✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yan banga sun kai wa ofishin ‘yan sanda hari

’Yan banga sun kai wa Babban Ofishin ’Yan Sanda na garin Kagara hari kan gazawarsu wurin magance ayyukan ’yan bindiga a yankin. Fusatattun ’yan bangar…

’Yan banga sun kai wa Babban Ofishin ’Yan Sanda na garin Kagara hari kan gazawarsu wurin magance ayyukan ’yan bindiga a yankin.

Fusatattun ’yan bangar sun kai wa ofishin farmaki ne bisa zargin kin kai musu dauki da wuri a lokacin da ’yan bindiga suka kai musu hari a kauyen Tashar Kare, har aka kashe takwarorinsu guda hudu.

Kakakin ’Yan Sandan Jihar Neja, ASP Wasiu Abiodun ya ce ’yan banga sama da 50 ne suka dirar wa ofishin a lokacin da Babban Baturen ’Yan Sanda Mai Kula da Yankin ke kokarin lallashin su.

Ya ce daga baya al’amura sun daidaita baya Mataimakin Kwamishinan ‘Yan Sanda Mai Kula da Ayyuka da Kwamandan yankin Kontagora da jami’an rundunar tsaro ta Operation Puff Adder sun shiga tsakani.

Rahotanni sun ce wani dan banga ya samu raunin harsashi bayan da ya yi kokarin kwace bindigar wani dan sanda mai gadi a ofishin.

ASP Abiodun ya ce Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Neja, Adamu Usman, ya umarci Mataimakinsa Mai Kula da Bincike ya gudanar da cikakken bincike ka abin da ya faru tun daga tushe.

Kwamishinan ya kuma bukaci jama’ar jihar su kwantar da hankulansu domin an riga an dauki matakan da suka dace na tabbatar da tsaro a garin.