Don haka me Baturen Zabe zai iya yi maka a wannan tsari? Kawai an sanya Baturen Zabe ne domin su tabbatar an bi doka da tsarin zabe. Maganar auren ’yarta kuma labaran kanzon kurege ne kawai. Ban ma san ko tana da ’ya ko ba ta ita ba.

Idan an rantsar da kai me za ka yi daban da Gwamna Yari a gwamnati?

Kasancewar ina cikin gwamnatinsa, dole zan tabbatar na ci gaba daga inda ya tsaya. Amma babban abin lura shi ne lamarin tabarbarewar tsaro. Dole mu kawo sababbin tsare-tsare. Ka san idan kana fada da ’yan ta’adda, duk yadda ka yi wajen magance matsalar, sai su ma sun fito da wani tsari. Don haka za mu dage wajen sababbin tsare-tsare cikin sauri ta yadda za mu kasance mun fi su saurin daukar mataki, maimakon mu rika jira sai sun kai hari kafin mu dauki mataki. Wannan shi ne abin da za mu yi tare da jami’an tsaro. Jami’an tsaro suna ta kokarin kawo sauyi wajen maganin matsalar, amma ba abin da za mu fada ba ne a jarida. Amma ina tabbatar muku cewa nan da ’yan makonni masu zuwa kafin Gwamna Yari ya kare mulkinsa, mutanen Zamfara za su ga canji matuka. Muna da jami’an tsaro da dama a kasa, sannan jami’an tsaron sa-kai ma suna bakin kokarinsu.

Abin takaicin kawai shi ne yakin sunkuru yana da wahalar gaske domin ba ka sanin makiyinka. Kana fada ne da mutanen da ba a gane su, kuma ba ka san ta yaya ko  yaushe za su kawo hari ba. Kawai

 

dai ka san abin da suke tunani ne. Za mu yi duk abin da za mu iya wajen tabbatar da cewa mun yake su.

Yadda Gwamna Yari ya tsayar da kai a matsayin wanda zai gaje shi ya haifar da cece-kuce a Jihar Zamfara. Me ya sa ya ce dole sai kai?

Kamar yadda mutane suke fada, masu ruwa-da-tsaki ne suka tsayar da ni. Duba ka ga wadanda suke fada da lamarin daya bayan daya, za ka ga dukansu sun ci moriyar ubangida. Misali Sanata Marafa, ubangida ne ya daga shi. Lokacin da ya tsaya Sanata na farko da na biyu duk ubangida ne ya tsayar da shi, amma bai taba cewa a’a ba. Haka  Mataimakin Gwamna Ibrahim Wakkala. Shi ma hakan abin yake. Shi ma Abu Magaji, lokacin da aka ba mu damar fitar da Babban Sakatare a Gwamnatin Tarayya, mutane kadan kawai ne aka tattauna da  su, sannan aka fitar da sunansa.

Don haka dukansu sun ci moriyar ubangida. Kawai saboda ba su aka tsayar ba, sai suka fara tada jijiyar wuya. Zabin ubangida sanannen abu ne a siyasa, kuma ana yi a ko’ina. Idan ka je Legas ana yi, ana yi a Sakkwato da sauransu.

Bayan Yari sai wane ne ya zabe ka?

Dukan jam’iyyar ta zabe ni, kuma ta amince da ni a matsayin dan takara kuma har yanzu babu wani dan jam’iyya da ya fito ya nuna cewa ba ya tare da ni.

Amma akwai bangarori biyu na Jam’iyyar APC a Jihar Zamfara, wanne kake magana a kai?

Babu bangarori a Jam’iyyar APC a Jihar Zamfara. Kotu ta riga ta yanke hukunci cewa Jam’iyyar APC guda daya ce.

Amma lura da yadda aka ta kai-koma, inda mambobin G-8 suka yi fito-na-fito da tsayar da kai, yanzu haka suna cewa kotu za ta cire ka bayan an rantsar da kai. Yaya kake shirin fuskantar wannan?

Wannan kuma tunaninsu ne. Kotun Jiha ta yanke hukunci, kuma Kotun Tarayya ta tabbatar. Don haka mene ne suka fada? Babu inda aka yi watsi da daukaka kara. Don haka muna jiransu. Idan bayan zaben sun tafi Kotun Sauraron Kararrakin Zabe, to muna da takardun da za mu nuna, kuma muna da mutane.

Yawanci akan samu sabani a tsakanin ubangida da wanda ya gaje shi. An taba samun irin haka a Zamfara. Ba ka tunanin hakan zai iya faruwa tsakaninka da Yari?

Mutane suna tsoron haka, amma akwai inda aka ci gaba da zaman lafiya. Misali a Jihar Kwara, Bukola Saraki ya tsayar da Gwaman Jihar, kuma har yanzu suna tare. Za a iya ci gaba da zaman lafiya da girmama juna, kuma ya danganci yanayin tsarin da ake ciki. Misali kuma ka dubi yadda Yari da Yarima suke mana, har yanzu suna zaman lafiya duk da cewa Yarima ne ya tsayar da Yari.

Amma akwai rade-radin cewa Yari ya yi wa Yarima ritaya a siyasa. Ba zai dawo Majalisar Dattawa ba, sannan dan takararsa na Gwamna Ibrahim Wakkala bai samu ba?

Yarima da kansa ya ba Yari takarar Sanata, ya sha fadar haka da kansa cewa yana so ne ya ba Yari dama ya tafi Majalisar Dattawa.

Ya yi Sanata na tsawon shekara 12, kuma ya yi Gwamna na shekara 8. Sannan ya rike mukaman siyasa na kusan shekara 20, wanda hakan ya sa ya ce yana so ya ba jikokinsa waje. Mu jikokinsa ne, su Yari kuma ’ya’yansa ne. Akwai kyakkyawar dangantaka a tsakanin Yarima da Yari. Wannan misali ne mai kyau.

Amma ana cewa Yarima da Yari sun yi yarjejeniyar cewa Yarima zai bar wa Yari kujerar Sanata, shi kuma Yarima sai ya tsayar da Gwamna. Me ya sa Yari ya yi watsi da yarjejeniyar?

Labarin Wakkala ke nan, babu wata yarjejeniya kamar haka. Matsayar a lokacin ita ce idan lokacin ya zo, Yarima da Yari za su zauna tare da sauran masu ruwa-da-tsaki domin su fitar da dan takarar Gwamna. Kuma hakan aka yi. Kuma har yanzu Yarima bai taba fitowa ya ce bai aminta da takarata ba.