Da Dumi Dumi

Yaki da Coronavirus: China za ta ba da dala biliyan biyu

Shugaba Xi Jinping na China (Hoto: Quartz)

Kasar China ta yi alkwarin ba da dala biliyan biyu a cikin shekaru biyu saboda dakile cutar coronavirus a fadin duniya.

Shugaban kasar ta China Xi Jinping ne ya sanar da haka ranar Litinin a wani sako da ya aike wa Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) a yayin wani taron bita na shekara-shekara inda ya yi nuni da cewa kudaden ba za su takaita ga harkar kiwon lafiya kawai ba har ma da ayyukan ci gaba a yankunan da abin ya shafa.

Ya bukaci kasashe da su kara kudaden da suke bayarwa saboda daukar nauyin hukumar.

Sakon ya kara da cewa a halin da duniya ta shiga na yaki da cutar da kuma janye hannu da Amurka ta yi daga al’amuran hukumar akwai bukatar “Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta kasance kan gaba wurin yaki da cutar”.

Amurka dai na zargin kasar ta China da rufa-rufa game da cutar ta coronvirus wadda ta yadu a fadin duniya.

ADVERTISEMENT

Zarge-zargen dai sun hada da sakaci tun a karon farko na sanar da duniya gaskiya game da cutar.

Tuni dai gwamnatin kasar ta China ta yi watsi da zarge-zargen inda ta bayyana cewa bata aikata lafin komai ba.

Tura
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya