Da Dumi Dumi

Yaki da Cin Hanci da Rashawa a Najeriya: Nazari a mahangar Musulunci (4)

Wannan lacca ce da aka gabatar a ranar 26-9-2016, don kara wa juna sani da Babban Lauya Ustaz Yusuf Alaoye Ali (SAN) ya gabatar a wani taro da ake shiryawa duk shekara mai taken ‘Muslim Legal Year Serbice’ a Babban Masallacin Egba, Kobiti, Abeokuta, Jihar Ogun. Barista M.B. Mahmoud Gama (08130969818) ne ya fassara.

 

Yawaitar talauci

A duk lokacin da jami’an hukumomin gwamnati da na masu zaman kansu suka mayar da hankali wajen daka wasoso ga dukiyar jama’a, to babu abin da yin haka zai haifar sai durkushewar wadannan hukumomi, inda daga karshe zai jawo wa talakawa rashin aikin yi daga bisani talauci ya shige su, in ma ba a yi hankali ba, ya shige su irin shigar nan ta Sojan Badakkare.

Rashin ci gaban kasa

ADVERTISEMENT

Duk kasar da karanta ya kai tsaiko cikin cin hanci da rashawa kamar Najeriya, to babu shakka akwai yiwuwar za ta fuskanci mummunar koma-baya dangane da ci gabanta. Duk lokacin da aka ce manyan jami’an gwamnati da na masana’antu masu zaman kansu ba abin da suka sani sai azurta kansu ta hanyar handame dukiyar jama’a zuwa kasashen waje, to babu shakka tattalin arzikin wannan kasa zai shiga kwaramniyar da ba a san lokacin fita daga cikinsa ba.

Rikice-rikice a cikin kasa

Shin ko kun san cewa duk tashe-tashen hankalin da ke aukuwa nan da can a cikin Najeriya kama daga rikicin ’yan Boko Haram da masu garkuwa da mutane da na ’yan Neja-Delta da na makiyaya da manoma zuwa ta ’yan Biyafara, duk sun wanzu ne saboda cin hanci da rashawa. Wato rashin gaskiya da kin yin abu bisa ka’ida. Duk wadannan rikice-rikice sun haifar da mummunan tasiri da dakile ci gaban tattalin arzikin kasar nan ta hanyar korar mutanen kasashen waje masu niyyar zuba jarinsu don ci gaban tattalin arzikin kasar nan.

Musulunci shi ne addini daya tilo da yake da ruwa-da-tsaki cikin gudanar da kacokan din rayuwar mabiyansa.  Don haka ne Musulunci ya yi umarni ga kowane Musulmi ya zama mutumin kirki, mai tsoron Allah wanda ya wofinta daga aikata munanan ayyuka, ya kuma danfaru da aikata kyawawa cikin al’amuransa dukkansu.

Kasancewarsu masu tsoron Allah, shi ne mataki na farko kuma cikamakin matakan maganin matsalolin da cin hanci da dan Adam zai tsinci kansa a yanzu da kuma nan gaba, a cikin rayuwarsa. Mafi girman daraja ga mutum Musulmi a cikin mu’amalarsa, shi ne ya zamo mai gaskiya da adalci da taimakon gajiyayyu da mabukata da girmama iyaye da na-gaba da malamai da kuma nuna jinkai ga mata da kananan yara da sauransu.

Musulunci bai tsaya nan ba, sai da ya haramta wa Musulmi yin yasasshiyar magana da kisan ran da bai ji ba, bai gani ba da yin ta’addanci da cin zali da rashin adalci da bakar gaba da zinace-zinace da shaye-shaye, da sauransu.

Wannan umarni da hani suna tabbatar da Musulunci shi ke rike da ragamar gudanar da rayuwar Musulmi kacokan dinta. Don haka ne Allah Mai girma da Daukaka Yake fada a cikin Alkur’ani cewa: “Ka ce (Ya Annabi Muhammadu), lallai Sallata da yankana da rayuwata da mutuwata, (duk ina yin su ne) ga Allah Ubangijin talikai.”

