Da Dumi Dumi

’Yan bangar siyasa sun kusa hana da dan takarar Gwamnan PDP shiga dakin taro

’Yan bangar siyasa sun kusa hana dan takarar Gwamnan Jihar Jigawa  a Jam’iyyar PDP Malam Aminu Ringim shiga dakin taro a hedikwatar jam’iyyar a ranar Litinin da ta gabata da aka gudanar da taron masu ruwa-da-tsaki na jam’iyyar don cike gurabun masu rike da mukamai a jam’iyyar da suka fice daga cikinta.

Malam Aminu Ringim bai samu damar shiga wajen taron ba, sai da kokawa, sannan da ya shiga dakin taron matasa suka rika yi masa ihu lamarin da ya sa ba a tashi daga taron ba ya fice.

Wani jigo a jam’iyyar da ya nemi a sakaya sunansa ya bayyana wa Aminiya cewa akwai jita-jitar da ke yawo cewa Aminu Ringim zai fice daga jam’iyyar zuwa APC ko PRP lamarin da ya sa ’ya’yan jam’iyyar suke kallon haka a matsayin cin amana ga jam’iyyar.

Bayan tsohon Gwamnan Jihar Alhaji Sule Lamido ya fito daga dakin taron, wadansu da ake zargin magoya bayan Malam Aminu Ringim ne sun tsaya a kan titi suna cewa “Sai Malam! Sai Atiku.”

Kokarin da wakilinmu ya yi don jin ta bakin Malam Aminu Ringim kan zargin da ake yi masa na shirin sauya sheka ya ci tura.

ADVERTISEMENT

Aminiya ta gano tunda jam’iyyar ta fadi zabe a jihar babu wani taro da ta yi a jam’iyyance har abubuwa suka yi kamari aka rasa mukamai ganin yadda jiga-jigan jam’iyyar suka rika ficewa daga cikinta.

Share