✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga: Noma ya ragu da kashi 30 a Katsina

Akalla gonaki 500 ne a jihar manoma suka yi watsi da su domin tsira da rayukansu

Ayyukan ’yan bindiga sun kawo nakasu ga ayyukan noma da kashi 30 cikin 100 tare da tilasata wa manoma tserewa daga gonakinsu a Jihar Katsina.

Kwamishin Noma kuma Mataimakin Gwamnan Jihar, Mannir Yakubu, ya ce akalla gonaki 500 ne a fadin jihar manoma suka yi watsi da su domin tsira da rayukansu daga ‘yan bindiga.

“Gonakin guda 500 sun kai girman hekta 58,000 kuma hakan ya yi mummunan tasiri wajen rage yawan hatsin da ake nomawa da kashi 30 cikin 100 a Jihar Katsina”, inji shi.

Da yake jawabi a ranar Juma’a, Mataimakin Gwamnan ya ce duk da cewa annobar COVID-19 ba ta kawo cikas ga noma ba, ta kawo nakasu ga samuwar takin zamani da kuma rabonsa a jihar da wasu sassan Najeriya.

“Mun saba samun metric ton 30,000 na takin zama a duk shekara amma bana metric ton 10,000 aka yi mana alkawari, wanda daga ciki metric ton 3,000 kawai muka samu.

“Mun kokarin karawa da ragowar metric ton 1,000 da muke da shi na bara domin rabawa ga manoman rani”, inji shi.

Ya ce a karon farko jihar za ta fara noman auduga da rani a bana baya ga masara da alkama da ta saba nomawa da rani.