Wannan aya tana nuna cewa duk abin da Musulmi zai yi, to yana yinsa ne gwargwadon tanade-tanaden da Musulunci ya yi. In kuwa haka ne, to ba wani abu a cikin Musulunci illa na umarni da kyakkyawa da kuma hani daga mummuna.

Nan baya kadan, mun ambaci dalilan da suke haddasa cin hanci da rashawa a cikin al’umma. To yanzu bari mu kutsa don gano yadda za a magance wannan annoba ta cin hanci da rashawa, ta yin la’akari da hanyoyin da Musulunci ya shimfida don samun gwamnati da al’umma irin wadda Allah da kanSa Ya yaba saboda umarni da kyakkyawa da kuma hani da mummuna, in an bi su.

Allah Yana cewa: “Ku (al’ummar Annabi Muhammadu) kun kasance mafi alherin al’ummai da Allah Ya taba halitta, (saboda) kuna umarni da kyakkyawa kuma kuna hani da mummuna; sannan kuna imani da Allah…” (Alkur’ani: 3:110).

Daga wannan aya ta sama, ya bayyana karara cewa shika-shikan kafuwar gwamnati ko al’umma tagari su ne umarni da kyawawan ayyuka don dabbaka su da kuma hani daga munana don nesa da su, duk cikin yin imani da Allah Madaukaki. Wadannan ginshikai guda uku na samun al’umma tagari idan aka dasa su kuma aka bi su sau-da-kafa, to babu shakka za su taimaka wajen yaki da kakkabe cin hanci da rashawa a cikin al’ummarmu.

Umarni da kyakkyawan aiki

Duk al’ummar da ko mafi yawanta ke umarni da aikata kyawawan ayyuka, to babu shakka za ta zama mai cike da salama da natsuwa a bayan kasa, tunda sakamakon mai aikata alheri shi ne samun alherin don aikata ayyuka na alherin. Kamar yadda Allah Mabuwayi Ya fada a cikin Alkur’ani (55:50), inda Yake cewa: “Mene ne sakamakon alheri in ban da (samun) alheri kwatankwacinsa?” Amma abin bakin ciki, mafi yawan ’yan Najeriya, aikata alheri ya yi gabas su kuma sun danna yamma a guje! Wannan ya sa muka tsinci kanmu a irin wannnan mummunan hali da muke ciki a yanzu. Ko shakka babu, cin hanci da rashawa da muke ta tafkawa ta fuskoki daban-daban a kasar nan, ba komai ne ya haddasa su ba illa rashin tarbiyyar umarni da dabbaka kyawawan ayyuka.

Musulunci yana kallon dabi’ar cin hanci da rashawa da ta yi katutu a tsakanin al’umma, a matsayin son kai da son tara abin duniya cikin dare daya, don haka ne Musulunci ya yi umarni da tsantseni da kamewa ta hanyar yin adalci da daidaita al’amura da yin gaskiya da jin tsoron Allah da nuna duk wani halin kirki. Allah Madaukakin Sarki Ya fada a cikin Alkur’ani (11:25) cewa: “Ya ku mutane, ku cika awo da mizani cikin adalci, sannan kada ku cuci mutane cikin kayansu, sannan kada ku aikata rashin adalci a bayan kasa kuna masu (haddasa) fasadi.”

Wannan aya tana nuna yadda Musulunci balo-balo ya nuna kin duk wani nau’in abin ki da ya hada da cin hanci da rashawa. Sannan ayar, ta yi kira da aikata duk wani halin kirki da suka hada da adalci a tsakanin mutane, saboda a samu  daidaito da girmama doka da zaman lafiya da karuwar arziki a tsakanin mutane. Da wannan ne za a iya fahimtar cewa, Musulunci kullum yana kira ne da kuma tabbatar da wani tsari ga duniya baki daya da zai inganta tsakanin mutane da Mahaliccinsu da a tsakaninsu a karan kansu, kai har da tsakaninsu da sauran halittu (dabbobi da sauransu), ta hanyar yin adalci da daidaito a tsakanin su mutane, wanda yin hakan ba kawai zai tabbatar da walwala a tsakanin mutane ba ne, a’a, har da samar da al’umma nagartacciya mai kuma gaskiya.

Za mu ci gaba

 

Tura
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya