✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Yan banga sun ceto mutum 5 da aka yi garkuwa da su a jihar Edo

Wasu ‘yan banga sun kubutar da wasu mutum biyar da aka yi garkuwa da su a Karamar Hukumar Esan ta Yamma, a jihar Edo. Rahotanni…

Wasu ‘yan banga sun kubutar da wasu mutum biyar da aka yi garkuwa da su a Karamar Hukumar Esan ta Yamma, a jihar Edo.

Rahotanni na cewa, ‘yan bangar sun ceto mutanen ne a jiya Lahadi, a wani kauye mai suna Egoro na Oka, cikin Jihar ta Edo.

Su dai wadanda aka sace kana aka yi garkuwar da su, an sace su ne yayin da suke kan hanyar dawo wa daga bukin rufe wata gawa a wannan yankin.

Rahotanni sun ce an shafe dare guda ana ta neman yadda za a kubutar da wadanda aka yi garkuwan da su.

Sai dai ko da Wakilin Aminiya, ya tuntubi kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Chidi Nwanbuzor, ya ce bai da ta cewa game da al’amarin, sakamakon yadda al’amuran daukar sabbin ‘yan sanda ya sha masa kai, amma ya ce daga baya zai kira Wakilin Aminiyan.