Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

Yadda ziyarar Yariman Saudiyya Tunisiya ta tayar da kura

Daruruwan mutanen Tunusiya ne suka fito suka yi zanga-zangar adawa da ziyarar da Yarima mai jiran gado na Saudiyya Mohammed bin Salman ke yi a kasar, a yayin da ake ci gaba da cece-ku-ce kan kisan dan jaridar kasarsa Jamal Kashoggi.

Masu fafutika sun yi cirko-cirko a tsakiyar birnin kasar wato Tunis, suna cewa Yarima mai kisan kai ne kuma ba a maraba da shi a Tunisiya.

ADVERTISEMENT

Wata majiya daga Tunisiya ta ce an kafa wani babban hoton Yariman a ofishin Kungiyar ’Yan jaridar kasar da ke nuna shi dauke da zarto, wanda ke nufin da shi aka sassara Kashoggi.

Yarima Muhammad bin Salman dai ya kai ziyara kwana daya ce a kasar, inda ya gana da Shugaban kasar Tunusiya Kaid Essebsi a birnin Tunis.

ADVERTISEMENT

Muhammad bin Salman da Beji Kaid Essebsi sun tattauna kan dangantakar da ke tsakanin kasashensu kamar yadda rahoto ya nuna game da ziyarar.

A sahun abubuwan da suka tattauna, akwai tattalin arziki da tsaro da kuma bunkasa dabarun soja, kamar yadda wata sanarwar da fito daga fadar gwamnatin Tunisiya ta fitar.

Haka zalika, a wannan ganawar an waiwaiyi ayyukan  hadin gwiwa da kasashen biyu suka gudanar a baya, musammam a fannin fasaha da kimiyya da raya al’adu da kuma wasu muhimman lamuran da suka danganci ciki da wajen Saudiyya da Tunisiya.

A karshe, sun tattauna a kan shirye-shiryen da yanzu haka Tunisiya ke ci gaba da yi don karbar bakuncin babban taron kasashen Labarawa karo na 30 a watan Maris na badi.

Bin Salman ya fara kai ziyara Hadaddiyar Daular Larabawa a ranar Alhamis din makon jiya, inda daga bisani ya yada zango a kasashen Bahrain da Masar kafin ya isa Tunisiya.

Wannan shi ne karo na farko da Yariman na Saudiyya ya kai ziyara kasashen ketare bayan mutuwar dan jarida Jamal Kashoggi a ofishin jakadancin Saudiyya da ke birnin Istanbul na Turkiyya.

Babban abin da ya dauki hankali a ziyarar, shi ne yadda mutanen Tunisiya, wadanda suka hada da kungiyoyi da dalibai da ’yan siyasa suka fito fili suka nuna adawarsu da ziyarar, ta hanyar gudanar da zanga-zanga a babban birnin kasar.