✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda Zanga-zangar #EndSARS ta zama abun tsoro

Zanga-zangar #EndSARS ta fara daukar wani yanayi na daban a Jihar Legas, bayan kulle wasu manyan titunan jihar da wasu bata-gari suka yi da sunan…

Zanga-zangar #EndSARS ta fara daukar wani yanayi na daban a Jihar Legas, bayan kulle wasu manyan titunan jihar da wasu bata-gari suka yi da sunan zanga-zanga.

Bata garin suna amfani da zanga-zangar ne wajen kai hare-hare kan wuraren sana’ar mutane da ke kan hanyar Herbert Macaulay da ke unguwar Yaba a jihar ta Legas.

Zuwa lokacin hada wannan rahoto babu wani jami’in dan sanda ko daya a kan titin saboda gudun kai musu farmaki.

Duk da haka an shawarci mutane da su zama masu kallon da abubuwan da ke faruwa daga nesa saboda guje wa tsautsayi, kamar yadda hakan ta faru da wasu wadanda ba su ji, ba su gani ba tun farko-farkon fara zanga-zangar.

Ratonni sun bayyana cewa akwai wasu ‘yan kungiyar asiri da suke amfani da zanga-zangar wajen afka wa junansu da muggan makamai.

A yanzu haka dai an shawarci makarantun kudi da ke yankin na Yaba da su kulle rufe, saboda gudun abin da ka iya zuwa ya dawo.