✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yajin Aiki: Ministan Kwadago ya shawarci mambobin ASUU

Ministan Kwadagon Najeriya, Chris Ngige, ya shawarci Kungiyar Malaman Jami’a (ASUU) da su karbi tayin da Gwamnatin Tarayya ta yi musu su janye yajin aikinsu…

Ministan Kwadagon Najeriya, Chris Ngige, ya shawarci Kungiyar Malaman Jami’a (ASUU) da su karbi tayin da Gwamnatin Tarayya ta yi musu su janye yajin aikinsu na wata takwas.

Ngige wanda a ranar Litinin ya bayyana a shirin gidan talabijin na Arise, ya nemi mambobin kungiyar ASUU su gaggauta tuntubar junansu su cimma matsaya kafin dawowa teburin sulhu da Gwamnatin Tarayya a ranar Juma’a mai zuwa.

Ministan ya ce, al’ummar Najeriya za su yaba musu matukar suka amince da tayin suka janye yajin aikin domin bai wa dalibai damar koma wa ajujuwa wajen ci gaba da karatu.

“Ina jin wannan shi ne mafi kyawun tayi da na gabatar musu tun daga lokacin da na fara jagorantar zaman sulhu da su.”

“Ba na jin akwai dalilin da zai hana su karbar tayin domin an biya duk bukatun da suka nema saboda haka ba na jin za su yi watsi da wannan tayi”, inji Ministan.

“Sai dai na fada musu cewa neman al’ummar kasar da dalibai su jira daga Juma’a zuwa wata Juma’a ba daidai ba ne, ya kamata su waiwaye mu zuwa ranar Talata.

“Sun yi irin haka ne a baya bayan zaman sansanci da Shugaban Majalisar Dattawa, an yi musu tayi a ranar Alhamis, kuma suka dawo mana a ranar Talata.

“Saboda haka wannan shi ne abin da nake sa ran zai sake kasancewa a wannan karo, kuma idan suka cika muradinmu, al’ummar kasar nan za su yaba musu kuma za a dauke su a matsayin ’yan kasa na gari kuma masu kishi.”

“Ina tsammanin za su tuntube a lokaci mafi kusa gabanin ranar Juma’a.”

Aminiya ta ruwaito cewa Gwamnatin Tarayya ta mika wuya inda ta amince da tsame malaman jami’a daga cikin ma’aikatan da za ta rika biya a karkashin sabon tsarin albashin bai-daya na IPPIS.

A zaman sulhun da ta yi da kungiyar malaman jami’o’in a ranar Juma’ar makon da ya gabata, gwamnati ta amince za ta sauke nauyin bashin da ke kanta na biyansu albashin watan Fabrairu zuwa Yuni a bisa tsohon tsarin biyan albashin ma’aikatan gwamnati na GIFMIS.

Sai dai gwamnatin ta ce tsame mambobin ASUU daga tsarin biyan albashin na IPPIS na wucin gadi, inda a halin yanzu ake ci gaba da kirdadon tantace nagartar sabon tsarin biyan albashin na UTAS da kungiyar malaman ta gabatar.