✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yan bindiga: Muna mamaki kan mamakin da Buhari ya yi

A ranar Talata ce Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya fada wa ayarin manyan mutanen Jihar Neja da suka ziyarce shi a fadarsa da ke Abuja…

A ranar Talata ce Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya fada wa ayarin manyan mutanen Jihar Neja da suka ziyarce shi a fadarsa da ke Abuja cewa yana mamakin jin cewa har yanzu akwai ’yan bindigar da suke addabar wasu yankuna a Najeria. Ya ci gaba da cewa can baya lokacin da yake kamfe matsalar Boko Haram ce babban kalubale, amma ga shi yanzu kuma ’yan bindiga suna mayar masa da hannu agogo baya ganin cewa an ci lagon ’yan Bok Haram.

Ya yi alkawarin cewa “Tsanani na tafe ga ’yan bindigar” wadanda a halin yanzu suka jefa jama’a da dama a cikin kuncin rayuwa. “An mayar mini da hannun agogo baya, domin lokacin da muke kamfe Boko Haram ce muka sani. Abin da muke gani yanzu yana ba ni mamaki. Shi ba kabilanci ba kuma ba rikicin addini ba, amma dai wani sabon shiri ne aka kirkira na ruguza kasar nan. Don haka dole mu tsananta musu, domin hakki ne da ya rataya a wuyan gwamnati ta kawo tsaro a kasa. In har kuwa ba mu iya kawo tsaro a kasa ba to babu yadda za a yi mu iya bunkasa tattalin arzikin kasar,” inji shi.

Shugaba Buhari ya ci gaba da cewa; wadannan hare-hare da ’yan bindiga suke kaiwa ya kuma maida hannun agogo baya ta fannin noma, inda ya ce manoma da dama ba sa iya zuwa gonakinsu saboda gudun abin da ka je ya komo. Wannan kuwa ya sanya da yawa sun kaurace wa gonakin wanda hakan na nufin ci baya.

Washegarin wannan taro Kakakin Shugaban Kasa, Mista Femi Adesina, ya zargi ’yan jarida da “kirkirar wani zance don dadada wa wadansu” a kan jawabin da Shugaban Kasar ya gabatar, inda Femi ya ce “Ai Shugaban Kasa yana magana ne a kan matsalar tsaro ta Arewa maso Yamma inda yake mamakin cewa duk da yake mafi yawan mazaunan wannan yanki Hausawa da Fulani ne kuma Musulmi amma ga shi sun kasa zama lafiya. Don haka wannan shi ne abin da yake ba Shugaba Buhari mamaki.”

Adesina  ya ci gaba da cewa “Wannan ba adalci ba ne, domin an debo farko da kuma karshen jawabinsa ne aka harde, sannan aka kamo tsakiyar zancen aka yi masa mummunar fassara cewa wai Shugaban Kasa Buhari bai da masaniya game da abubuwan da suke faruwa ta fuskar tsaro a kasar nan.”

Duk da yake babu wani shakku a cikin abin da Shugaban Kasa ya fada, amma a gaskiya akwai abin takaici game da jawabin nasa. Domin kuwa a matsayinsa na Babban Kwamandan Askarawan Najeriya kuma Shugaban Tsaro na Kasa a kullum yana samun bayanai game da duk wani abu da ya shafi tsaron kasa.

Duk da yake a kowace rana aikata laifi yana sake sabon salo ne, ya kamata Shugaban Kasa ya zage damtse ta hanayar tuntubar masu ba shi shawara ta fuskar tsaro don babu wani abu yanzu da zai bada mamaki game da tabarbarewar tsaro a kasar nan.

Sannan idan Shugaban Kasa ya ce yana mamaki, to wannan ma ai abin mamaki ne domin kuwa ko a Jihar Katsina mahaifarsa tana fuskantar matsalar tsaro kuma ko Sarkin Daura da kuma matar Shugaban Kasar Hajiya A’isha Buhari sun ce ’yan bindigar sun yi sanadiyyar lalata amfanin gona mai yawa. Abin tambaya a nan shi ne, shin da gaske ne Shugana Kasa Buhari bai da masaniya ko kuwa ba ya jin labarin cewa matsalar ’yan bindiga ta addabi jama’a?

Mu ba mu yarda da maganar cewa wai wannan matsala ta tsaro wani kulli ne da aka yi don ruguza kasar nan ba, domin iya saninmu ba mu taba jin masu garkuwa da mutane da ’yan bindiga sun yi wani zama sun kulla yadda za su ruguza kasar nan ba.