✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun kashe jama’a a kauyukan Katsina

Wasu ’yan bindiga sun kai wani mummunan hari a kananan hukumomi uku na jihar Katsina da suka hada da: Safana da Danmusa da Dutsinma. Rahotan…

Wasu ’yan bindiga sun kai wani mummunan hari a kananan hukumomi uku na jihar Katsina da suka hada da: Safana da Danmusa da Dutsinma.

Rahotan ya bayyana cewa kwanaki kadan ne aka tallafawa wasu ’yan gudun hijira da ke yankin.

Wasu da suka samu tallafin sun ce gwamnati ta tallafa masu da kayan abincin, amma lokacin harin ’yan bindigar sun kwace sun yi gaba da kayan tallafin da safiyar ranar Asabar.

Majiyarmu ta samu rahoton samun gawarwakin jama’a da ’yan bindigar suka kashe a kauyukan kananan hukumomin.