✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Yan bindiga sun mamaye wasu yankunan Katsina – Masari

Gwamnan jihar Katsina Aminu Masari ya bayyanawa Mukaddashin Sufeta Janar na `yan sandan Najeriya Muhammed Adamu, cewa ‘yan bindiga da masu garkuwa da mutane sun…

Gwamnan jihar Katsina Aminu Masari ya bayyanawa Mukaddashin Sufeta Janar na `yan sandan Najeriya Muhammed Adamu, cewa ‘yan bindiga da masu garkuwa da mutane sun mamaye wasu yankunan jihar Katsina.

“Yan bindiga da masu garkuwa suna kai hare-hare a duk lokacin da suka dama tare da raunata jama’a da kone dukiyoyin su”. Kamar yadda Mataimakin Gwamnan jihar Mannir Yakubu ya sanarwa shugaban ‘yan sandan a madadin Gwamna Masari.

Mannir, ya kara da cewa, masu garkuwa ba wai kawai a hanya suke yin garkuwa da mutane ba, wasu har gidajen jama’a suke shiga su tafi da su, kamar yadda aka yi garkuwa da surikar Gwamnan jihar.